• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, July 5, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ƙungiyoyin ƙwadago sun fasa yajin aiki bayan yarjejeniya da gwamnati

by DAGA WAKILIN MU
October 3, 2023
in Nijeriya
0
Ministan Ƙwadago da Samar da Aiki, Simon Bako Lalong (a hagu) da Shugaban NLC, Comrade Joe Ajaero

Ministan Ƙwadago da Samar da Aiki, Simon Bako Lalong (a hagu) da Shugaban NLC, Comrade Joe Ajaero

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƘUNGIYOYIN ƙwadago na NLC da TUC sun janye shirin su na shiga yajin aikin da a da za su fara a yau Talata.

Hakan ya biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin su da Gwamnatin Tarayya a wani taro da su ka yi a jiya Litinin a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Wasu daga cikin muhimman abubuwan da aka cimma a yarjejeniyar sun haɗa da alƙawarin da gwamnati ta yi na ƙarin N35,000 ga duk ma’aikata har na tsawon watanni shida daga watan Satumba.

Haka kuma akwai “kafa wani kwamiti mai ƙarfi cikin wata ɗaya wanda zai duba batun ƙarin albashi ga ma’aikatan ƙasar nan.

“Janye harajin da aka sanya a harkar man gas (diesel) na tsawon watanni shida daga watan Oktobar 2023.

“Sanya naira biliyan 100 don sayo manyan motocin bas-bas masu amfani da man gas don sauƙaƙa wa jama’a hanyar zirga-zirga a duk faɗin ƙasar nan, wanda ake sa ran za a yi a watan Nuwamba mai zuwa.

Haka kuma an cimma yarjejeniyar cire haraji ga wasu kamfanoni da ɗaiɗaikun jama’a don sauƙaƙa masu wajen hada-hadar yau da kullum.

Haka kuma an cimma yarjejeniyar sasantawa a ƙungiyar direbobi ta ƙasa (NURTW) tare da sanya baki a batun soke ƙungiyar masu motocin N25,000 a duk wata daga Oktoba ɗin nan ga ‘yan Nijeriya mutum miliyan15, wanda ya haɗa da tsofaffin ma’aikata masu karɓar fansho.

Akwai kuma ƙara faɗaɗa shirin nan na rabon taki ga manoma a duk faɗin ƙasar.

An kumma amince da cewa su ma jihohi da ƙananan hukumomi za a ƙarfafa masu gwiwa domin aiwatar da wannan ƙarin albashi ga ma’aikatan su.

Za a samar da kuɗaɗe ga matsaƙaita da ƙananan masana’antu, sannan za a mayar da hankali wajen ƙirƙiro da ayyuka ga matasa.

Za kuma a fito da shirin zagaya matatun man fetur ɗin ƙasar nan don tantance irin gyaran da su ke buƙata.

Gwamnatin Tarayya za ta yi amfani da takardun da kotu ta sahale ne wajen saka hannu a kan wannan yarjejeniyar fahimtar juna cikin mako ɗaya.

Ita dai wannan yarjejeniya ta samu sanya hannun shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero, Sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja, shugaba da Sakatare na TUC, Festus Osifo da Nuhu A.

A ɓangaren gwamnati kuwa akwai Ministan Ƙwadago, Simon Baƙo Lalong, da Ƙaramin Ministan sa, Nkeiruka Onyejeocha, da kuma Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Mohammed Idris.

Loading

Previous Post

Marubuci Larabi ya zama jakaden asibitin Indiya

Next Post

Ranar ‘Yanci: ‘Yan Nijeriya mazauna London sun nemi a yi wa gwamnatin NNPP a Kano adalci

Related Posts

SHEKARA ƊAYA BAYAN KOMAWA KAN KARAGAR MULKI: Tasirin Yadda Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Dawo Da Martabar Masarautar Kano
Nijeriya

SHEKARA ƊAYA BAYAN KOMAWA KAN KARAGAR MULKI: Tasirin Yadda Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Dawo Da Martabar Masarautar Kano

July 5, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya

July 1, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina

June 30, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin akwai tsaro a Abuja duk da gargaɗin da Amurka ta ba matafiya

June 23, 2025
Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya
Nijeriya

Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya

June 21, 2025
Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu
Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu

June 20, 2025
Next Post
Ranar ‘Yanci: ‘Yan Nijeriya mazauna London sun nemi a yi wa gwamnatin NNPP a Kano adalci

Ranar 'Yanci: 'Yan Nijeriya mazauna London sun nemi a yi wa gwamnatin NNPP a Kano adalci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!