• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Nason Musulunci A Kirarin Hausa: Misalai Daga Kirarin Da Lawal Tsangaya Ya Yi Wa Mamman Shata

by DAGA IBRAHIM SHEME
September 4, 2018
in Mawaƙa
0
Alh. Muhammadu Lawal Tsangaya ... ya rasu cikin 1984

Alh. Muhammadu Lawal Tsangaya ... ya rasu cikin 1984

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Maƙala da IBRAHIM SHEME ya gabatar a taron duniya mai taken “International Conference On Mamman Shata” wanda Centre for Research in Nigerian Languages and Folklore, da haɗin gwiwar Department of Nigerian Languages da Department of Linguistics and Foreign Languages, Jami’ar Bayero, Kano, ta shirya, a BUK, Kano, a ranar Litinin, 3 ga Satumba, 2018

 GABATARWA

 Tasirin addini a rayuwar Bahaushe ba abu ne da zan iya yin cikakken bayani a kan sa a cikin ƙanƙanin lokaci ba. Amma dai zan so in fara da cewa: rayuwar Bahaushe da addinin sa na yi wa junan su shigar gizagizai, ko kuma in ce sun ɗaura auren zobe da junan su, tun daga haihuwa zuwa mutuwa, walau dai a rayuwar sa ta haihuwa ce ko mutuwa, a al’adance ne ko a zamanance, a zamantakewa ne ko a ɗabi’a, ba yadda za ka iya raba yadda Bahaushe ya ke rayuwar sa da addinin sa, ko dai na gargajiya (maguzanci) ko kuma na zamani, wato Musulunci ko Kiristanci. 

Zuwan Musulunci ƙasar Hausa ya zo da sauye-sauye da kuma wasu sababbin ɗabi’u, su ka yi tasiri a rayuwar Bahaushe, su ka mamaye rayuwar sa ta kowane fanni, musamman ɗabi’a, tunani da kuma adabi. Kusan ya zamana raba Musulunci da rayuwa, tunani, ɗabi’a da adabin Bahaushe da Musulunci tamkar yunƙurin raba hanta da jini ne. Kusan inda duk ka duba sai ka ga nason addini a cikin dukkan abin da ya ke yi na rayuwa, walau dai abin da ya ke ɗin ya zama daidai da koyarwar Musulunci ko kuma akasin haka. Amma dai abin lura shi ne daidai da ba daidai ɗin ba, dukkan su a mahangar Musulunci ya ke kallon su.

 Wannan taƙaitaccen nazari ba a kan abin da Mamman Shata Katsina ya yi ko ya faɗa aka yi shi ba, a’a, an yi shi ne kan wani abu da wani daban ya yi ko ya faɗa a kan Shatan. Na yi nufin in shirya wata miyar adabi, da kayan cikin Musulunci, inda zan zama ina mai haɗa miyar kuma ina bayani da irin kayan masarufin da na yi amfani da su wurin haɗa miyar.  

Abin nufi dai shi ne zan kalli tasirin da addinin Musulunci ya yi a salon kirarin Bahaushe, inda zan maida himma ne wurin yin bayani a kan kirarin da Alhaji Muhammadu Lawal Tsangaya ke wa ubangidan sa, Alhaji Mamman Shata. 

KIRARI A ƘASAR HAUSA 

Kirari wani muhimmin ɓangare ne a al’adar Hausawa, musamman a waƙa ko a waƙe. A kan yi shi cikin waƙa ko a wajen taro ko biki irin su naɗin sarauta ko a mahauta ko filin dambe ko wajen farauta ko wasan tauri da sauran su. Nau’i ne na yabo, amma ya bambanta da yabo domin shi tsagwaron zuga ne ko kambamawa. 

 Yawanci, mutum ɗaya ne ke yi wa wani mutum ɗaya kirari, kuma mutum ɗaya ake yi wa kirarin a lokaci guda. Haka kuma, mutum zai iya yi wa kan sa kirari, kamar yadda ’yan dambe ko ’yan kokawa ko ƙauraye ke yi.

 Ana yin kirari ga mawaƙi ko basarake ko attajiri ko mayaƙi ko malami ko maharbi ko ɗan dambe ko ɗan kokawa – kai, ko ma ɓarawo – don ƙara fito da bunƙasar sa ko gwarzantakar sa a fagen da ya yi fice. Sau tari, wanda ke zugar – wanda ake kira maroƙi ko mazugi – ya kan yi ƙoƙarin tunzura ko ingiza wanda ya ke yi wa kirari don ya yi wani abu ko ya ƙara azama, sannan ya taimaka wajen ɗaga darajar wanda ya ke yi wa kirarin, ya fifita shi a kan sauran mutanen da ke cikin fagen sana’a ko aikin mutumin. Haka shi ma wanda kan yi wa kan sa kirari, ya kan koɗa kan sa, ya nuna shi wani ne, don ya ɗaga darajar sa a wajen masu saurare.

