MAWAƘI a Kannywood, Abdullahi Abubakar, wanda aka fi sani da Auta Waziri, ya yi kira ga abokan sana’ar sa da kada su dogara kacokam da harkar waƙa, amma su riƙa haɗawa da ‘yan sana’o’i.
Auta ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ke bayyana wa mujallar Fim dalilin sa na buɗe gidan ɗaukar hoton kati da kuma wurin shaƙatawa.
A tattaunawar sa da wakilin mu, fitaccen mawaƙin wanda ke zama a Kaduna ya ce: “Gaskiya, alal haƙiƙa duk wanda ya san ni, ya san ina da sha’awar kasuwanci, saboda mahaifi na ɗan kasuwa ne. Ya yi karatu duk irin karatun da ake so, digiri da sauran su, amma kuma ɗan kasuwa ne. To kuma Allah ya yi masa rasuwa.
“Don haka kasuwanci ina jin sa a jiki na ne, shi ya sa ka ga ina yi. Wannan wurin shi ne na biyu, domin mu na da ‘Diamond Star Photos’, sannan sai kuma ‘Diamond Star Resort’. Ni haka na ke, ina da plan ɗin bizines gaskiya.

“Wannan wuri da mu ka buɗe, mun buɗe shi washegarin Babbar Sallah ne, inda aka yi kwanaki uku ana wasan Sallah a harabar wurin. Manya da ƙananan mawaƙa da ‘yan fim sun halarci wasan Sallar.”
Ya lissafa abubuwan da ake yi a ‘Diamond Star Resort’ kamar haka: sun haɗa da gidan abinci, wanda ana yin kifi, shayi, chifs da ƙwai, kaza, indomie, abubuwan sha dai duk wasu kayan maƙulashe.
“Sannan akwai ɓangaren da ake wankin mota, wurin wasanni irin sunuka, ana yin taron bikin aure, bikin suna, murnar zagayowar ranar haihuwa da sauran ‘shows’. Za kuma mu ƙara buɗe wasu wuraren a nan gaba da za mu kawo sababbin abubuwa.
“Zuwa yanzu akwai ma’aikata a ƙasa na daga ‘Diamond Star Photos’ zuwa ‘Diamond Star Resort’, sun kai mutum goma sha biyar.
“Wurin ɗaukar hoto na Ƙofar Gamji, wurin shaƙatawar kuma na nan a kan Titin Swimming Pool, kafin ka ƙarasa Ƙofar Gamji.”

A nan ne Auta Waziri ya yi kira ga abokan sana’ar sa da kada su mayar da hankali a kan harkar waƙa kawai.
“Mu yi ƙoƙari mu na haɗawa da kasuwanci, domin da harkar waƙar za ka taimaki kasuwancin ka,” inji shi.

![]()







