ƘWARARREN sanƙira, ko master of ceremony (MC) a Turance, Malam Kabir Sa’idu Bahaushe, zai ƙara aure a ranar Asabar mai zuwa a Katsina.
Za a ɗaura auren sa da santaleliyar abar ƙaunar sa, Zainab Abdullahi Matazu, da misalin ƙarfe 1:15 na rana a masallacin Bilal Bin Raba da ke Lowcost, Ƙofar Marusa, Katsina.
Kafin ranar, akwai bukukuwan da za a gudanar kamar haka:
Alhamis: za a yi dina da ƙarfe 8:00 na dare.
Asabar: za a yi yinin iyaye mata da ƙarfe 12:00 na rana a gidan su amarya.
Lahadi, kwana ɗaya da ɗaurin aure: za a yi walima da ƙarfe 3:30 na rana.
Kabir, wanda mazaunin birnin Katsina ne, ya nemi duk wanda bai samu damar halartar ɗaurin auren ba da ya yi masu addu’a shi da amarya.