 Kirari ya ƙunshi kalmomi kamar: “Kai ne wane ɗan wane jikan wane! Babu kamar ka! Ba a ja da kai! Kai ne ka yi abu kaza da kaza!” A wani kirarin, a kan ƙara da kalmomi na tsoratarwa ko firgitarwa saboda abokan gaba, misali a kira mutum Dodo. Wata sa’a har ashariya ko batsa a kan watsa a cikin kirari. Shi ma mai koɗa kan sa da kan sa ɗin hakan ya kan yi.

 Idan ana maganar waƙa, za mu iya cewa ta wani fannin akwai bambanci tsakanin maroƙi da mai yin kirari. Inda za a gane haka shi ne a yayin da mawaƙa da dama a ƙasar Hausa su na da maroƙi, amma ba kowanne mawaƙi ba ne ya ke da mai kirari. Maroƙi shi ne wanda ke yin ‘He!’ idan ana wasa, ya bayyana kyautar da wani ya yi wa mawaƙi, ko ya tayar da mawaƙi a lokacin da ya ke cikin waƙa ta hanyar jefa wasu kalamai waɗanda mawaƙin zai iya cafewa ya gina baiti ko ɗan waƙar sa na gaba, misali ya ambaci sunan ɗa ko mata ko ɗan’uwan wanda ake yi wa waƙa.Amma shi mazugi, zugar ce ya ke yi wa mawaƙi, ya koɗa shi, kafin ya fara waƙa. Ba a cika yin kirari a cikin waƙa ba, amma fa ana yi. Misali shi ne kirarin da Shago ke yi a tsakiyar waƙar sa da Bawa Ɗan’anace ya yi. Shi ma Shata, shi da kan sa ya riƙa yi wa Alhaji Liman na ’Yalleman da Alhaji Widi Usman Jalo (‘Widi ɗan Tijjani’) kirari a waƙoƙin da ya yi masu, waɗanda kusan gaba ɗayan su ma kirari ne. 

Sannan duk abin da ka ji a kirari ba lallai ne ya zama gaskiya ba; yawanci ma shaci-faɗi ne, misali a ce wane (wanda ake kambamawa) aljana ce ta goya shi ya na jariri ko kuma ya na zuwa sallar Asuba a Ka’aba sannan a gan shi ya fito daga gida da hantsi, ko a ce duk wanda ya ja da shi zai kurunce ko zai makance. 

A cikin wannan nazari, za mu kira mai yin kirari da mazugi, maimakon maroƙi, don bambance shi da wanda tsagwaron roƙon kaɗai ya ke yi. 

Mawaƙan Hausa masu mazugi sun haɗa da Hamisu Caji Sarkin Kiɗa, Surajo Mai Asharalle, Sani Sabulu Kanoma, Ali Makaho da sauran su. 

Alhaji Mamman Shata Katsina ya na daga cikin mawaƙan Hausa masu mazugi. Shi mazugin sa ma ba ɗaya ba ne, amma waɗanda aka fi sanin sa da su guda biyar ne: Lawal Tsangaya, Muhammadu Gizo, Garba Kora Ɗanmusa, Shehu Tsatso da Sabitu Katsina. A cikin waɗannan, Tsangaya ne babban, kuma shi ya fi yin fice, sannan kirarin da ya yi wa Shata ma an fi sanin sa. 

Wannan nazari ya ɗauki samfurin kirari guda uku da Tsangaya ya fi yi masa, waɗanda kuma su ne aka fi sani. Ya dubi yadda addinin Musulunci da addinin Maguzanci su ka yi tasiri a zugar da mazugin ke yi, wanda kuma ya yi daidai da yadda Shata ya riƙa gabatar da wasu daga cikin waƙoƙin sa. Nazarin ya dubi kalaman da Tsangaya ya yi amfani da su, waɗanda tushen su daga Musulunci ne, wasu kuma daga Maguzanci. 

