• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Aikin bututun gas na AKK zai bunƙasa tattalin arzikin Arewacin Nijeriya – Minista

by WAKILIN MU
June 22, 2024
in Nijeriya
0
Aikin bututun gas na AKK zai bunƙasa tattalin arzikin Arewacin Nijeriya – Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar Da Kai, Mohammed Idris (na 2 daga hagu) tare da su Ministan Kuɗi da Tsara Tattalin Arziki, Wale Edun; Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Hadiza Balarabe; Ƙaramin Ministan Albarkatun Gas, Ekperikpe Ekpo, da Shugaban NNPC, Mele Kyari, lokacin ziyarar su ga wurin aikin tsallaka Kogin Kaduna da bututun gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK) a ranar Juma'a

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce aikin shimfiɗa bututun gas daga Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK) zai bunƙasa hanyoyin tattalin arzikin Arewacin Nijeriya.

A takardar sanarwa ga manema labarai da ya rattaba wa hannu, mai ba ministan shawara kan aikin jarida, Malam Rabiu Ibrahim, ya ce Idris ya bayyana haka ne a Kaduna a lokacin da ya kai ziyara wurin aikin bututun gas na AKK da ake yi a gaɓar Kogin Kaduna.

Sun je wurin ne tare da Ministan Kuɗi, Wale Edun; da Ƙaramin Ministan Albarkatun Gas, Mista Ekperikpe Ekpo, da kuma Shugaban Kamfanin NNPC, Mele Kyari.

A jawabin sa a wajen, Idris ya ce, “Aikin na AKK ya mayar da hankali ne wajen fitar da ɗimbin ƙarfin tattalin arzikin Arewacin Nijeriya. Gas ɗin da za a yi jigilar sa zai samar da makamashin da ake buƙata ga gidaje, kasuwanci, da masana’antu, sannan kuma zai ba da damar hadahadar sufuri da rage farashin sa.

“Ci gaba da aiwatar da wannan aiki, wanda shi ne babban aikin bututun gas na cikin gida a Nijeriya zuwa yanzu, wanda gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta yi, wata alama ce da ke nuni da ƙudirin Shugaban Ƙasa na bunƙasa masana’antu da cigaban tattalin arzikin kowane ɓangare na ƙasar nan.”

Wurin da ake aikin tsallaka Kogin Kaduna da bututun gas ɗin na AKK

Haka kuma ya yaba da aikin a matsayin mai muhimmanci ga cigaban masana’antu da tattalin arzikin Nijeriya a ƙarƙashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana shi a matsayin aikin bututun gas na cikin gida mafi girma a ƙasar.

Ministan ya kuma danganta cigaban tattalin arziki da tsaro, inda ya ce yawancin matsalolin tsaro da ake fama da su a Arewacin Nijeriya suna faruwa ne sakamakon taɓarɓarewar tattalin arziki, wanda za a iya ragewa ta hanyar samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki.

Ya ce, “Samar da makamashi a gidaje, gonaki, da masana’antu ya na da matuƙar muhimmanci ga samar da ayyukan yi masu yawa.”

Idris ya bayyana yiwuwar aikin zai taimaka wa harkar noma sosai a Arewacin Nijeriya.

Bugu da ƙari, ya yi nuni da irin tasirin da irin waɗannan ayyuka ke yi a faɗin ƙasar nan, inda ya ce a watan da ya gabata an ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan samar da gas guda uku a yankin Neja Delta.

A bayyana cewa a ranar Asabar mai zuwa zai yi wata ziyarar zuwa Jihar Rivers domin duba Aikin Tsallaka Kogin Ƙwara da Bututun OB3, wanda shi ma wani muhimmin aikin gas ne.

Idris tare da sauran manyan baƙin

Ya ƙara da cewa aikin na AKK zai tallafa wa Shirin Shugaban Ƙasa na Gas (Pi-CNG), wanda tuni ya jawo jarin sama da dalar Amurka miliyan 50.

Ya ce: “Wannan shiri na da nufin kafa CNG da samar da gas a faɗin ƙasar nan, tare da ƙara azama a Nijeriya na yin amfani da ɗimbin albarkatun gas.”

Idris ya bayyana jin daɗin sa kan manufar Shugaba Tinubu ta “Shekara Goma ta Gas,” wadda dama ce da za ta yi amfani da albarkatun gas na Nijeriya don kawo cigaban ƙasa.

Ya ce, “Aikin bututun na AKK wani ginshiƙin fata ne, wanda zai farfaɗo da tattalin arzikin dukkan ‘yan Nijeriya.”

Loading

Tags: AKK gasArewacin NijeriyaMohammed Idristattalin arziki
Previous Post

Minista Bagudu ya ba shugaban Hukumar Finafinai Ali Nuhu shawarwari

Next Post

Minista ya buɗe taron horas da ‘yan jarida kan yaƙi da aƙidun ta’addanci

Related Posts

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London
Nijeriya

Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

May 16, 2025
Next Post
Minista ya buɗe taron horas da ‘yan jarida kan yaƙi da aƙidun ta’addanci

Minista ya buɗe taron horas da 'yan jarida kan yaƙi da aƙidun ta'addanci

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!