A YAU Juma’a aka ɗaura auren mawaƙin Kannywood, Musa S.J. Dikko.
An ɗaura auren sa da abar ƙaunar sa, Hauwa Salisu Adam, da misalin ƙarfe 1:40 na rana a Masallacin Juma’a na Sultan Bello da ke Unguwar Sarki, Kaduna, a kan sadaki N200,000.

Bayan ɗaurin auren, an yi walima a ɗakin cin abinci na Sadau’s Home da ke Titin Raɓah a Unguwar Sarki.
Walimar ta ƙayatar matuƙa, kuma mahalarta sun ci sun sha, abinci har barin shi aka yi.
A waɗanda su ka samu halartar ɗaurin auren da walima, mujallar Fim ta ga Sagir Baban Kausar, Auwal Hannun Dama, Jamilu Ɗan Masu Kuɗi, Albashir Yareema, Harith Mai Gula, Abubakar Mai Biyu-Biyu, Ɗanladiyo Mai Atamfa, Al-Amin E-Mana, Zayyanu Extra da S. Imam Fadare.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.