ADDINI DA GARGAJIYANCI 

Kowace al’umma ta na bin bautar wani abu wanda ta ke ganin shi ne ya ke gudanar da rayuwar ta. Kafin bayyanar manyan addinan da aka sani yanzu, wato Musulunci, Kiristanci, Yahudanci da sauran su, al’ummomi kan yi bautar abubuwa daban-daban, wanda a cikin su su kan ware wani guda ɗaya a matsayin shi ne babban abin bautar su, wato allan su. Akwai masu bauta wa rana ko wata ko wani dutse ko bishiya ko gumaka ko dabba ko aljannu ko wani abin daban. Wasu al’ummar ma na bauta wa alloli da dama, ba guda ɗaya kaɗai ba. 

Hausawa su na da daɗaɗɗiyar al’ada wadda ta shafi addinin da su ke bi tun kafin zuwan Musulunci, wato Maguzanci. Addinin su ya ginu ne bisa imanin da su ka yi da cewa iskokai – wato aljanu – su na shafar rayuwar su.  

Kafin zuwan Musulunci ƙasar Hausa, Maguzanci ya na da ƙarfi sosai. Hausawa sun riƙa bauta wa iskokai ta hanyoyi daban-daban. Haka kuma sun yi imani da wasu halittun na daban masu kama da aljanu, misali dodanni, waɗanda halittu ne masu ban-tsoro waɗanda idan aka shige masu har kisa su na yi. Akwai kuma masu zuwa wajen wata bishiya kamar tsamiya ko wani dutse ko kuma wata dabba kamar maciji ko kada, su allantar da su a matsayin abin bautar su, wanda sun yi imani da cewa zai iya ba su kariya ko dukiya ko haihuwa ko ƙarfi ko nasara ko dai wani abin daban. 

Da Musulunci ya zo, ya tarar da wannan addinin na gargajiya, sai ya yi ƙoƙarin shafe shi. To amma bai cimma nasarar hakan ɗari bisa ɗari ba domin Maguzanci daɗaɗɗen addini ne wanda kau da shi farat ɗaya ya yi matuƙar wuya. Kuma duk da yake Hausawa sun rungumi Musulunci, sai ya kasance da yawa daga cikin su sun ci gaba da yin amanna da wasu sassa na Maguzanci. Hakan ya sa shugabannin addinin na gargajiya tare da muƙarraban su – kamar ’yan bori da wasu malaman tsibbu – su ka ci gaba da cin karen su ba babbaka. Hasali ma dai, wasu sun goya Maguzanci a gadon bayan Musulunci, su ka nuna kamar Ɗanjuma ne da Ɗanjummai. Shi ya sa a waƙar “Iro Sarkin Malamai” Shata ya na cewa: “Ga fa sallar nan su nai, / Sun aje ɗan gunki gida! /-/ Shi Iro bai alla biyu.” 

Gwama shirka da Musulunci da Hausawa su ka riƙa yi, ciki kuwa har da wasu sarakunan ƙasar Hausa ɗin, da malamai, ya na daga cikin manyan dalilan da su ka jawo Jihadin Sheikh Usmanu Ɗanfodiyo a shekarar 1804, ba domin komai ba sai domin tsarkake Musulunci daga Maguzancin da aka cusa a cikin sa. Ɗanfodiyo ya samu nasarar yin juyin juya halin sarauta tare da sauya tunani daga gwama shirka da Musulunci, to amma kuma akwai ɗimbin Hausawa da su ka ci gaba da bai wa iskokai muhimmancin da har su ka ci gaba da yin tasiri a rayuwar su ta yau da kullum. 

Za mu iya gane hakan daga ɗimbin misalan yadda mawaƙan Hausa su ke nuna cewar wasu mutane na da rauhanai ko aljanu. A kan kira Shata da “dodo” ko “mai rauhanai”, kuma shi ma ya kan kira kan sa “aljani” ko “dodo”. 

A wannan nazarin, za mu ga yadda Lawal Tsangaya ya ciyar da irin wannan tunanin gaba a kirarin sa. Kuma za mu ga yadda Hausawa Musulmai masu sauraren Tsangaya da Shata ba su ɗauki wannan a matsayin wani abin a zo a gani ba ballantana su ɗaura jihadi da wannan tunanin na fasihan biyu, wato makaɗin da mazugin sa. 

WANENE LAWAL TSANGAYA? 

Tarihin Ɗanliti Tsangaya ko Lawal Tsangaya ya yi kama da na Shata ta fuskoki da dama. Da farko dai, sunan su ɗaya, wato Muhammadu Lawal. Ɗanliti sunan rana ne, wato wanda aka haifa a ranar Litinin. A cewar Ya’u Wazirin Shata, tun ya na matashi ake masa laƙabi da “Tsangaya feshi!” saboda yadda ya iya feso magana.

