• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ministan Yaɗa Labarai ya kwaɗaita wa ‘yan kasuwar Faransa alfanun zuba jari a Nijeriya

by ABUBAKAR IBRAHIM
April 10, 2025
in Nijeriya
0
Ministan Yaɗa Labarai ya kwaɗaita wa ‘yan kasuwar Faransa alfanun zuba jari a Nijeriya
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jawo hankalin masu zuba jari daga ƙasar Faransa, inda ya jaddada masu irin sauye-sauyen tattalin arziki masu ƙayatarwa, damar kasuwanci mai faɗi da yanayin da ya dace da masu zuba jari yanzu a Nijeriya, a wani yunƙuri na Gwamnatin Tarayya na ƙara janyo jarin ƙetare na dogon lokaci.

A sanarwar da Rabiu Ibrahim, Mai Taimaka wa Ministan kan Harkokin Yaɗa Labarai, ya bayar, Idris ya bayyana ƙudirin sa na zurfafa dangantakar tattalin arziki da Faransa yayin da yake magana a Taron Kasuwanci na Nijeriya da aka gudanar a birnin Paris a ranar Alhamis.

Taron, wanda kamfanin Business France ya shirya, ya samu halartar kamfanonin Faransa fiye da 200 tun a shekarar 2023.

Idris ya gode wa kamfanonin Faransa da suka daɗe suna aiki a Nijeriya, irin su TotalEnergies, Lafarge, Peugeot, Danone, Alstom, Schneider Electric da sauran su, saboda gudunmawar da suke bayarwa a sassa daban-daban na ƙasar nan kamar makamashi, ababen more rayuwa, noma, lafiya da masana’antu.

Idris ya ce a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Nijeriya tana kan “tafarkin sauyi da ba a taɓa ganin irin sa ba” wanda Ajandar Sabunta Fata ke ɗauke da shi.

Ya ce: “Waɗannan sauye-sauyen tarihi na gina tattalin arzikin da ya fi gasa, mai gaskiya da amfanar masu zuba jari, suna mayar da Nijeriya ƙofar shiga kasuwar masu saye ta Afirka wadda ke bunƙasa, ƙarƙashin Yankin Ciniki Cikin ’Yanci na Nahiyar Afirka (AfCFTA).”

Wasu daga cikin sauye-sauyen da ya yi nuni da su sun haɗa da:

Daidaita tsarin musayar kuɗi, cire tallafin mai domin daƙile asara, tsarin farashin wutar lantarki da ya dace domin ɗorewar sabis.

Sauran sun haɗa da sauye-sauyen haraji da ke inganta gaskiya da sauƙaƙe kasuwanci, sababbin dokoki da tsare-tsaren kuɗi da ke ba da goyon baya ga masu zaman kan su, sauƙaƙe harkokin shigo da kaya ta hanyar National Single Window, da sauye-sauyen dijital ciki har da tsare-tsaren shige da fice.

Ministan ya ce Nijeriya tana da fa’ida ta musamman ga masu zuba jari: ita ce mafi girman tattalin arziki a Afirka, yawan jama’a fiye da miliyan 220 — fiye da kashi 70 nasu kuma matasa ne ‘yan ƙasa da shekaru 35 — da kuma shekaru sama da 26 na dimokiraɗiyya ba tare da katsewa ba.

Ya ƙara da cewa gwamnati tana tabbatar da cewa tattalin arzikin ƙasar yana gudana ne ƙarƙashin ƙa’idojin doka, tare da tallafin hukumomin da suka haɗa da CBN, NIPC, SEC, da FCCPC.

A daren jiya, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi dina a birnin Paris wadda Business France ta shirya, kafin zaman zauren tattaunawa kan harkar kasuwanci a Nijeriya domin samun faɗaɗa zuba jarin kamfanonin Faransa a ƙasar nan. A wajen dinar akwai Gwamnonin jihohin Kwara, Kaduna, Ondo, Legas, Ebonyi da Oyo.
Ministan da gwamnonin a wurin dinar

Ministan ya ce a cikin watanni 20 kacal da gwamnatin Tinubu, an sauya tsarin kuɗi na ƙasa, inda aka samu ƙaruwa da kashi 3.84 na GDP a zangon farko na shekarar 2024, da samun ƙarin kuɗin shiga fiye da kashi 20, tare da rage yawan kuɗin da ake kashewa wajen biyan bashi.

Ya ce: “Gwamnatin ta kasance mai ƙarfafawa wajen haɓaka sashen masu zaman kan su ta hanyar wasu muhimman shirye-shirye kamar Asusun Raya Ababen More Rayuwa na Sabunta Fata (RHIDF), Hukumar Bai wa Jama’a Lamunin Kaya ta Nijeriya (CrediCorp), Shirin Fadar Shugaban Ƙasa na CNG, Asusun Zuba Jari na Gidaje na MOFI (MREIF), da wasu da dama.

“Waɗannan shirye-shiryen suna shimfiɗa tubalin da za a iya dogaro da shi wajen jawo zuba jari na tiriliyan-triliyan na naira daga sashen masu zaman kan su a fannonin ababen more rayuwa, lamunin kayan masarufi, kiwon lafiya, gidaje, da sauran su.”

Ya kuma bayyana cewa bankunan Nijeriya suna ƙara faɗaɗa zuwa Turai, ciki har da buɗe ofisoshi a birnin Paris, yana mai cewa Nijeriya za ta ƙara samun wakilci a Faransa ta fannoni kamar ƙere-ƙere, fasaha da yaɗa labarai.

Ya gayyaci kamfanonin Faransa — musamman masu sha’awar harkar noma — da su ci gajiyar sababbin damarmakin da ke akwai a sashen kiwon dabbobi na Nijeriya, inda sabuwar Ma’aikatar Raya Kiwon Dabbobi ta buɗe ƙofofin sababbin haɗin gwiwa.

Ya ce: “Dole ne mu shirya wa gaba da ƙwazo da fata mai kyau, tare da ƙarfin gwiwar da kakannin mu suka nuna.”

A yayin zaman sa a Paris, Minista Idris zai gana da manyan hukumomin yaɗa labarai da al’adu na Faransa, kamar France Médias Monde, ARCOM, Ma’aikatar Al’adu, da Thomson Broadcast, domin ƙarfafa dangantaka tsakanin Faransa da Nijeriya a fannin watsa shirye-shirye da yaɗa labarai.

Loading

Tags: FaransakamfanoniMohammed IdrisShugaba Bola Ahmed Tinubutattalin arzikizuba jari
Previous Post

Ministan Labarai ya ƙaryata rahoton wai ya ce a yi watsi da damuwar Gwamna Zulum kan tsaro

Next Post

Minista ya sake jaddada ƙudirin sabunta kayan aikin watsa labarai na gwamnati

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Minista ya sake jaddada ƙudirin sabunta kayan aikin watsa labarai na gwamnati

Minista ya sake jaddada ƙudirin sabunta kayan aikin watsa labarai na gwamnati

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!