SAU da dama idan ‘yan fim mata sun yi aure, to sun yi sallama da harkar fim kenan. To sai dai an fi samun hakan ga jarumai mata, amma abin da ya shafi shirya fim ko waƙa, yawancin matan su na ci gaba da sana’ar su.
Fa’iza Badawa ta na ɗaya daga cikin manyan mawaƙa mata da su ka daɗe ana damawa da su, domin kuwa ta shafe kusan shekara 20 ta na waƙa, kuma ta yi aure shekara biyar da ta gabata amma auren da ta yi bai hana ta ci gaba da waƙa ba, saboda ta riƙe ta a matsayin sana’a.
A tattaunawar da mujallar Fim ta yi da ita kwanan nan, Hajiya Fa’iza ta bayyana mana yadda ta ke gudanar da harkar ta ta waƙa duk da matsayin ta na matar aure.
Amma da farko ta fara da ba mu tarihin rayuwar ta da yadda ta fara waƙa. Ta ce: “Assalamu alaikum. Da farko dai suna na Fa’iza Muhammad, wadda aka fi sani da Fa’iza Badawa.
“Ni haifaffiyar garin Kano ce. An haife ni a unguwar Badawa kamar shekara talatin da uku da su ka wuce. Na yi karatu na a Kano.
“Na fara waƙa shekara goma sha takwas da su ka wuce.”
Da mu ka tambaye ta yawan waƙoƙin da ta yi kuwa, cewa ta yi, “A gaskiya, waƙoƙin da na yi ba zan iya lissafa su ba saboda yawan su. Amma dai waƙar da ta sa aka fara sani na ita ce waƙar ‘Oga Abuja Ɗan Lukuti Ɗan Siriri Dazi Guda Ɗaya Mamawo’ wadda aka saka a cikin fim ɗin ‘Oga Abuja’.
Dangane da auren da ta yi, Fa’iza ta ce: “Na yi aure a ranar 8 ga Afirilu, 2017. Zuwa yanzu mu na tare da maigida na. Mun haifi yaro ɗaya.”
Fa’iza ta yi tsokaci kan kallon da ake yi wa mata kamar ko
Shin tun da ta yi auren ne ta daina waƙa? Amsa: “Gaskiya ban daina waƙa ba. Kuma ban ɓoye kai na ba. Don yawancin manya-manyan mawaƙa maza -Sadiq Zazzaɓi, Nazifi Asnanic, Dauda Rarara, Kamilu Koko, Jaddah Garko, da Tijjani Gandu – sun san ina waƙa har yanzu tunda ina aiki tare da su har gobe.
“Akwai wanda in ya kira waya ta ma bai same ni ba ya na kiran miji na, sai miji na ya kira ni da wata lambar ya faɗa mini in je mu yi aikin. Amma dai na san akwai kuma wasu mawaƙa mata da in aka ce musu Fa’iza Badawa ta na waƙa kuwa sai su ce ‘a’a tun da ta yi aure’. Sai mun haɗu da wasu a cikin su na je ɗora wa wani babban mawaƙi aiki sai su ce mini ai an ce na daina waƙa, shi ya sa ba sa kira na, ko don wannan babban mawaƙi ne?’ Sai na ce musu da ma can ban daina ba. To da haka wasu su ke fara dawowa su na aiki da ni. Don a cikin shekarar da ta wuce na buɗe ƙungiyar mawaƙa mata; ka ga ko ai ban daina waƙa ba.
“Kuma duk biki ko suna na mawaƙa mata babu wanda ba na zuwa. Don akwai abubuwan da sai an shawarce ni ma ake yi.”

To ko yaya Fa’iza ta ke gudanar da waƙar ta bayan ta yi aure? Amsar ta ita ce: “Duk mawaƙin da zai kira ni ina tambayar sa: ka gama waƙar? In ya ce ya gama zan je in ɗora masa.
“Kuma akwai wani abu da masu situdiyo su ke yi. In dai matar aure ce ta zo za ta yi aiki, to ko waye ya ke yin aiki sai ya tsaya ta ɗora nata ta tafi sai ka zo ka ci gaba da waƙar ka, saboda a yanzu zan iya cewa mawaƙa matan aure mun fi ‘yan mata yawa a cikin masana’antar Kannywood, don babu matar da ta yi aure ta daina waƙa a cikin mu, daga lokacin da na fara waƙa zuwa yanzu, kamar ni Fa’iza Badawa, Zuwaira Isma’il, Murja Baba, Naja’atu Ta’Annabi, Maryam A. Baba, Jamila Sadi, Zainab Diamond, Sa’a Vocal, da Sa’a Nazifi Asnanic.”
Da mujallar Fim ta tambaye ta idan akwai wata matsala da ta ke samu a matsayin ta na matar aure da ta ke waƙa, sai ta ce: “A’a, babu wata matsala da na ke fuskanta a matsayi na na mawawaƙiya kuma matar aure saboda mu na fuskantar junan mu ni da miji na.
“Ina son miji na so na har abada. Ina so Allah ya bar ni da miji na har ƙarshen rayuwar mu mu na tare, domin shi abokin rayuwa ta ne kuma ya na ba ni ƙwarin gwiwa a game da sana’ar da na ke yi ta waƙa. Ina yi masa fatan alheri tare da dukkan masoya na da su ke sauraron waƙoƙin da na ke yi kuma su ke jin daɗin su.”


Aslm inayi muku fatan alkairi da fatan allah ya kara basira kuma dan Allah innada tambaya idan mace A masana,antar kannywood tayi aure tana cigaba da shirin fimne kokuwa?Dan Allah inna jiran amsa.