 Kuma kamar Shata, shi ma Tsangaya a Musawa aka haife shi, kuma an haife shi ne a wajajen shekarar 1920, wanda hakan ya nuna kenan ya ɗan girmi Shata da shekarun da ba su fi uku zuwa huɗu ba.

 Sunan mahaifin Tsangaya irin sunan mahaifin Shata ne, wato Malam Ibrahim, amma ana masa laƙabi da Mairiga. Malamin allo ne. Asalin su, Barebari ne da su ka taso daga Zariya.

 Sannan kamar Shata, shi ma Tsangaya ya yi karatun allo a Musawa, amma bai yi na boko ba. Haka kuma kamar Shatan, shi ma ya shiga cikin yayin nan da aka yi na waƙoƙin Asauwara wanda matasan wancan zamanin – samari da ’yan mata – su ka yi. Ta wannan hanyar ne ya zama mawaƙi a dandalin Asauwara. 

 Haka kuma kamar Shata, shi ma mahaifin sa ya yi ƙoƙarin hana shi yin sana’ar roƙo saboda yadda ake kallon ta a ƙasƙance.A farkon zamanin ficen Shata a fagen waƙa, Shata ya yi nasarar yi wa matasan mawaƙa zarra. Saboda haka da yawan su sai su ka riƙa zanzarewa su na bin Shatan a matsayin ’yan amshi ko makaɗa. To, shi ma Ɗanliti Tsangaya sai ya zaɓi zama maroƙin Shata, maimakon ɗan amshi. Ta haka shi ma ya zama “yaron Shata”, amma kuma abokin sa ne. Shata ne ya biya masa kujerar aikin Hajji da ya yi a 1969. Daga tsakiyar shekarun 1930 har zuwa lokacin da ya rasu ranar 8 ga Disamba, 1984, a Funtuwa ya yi rayuwar sa. Kusan duk inda Shata ya shiga kuwa, su na tare. 

KIRARIN TSANGAYA

 Lawal ko Ɗanliti Tsangaya mutum ne mai fiƙira ta iya jera kalmomin zuga. Ya kan yi wa Shata kirari gab da lokacin da zai fara rera waƙa. Haka kuma ya kan ƙara wa Shata kalmomi idan ana cikin waƙa, kamar yadda ake ji a waƙar “Abu Kaita Sarkin Malamai” da waƙar “Na Gode Goshi Ta Ɗangude” da sauran su da dama. Kuma shi ne ya ƙara wa Shata kalaman nan na cikin Bakandamiyar sa, wato “Su ci abinci kowanne yai shakwara yai jamfa” da “In sun sami kuɗi sui auren zamani.” 

Kirarin da Tsangaya ya yi wa Shata kala uku aka fi sani: na farkon shi ne wanda ya ke farawa da faɗin “Sarkin kiɗan da ba a muzanta shi ko garin da ba a da Hausa”, da wanda ya fara da “Dodo yardar Allah!” da kuma wanda zan kira da “kirarin magajiyar karuwan Makka”. A cikin kowannen su, akwai nason addinin Islama. Manufa a nan ita ce Tsangaya kan ɗebo wasu kalamai daga cikin tarihi ko ruhin Musulunci ya ɗora su a kan kwarzanta Shata a fagen waƙa. Hakan ya nuna cewa Tsangaya mazugi ne wanda ya san tarihin Musulunci bakin gwargwado, kuma ya san gargajiyanci ko Maguzanci. A ina ya san waɗannan abubuwan? Amsa ita ce tun a garin su na Musawa, inda ya tashi a matsayin ɗan Malam, wanda ya yi karatun allo amma ba mai zurfi ba. Bugu da ƙari, tarihe-tarihen Musulunci da aka riƙa yaɗawa da fatar baki ko a wajen taron wa’azi sun shahara a ƙasar Katsina a wancan lokacin kusan ma fiye da sauran ƙasashen Hausa. 

