• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, May 15, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwarzon dimokiraɗiyya: Hukumar zaɓen Laberiya ta karrama shugaban INEC

by DAGA WAKILIN MU
January 2, 2024
in Nijeriya
0
Gwarzon dimokiraɗiyya: Hukumar zaɓen Laberiya ta karrama shugaban INEC

Farfesa Yakubu ya na karɓar hatimin karramawa daga hannun Madam Davidetta Browne Lansanah a birnin Monrovia

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
Farfesa Yakubu ya na karɓar hatimin karramawa daga hannun Madam Davidetta Browne Lansanah a birnin Monrovia

HUKUMAR Zaɓe ta Laberiya (NEC) ta yi jinjina da damƙa kambin yabo ga Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, bisa ƙoƙari da muhimmiyar rawar da ya taka wajen ƙara wa dimokiraɗiyya karsashi a ƙasar.

Wannan karramawa ta fito ne daga Shugabar Hukumar Zaɓen Laberiya ɗin, Madam Davidetta Browne Lansanah, a ranar Juma’a, a Monrovia, babban birnin ƙasar.

An damƙa masa kambin girmamawar ne a wurin taron sanin makamar aiki da aka shirya wa ma’aikatan hukumar zaɓen Laberiya, wanda Yakubu ne ya jagoranci horaswar.

A cikin jawabin ta, Lansanah ta nuna farin ciki da gamsuwa da irin basira da kyawawan tsare-tsaren da INEC da Yakubu su ka shimfiɗa wa Hukumar Zaɓen Laberiya, wanda ta ce ya ƙara wa matakan shirya zaɓuɓɓukan ƙasar inganci da nagarta.

Ta nuna godiya ga Farfesa Yakubu, a madadin Hukumar Zaɓen Laberiya, bisa ga gagarumar rawar da ya taka wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya da matakan kafa dimokuraɗiyyar a Laberiya.

Da ta ke tuna rawar da gudunmawar da ya bayar a matsayin sa na Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Hukumomin Zaɓe na Ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), Lansanah ta lissafo yadda ya tafiyar da ƙungiyar bisa nuna kishin aiki da bin ƙa’idoji. Ta kuma jinjina masa dangane da yadda ya riƙa ba ta goyon baya a matsayin ta na Shugabar Hukumar Zaɓe ta Laberiya.

Farfesa Yakubu da sauran mahalartan taron

Da ya ke nuna godiya bisa karamcin da aka yi masa, Farfesa Yakubu ya bayyana farin ciki dangane da karramawar da Hukumar Zaɓen Laberiya ɗin ta yi wa INEC.

Haka kuma ya nuna muhimmancin nagartattun ayyuka da tsare-tsaren da ma’aikatan INEC su ka bijiro wa ma’aikatan hukumar zaɓen Laberiya.

Ya tuno da irin rawar da INEC ta bayar lokacin tsare-tsaren shirya zaɓen shugaban ƙasa a Laberiya da aka yi cikin 2017, sai kuma gudunmawar da INEC ɗin ta bayar a zaɓen raba-gardama cikin 2020, wanda ECOWAS ta gudanar.

Yakubu ya nuna yadda INEC ta taimaka wa hukumar zaɓen Laberiya wajen gina wa ƙasar turbar rajistar masu zaɓe ta hanyar tsarin na’urar tantance masu katin rajista.

Loading

Tags: ECOWASFarfesa Mahmood YakubuHukumar Zabe ta Kasa (INEC)LaberiyaLiberiaMadam Davidetta Browne Lansanahzaɓe
Previous Post

Jarumin Kannywood, Abdullahi Amdaz ya zama angon Aisha

Next Post

Minista na so ‘yan kasuwa su zuba jari don haɓaka shirin iskar gas na CNG

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Minista na so ‘yan kasuwa su zuba jari don haɓaka shirin iskar gas na CNG

Minista na so 'yan kasuwa su zuba jari don haɓaka shirin iskar gas na CNG

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!