RUNDUNAR ‘yan sandan Jihar Katsina ta ce ta kama mutum biyu da ake zargin su na da hannu wajen sace mahaifiyar shahararren mawaƙin siyasa, Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara).
Kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya bayyana haka a Katsina a yau a cikin wata sanarwa da ya fitar, wadda aka raba wa manema labarai.
Rundunar ta ce mutanen biyun da aka kama bisa zargin su na sa hannu a sace mahaifiyar mawaƙin su na amsa tambayoyi ne a rundunar, inda ta ce daga baya za ta ba da sanarwa kan cigaban da aka samu a kan lamarin.
Tun da farko sai da ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce shugaban ‘yan sanda na Ƙaramar Hukumar Ɗanja ya jagoranci jami’an tsaro zuwa wajen da lamarin ya faru domin kama waɗanda ake zargi da aikata laifin.
Ya ƙara da cewa ‘yan sanda sun yi nasarar damƙe mutum biyu waɗanda a yanzu haka su ke amsa tambayoyi a hannun jami’an tsaro.
Mujallar Fim ta ba da labarin yadda lamarin ya faru na sace mahaifiyar Rarara Hajiya Halima ‘yar shekara 75 a daren jiya Alhamis a garin Kahutu da ke Ƙaramar Hukumar Ɗanja ta Jihar Katsina.
A ƙarshe, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce bincike a kan wannan lamari na cigaba da gudana sannan ya ba da tabbacin kamo waɗanda su ka yi wannan ɗanyen aiki.