Bayan haka, a wancan lokaci Maguzanci na da ƙarfi sosai a ƙasar Katsina. Akwai gidajen Maguzawa masu yawa. Tare da Maguzawa ake cin kasuwa kuma da su ake yin waɗansu hidindimu a cikin gari ko a gona ko a wajen farauta ko su (wato kamun kifi), sannan kowa na iya halartar bukukuwan su ya yi kallo, har ma ya ci abincin su. A waƙar “A Sha Ruwa Ba Laifi Ba Ne” Shata ya ambaci wasu daga cikin irin waɗannan Maguzawan da su ka shahara a wannan karkarar, wato irin su Ɗankilli Arne, Maidare da Ɗan’ali. 

i. “Sarkin kiɗan da ba a muzanta shi” 

A cikin wannan kirari, Ɗanliti ko Lawal Tsangaya ya kambama Shata da cewar shi ƙane ne na wani mashahurin masani a addinin Musulunci, wato Sasana. Sasana dai shi ne Hassana bin Thabit, sahabin Manzon Allah (SAW) wanda ya shahara a fagen waƙa. Shi ne aka ce ya na maida wa Yahudawa da martani a waƙe idan sun soki Annabi a waƙa.Haka kuma Tsangaya ya ce Shata ɗan’uwa ne na wasu Larabawan, fasihai, wato Alfazazi da Tanimuddari.  

Shi dai Alfazazi, cikakken sunan sa Sheikh Abu Zayd Abd al-Rahman al-Fazazi. Kalmar Al-Fazazi na nufin shi mutumin wani yanki ne mai suna Fazaz da ke arewa-ta-tsakiyar ƙasar Marokko, wato kamar a kira mutum Nagwambe ko Bazamfare ko Ɗandunawa. 

Malamin, wanda ya rasu a birnin Fez na ƙasar Marokko ɗin a shekarar 1230 miladiyya, shi ne ya rubuta shahararren littafin nan na dogon waƙe mai suna “Kasid al-Ishriniyyat fi Madh Saiyidna Muhammad”, wanda ake taƙaitawa a ce Ishiriniya. Haka kuma shi ne ya wallafa waƙen yabon kushewar Manzon Allah (S.A.W.) mai taken “Risalah ila draih an-nabi”, ko Risala a taƙaice. 

Shi kuma Tanimuddari, an faɗa mana a littafin “Labaru Na Da Da Na Yanzu” cewa ya na ɗaya daga cikin sahabban Manzon Allah (s.a.w.) wanda ya yi wani balaguro zuwa sama’u. 

A dai cikin wannan kirari, Tsangaya ya kira Shata da “Shaihun mawaƙa”, sannan ya faɗaɗa manufar sa da cewa shi ne “Sidi Abdulƙadirin duk mai bada waƙa”. A nan, ya alaƙanta shuhurar sa da ta Shehu Abdulƙadir Jilani, wato Sarkin Waliyyai kuma jagoran Ƙadiriyya, ɗarikar da ta fi kowace yawan mabiya a tsawon zamanin Shata. 

 Wato kenan Tsangaya ya ɗaga darajar Shata da shugabancin sa da yawan mabiyan sa, wato masoyan sa, zuwa matakin ta Abdulƙadir Jilani a cikin waliyyai – amma a fagen waƙa.

 Bugu da ƙari, ya kira shi da “‘La sharika’ na mawaƙa – wanda ba shi da abokin tarayya, / Ko ga wane mawaƙi in ya fito mawaƙi ne shi.”  

Nan kuma ya ɗauko waɗannan kalmomi ne daga Kalmar Shahada, amma ya yi sauri ya nuna cewa Shata ba shi da abokin tarayyar ne a tsakanin mawaƙa; ba ya na nufin tsakanin halittun Ubangiji ba ko allolin da wasu ke bauta wa. 

Mazugin ya ci gaba da cewa Shata “Hizbullahi” ne, wato tsarin Allah, sannan shi mutum ne “mai isimil azzamu”, wato a nan ya tsarkaka sunan sa. 

A bayyane ya ke cewa waɗannan sunaye an ɗauko su ne kai-tsaye daga tarihi da kuma ruhin addinin Musulunci. 

Wannan turbar ce ya ci gaba da tafiya a kan ta a cikin kirari na biyu, wato kirari mai taken “Dodo Yardar Allah”. 

 A wannan kirarin, Tsangaya ya zurfafa zugar sa domin ya ƙara ɗaga darajar ubangidan nasa, abin ya kai ƙololuwar da ma za a iya kallon sa a matsayin saɓo ko sakin baki.

 Tun a farkon wannan kirarin, ya maimaita alaƙoƙin nan da ya yi wa mawaƙin da su Alfazazi, Sasana da Tanimuddari, har ya ƙara da wani malamin, wato Shehu Jazuli, ya ce shi ma wan Shata ne. Sheikh Muhammad ibn Sulaiman Jazuli dai shi ne mawallafin shahararren littafin nan na “Dala’ilul Khairati”. 

Sannan sai Tsangaya ya ce:

 “Kun ga waɗannan, su ne su ka yabi Annabi,Da za su bar duniya su ka ce: ‘To Alhaji Mahamman Shata, kai ma ka yabi mutanen Annabin.’Shi ya sa idan Alhaji Mahamman Shata ya buɗe baki ya yabe ka, wallahi ba ka taɓewa har abada!” 

Da wannan kalamin, mazugin na nuna mana cewa akwai kusanci ta kai-tsaye tsakanin Shata da waɗannan manyan shaihunnai waɗanda su ka rayu tun shekaru masu yawan gaske da su ka shuɗe. 

 Duk da yake mu ba za mu ɗauki maganar kai-tsaye ba, wato mu kalle ta a haɗuwar ido da ido, za mu iya cewa mazugin ya na ba Shata wata keɓaɓɓiyar mu’ujiza ne, kwatankwacin wadda mabiya wasu ɗarikun ke bai wa shaihunnan su na yanzu da shaihunnan da aka yi a zamunnan da su ka shuɗe. Da ya ce “idan Alhaji Mahamman Shata ya buɗe baki ya yabe ka, wallahi ba ka taɓewa har abada,” faɗar sa ta yi daidai da wadda mabiya wasu ɗarikun ke yi game da shaihunnan su, wato idan har shehi ya yabe ka, to shakka babu ba za ka taɓa taɓewa ba. 

Tsangaya, har ila yau, ya bayyana cewar shi Shata “yardar Allah” ne, wato wanda Ubangiji (SWT) ya yarda da shi. Wannan yarda na nufin duk abin da ya furta ko ya aikata, to ba yin sa ba ne, kamar wahayi ne, kuma babu kuskure a ciki. Wannan magana ya ɗauko ta ne kai-tsaye daga cikin littafin “Arba’una Hadith” na al-Nawawi, musamman daga hadisin nan wanda ya ce idan Allah ya yarda da kai to ya zama jin ka, ya zama ganin ka, ya zama maganar ka, da dai sauran su.

 Akwai kuma inda Tsangaya ya siffanta Allah Mahalicci a wannan kirari da nufin kwarzanta Shata. Ya nuna cewa Shata ya bambanta da duk wani ɗan’adam da Allah ya halitta, wanda shi ya sa waƙar sa ta keɓanta. Ga abin da ya ce:

 “Zaki mai makogwaro, irin, ba irin namu ba ne na mutane maƙogwaran shi,A’a, maƙoshin sa ba irin namu ba ne mu,Wane mu mutane?Wane mu, maƙoshin mu da Allah ya halitta da nama da fata da ƙashi da daƙashi da ɓargo da jijiya da lakka da majina da mura da kwata da mashaƙo a cikin maƙogwaron mu?Shi ko da ɗanyen zinare Ubangiji ya halicci maƙogwaron Alhaji Mahamman Shata,Da Ubangiji ya gama halitta tai da ɗanyen zinari,Ubangiji kuma ya miƙe ya yi kirari,Ubangiji ya ce ya rantse da ikon shi,Wannan maƙogwaro na Alhaji Mahamman Shata ya yi shi ne don ya na ƙamna tai,Don ya gyara shi ne, ya yi ma mura kashedi: “Kul mura! Kul ki ka kama wannan maƙogwaro na Alhaji Shata!Ban da mura, ban da mashaƙo, ban da kwata, ban da atishawa ana cikin waƙan nan,Ban da mugun kaki a tofar;Ko ko tari ya sarƙe mutum,” duk an masu kashedi.Ba dai wannan maƙogwaro na Shata ba, har abada!”

 Mu lura da inda mazugin ya ce: “Da Ubangiji ya gama halitta tai da ɗanyen zinari, / Ubangiji kuma ya miƙe ya yi kirari, / Ubangiji ya ce ya rantse da ikon shi, / Wannan maƙogwaro na Alhaji Mahamman Shata ya yi shi ne don ya na ƙamna tai…” Wannan nuni ne muraran da yadda Allah ya halicci Annabi Adamu (A.S.) da matar sa Hauwa’u (R.A.). Adamu da Hauwa’u dai Allah ya halicce su ne kai-tsaye, aka gan su a matsayin baligai; ba wani ya haife su ba, su ka tashi daga jarirai su ka girma. Shi kuma Shata, a cewar mazugin sa, an halicce shi ne – ko mu ce an halitta maƙogwaron sa – da “ɗanyen zinari,” wato kenan ba a haife shi da maƙogwaro yadda aka san ana haihuwar sauran mutane da nasu ba.

Kwalin faifan garmaho na Mamman Shata daga kamfanin EMI

Haka kuma da ya ce, “Ubangiji kuma ya miƙe ya yi kirari, / Ubangiji ya ce ya rantse da ikon shi,” a nan ya siffanta shi ne da mutane masu tashi tsaye su yi kirari. Da ya ce, “Ubangiji ya ce ya rantse da ikon shi,” ya ɗauko wannan kalma ne kai-tsaye daga ayoyin Alƙur’ani masu nuna yadda Allah ya yi rantsuwa da wani abu mai bayyana ikon shi, misali a Suratul Asr inda Allah (SWT) ya yi rantsuwa da cewa, “Wal Asr innal insana la fi khusr”, ko Suratul Ƙamar inda Allah ya yi rantsuwa da wata, da Suratul Tinu inda Allah ya yi rantsuwa da itacen tinu da zaitun da dutsen Ɗurisinina da kuma birnin Makka (“gari mai aminci”).

 Bugu da ƙari, maroƙin na Shata, ko mazugin sa, ya ɗauko wasu siffofi da su ka keɓanta ga Annabi Muhammadu (SAW), ya liƙa wa Shata a fagen waƙa. Kamar yadda malamai ke faɗa, Annabi ne “khatimal anbiya’i” wanda ya yi daidai da “tammat bihamdihi”, wanda daga kan sa an rufe annabta har abada. Shi kuwa Tsangaya, ga abin da ya ce:

 “Shi dai kenan tammat bi hamdihi!Ba a yi ba, ba za a yi ba,Ba za a sake wani mawaƙi kama tai ba daga nan haw waccan abadar!” 

Haka kuma ya nuna cewa Shata ba zai mutu ba, zai ci gaba da rayuwa, ba wai a cikin waƙoƙin sa kaɗai ba, a’a har ma cikin siffar sa da wanzuwar sa ta ɗan’adam domin shi ba a ɗebar masa kwanaki a doron ƙasa ba. Cewa ya yi:

 “In ba kai ba ƙanen Tanimuddari, wane mawaƙi ne wanda Mahadi ya wo ma takarda ya ce kada yai nisa, kada Alhaji Mamman Shata yai nisa, sai yai kiɗa wurin bayyana tai?Ga shi ko sauran shekara dubu Mahadi zai bayyana,Shata na nan, na waƙa tai.Shi ba irin mu ba ne mutane: au sittina, au saba’inawwatun;Shi ya na nan har abada, haw waccan abadar.Dodo na Ali, ba fasawa, mai tambura na Bilkin Sambo,Sarkin kiɗan da ba shi mutuwa;Sun ma daidaita da mutuwa tun can a hanyar Barno,Da mota ta faɗi da mu, Mutuwa ta ce: ‘A’a Shata, tashi kai da iyalin ka! Shata ina ruwa na da kai!’ inji mutuwa.” 

A bayyane ya ke cewa wannan magana ta saɓa wa Musulunci, domin ta shiga wani hurumi na Ubangiji domin shi kaɗai ne tabbatacce, kadimi.

 A kirari na uku da mu ka yi nazari, wato na “Magajiyar Karuwan Makka”, bayan Tsangaya ya koɗa Shata ta hanyar danganta shi da su Sasana da Alfazazi da Tanimuddari, kamar yadda ya saba, sai ya kira shi da “khuɗubul fasahati” (Khuɗubi shi ne wanda ya kai ƙololuwa a sufanci), to amma khuɗubil fasahati ya kai ƙololuwa a fasaha kenan.

 Sannan ya ce Shata ne “nuruz zamani”, wato hasken zamani. Wannan kuma ya na daga cikin muƙaman da malamai su ka bai wa Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. Amfani da kalmomin Larabci ba tare da fassara su ba, kamar yadda Tsangaya ya yi a nan, ya alamta wani yunƙuri na addinantar da kirarin, kwatankwacin yadda malami mai wa’azi ke yi.

 Bugu da ƙari, ya taɓo batun aikin Hajji da Shata ya je a shekarar 1956, ya ce, “Shi ko da ya je Makka, ba sallah ta kai shi ba, dacewa ya yi ana sallah yai sallar.” A cewar sa, hasali ma dai Shata ya je Makka ne bisa gayyatar Sarkin Makka Masa’audu wanda zai aurar da ’ya’yan sa su 12, bayan ’yan majalisar Sarkin sun bada shawarar cewa duk Afrika mawaƙin da za a kira shi ne Mamman Shata Katsina. 

 Da Shata zai dawo gida bayan an ƙare bikin, waɗanda su ka rako shi gida su ne jagororin karuwanci a Makka da Madina da Jidda. Ga yadda Tsangaya ya zayyana zuwan nasu: 

“Bayan an gama biki, matan biki su ka rako shi su goma sha biyu har Kano:Da Lauratul Akhiru, magajiyar mata ta Madina,Da Badi’atuj Jimali, magajiyar mata ta Makka,Da Dunyazada, magajiyar karuwai ta JiddaDa Imtusankuru, magajiyar mata ta Masar wadda kyau ya hana ta mutu,Har da Baturiya ’yar gidan Sakina wadda ake ibar sawun ta anai ma mata hoda su na shafawa.Su su ka kawo shi har Kano, a taƙaice!”

 Daga jin wannan hikaya, za a ji kamar an ɗebo ta ne daga cikin littafin “Dare Dubu Da Ɗaya” domin wasu daga cikin waɗannan matan da ya ambata, a cikin littafin su ke. Babu ruwan sa da nuni da cewa a ƙasar Musulunci irin Saudi Arebiya babu magajiyoyin karuwai a birane masu tsarki, waɗanda kuma su ke tare da sarakuna da malaman ƙasar har su na wakiltar su!

 Tsangaya ya ƙera wannan hikayar ne ba domin akwai ta a tarihi ba sai don ya addinantar da kambamawar da ya ke yi wa Shata, wanda a daidai lokacin da ya ƙirƙiri kirarin ya kan yi mu’amala da mata masu zaman kan su da kuma maneman su ta hanyar yi masu zuwa bukukuwan su, ya waƙe su. Nuna cewa karuwai daga ƙasar da ruhin Musulunci ya samo asali, kuma su ne mafi kyau da isa a zamanin su, su ne su ka rako Shata zuwa gida wani salo ne na nuna isar sa a tsakanin mata Hausawa masu zaman kan su. 

Duk da yake hotuna da siffofin addinin Musulunci ne su ka mamaye waɗannan kirarin na Tsangaya, amma dai mazugin ya kuma sarƙo ɗan abin da ba a rasa ba daga Maguzanci. Misali, a cikin kowanne daga waɗannan kirari guda uku, ya riƙa kiran Shata “dodo”. Akwai kuma inda ya yi wa ubangidan nasa tambaya da cewa, “In ba kai ba, dodo na Ali, shin wane mawaƙi ne wanda ya ratsa teku da waƙa har aljanai su kai mashi guɗa, su ka ba shi raƙumin ruwa yai kiwo?”

 NAƊEWA 

Idan mu ka yi la’akari da wannan ɗan bayani da na gabatar, za mu fahimci cewa tasiri da yaɗuwar ilimin addini ya yi naso a cikin salon kirarin da Alhaji Lawal Tsangaya ke wa Alhaji Mamman Shata, musamman ilimin tarihi da kuma sufanci, wanda a wannan lokaci shi ne abin da ya fi ƙamari a tsakanin Musulmin Hausawa a arewacin Nijeriya.

 Za kuma mu fahimci yadda Bahaushe ke amfani da addinin sa da ilmin addinin domin ya ƙawata adabin sa.

 Wani abin lura kuma shi ne yadda aka hausantar da rayuwar Larabawa ta zama Bahaushiya domin ingiza wanda ake wa kirarin, ya yi wani abu na bajinta a fagen sa. Tunda in an lura, mun yi bayani a baya cewa akan yi wa mutum kirari ne walau don a sanya shi ya aikata wani abu da ake ganin in ba a bi ta wannan hanyar ba ba zai yi ba, ko kuma a yaba masa saboda wani abin ku zo ku gani da ya aikata.

Ibrahim Sheme shi ne marubucin littafin “Shata Ikon Allah!” Shi ne Daraktan Yaɗa Labarai a ‘National Open University of Nigeria’ (NOUN), Abuja.(An cire jerin ‘sources’ da ‘references’)

Loading

Previous Post

Hauwa Maina ta samu jika

Next Post

Ƙarairayi 16 a martanin Aliyu Ibrahim Kankara

Related Posts

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala

July 16, 2024
Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara
Mawaƙa

Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara

May 13, 2024
Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 
Mawaƙa

Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 

December 7, 2023
Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala
Mawaƙa

Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala

December 3, 2023
Next Post
Dr. Aliyu Ibrahim Kankara

Ƙarairayi 16 a martanin Aliyu Ibrahim Kankara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!