A RANAR Alhamis, 30 ga Yuli, 2009 aka ba ni wani faifan sidi na bidiyo ɗauke da wata muhawara da aka yi tsakanin wasu malamai biyu: Malam Isa Ali Ibrahim Pantami da Malam Mohammed Yusuf. Ban san ko ɗaya daga cikin su ba, amma sha’awa ta ta in san su ta ƙaru ne a daidai wannan ranar. Dalili: a ranar ne ’yan sanda su ka bindige Mohammed Yusuf a hedikwatar su da ke Maiduguri. Mohammed dai shi ne shugaban ƙungiyar Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, wadda daga baya aka riƙa kiran ta Boko Haram, kuma sunan ta ya yi tambari a duniya.A lokacin, ni ne Editan jaridar Leadership.
A ranar da na samu bidiyon ne na zauna na kalle shi. Na yi sha’awar yadda muhawarar ta gudana tsakanin malaman biyu. Na farko dai dukkan su matasa ne, tsararrakin juna: Mohammed ɗan shekara 36 ne lokacin da su ka yi muƙabalar a cikin 2006, yayin da shi kuma Pantami shekarun sa 34. Na biyu, kowanne ya na ji da kan sa kan maudu’in zaman, wato dacewar karatun zamani wanda aka fi sani da karatun boko.
Kowannen su ya riƙa jawo aya da hadisi domin kare matsayin sa. Mohammed, wanda ya ce shi bai yi karatun boko ba, har cikin kundin Encylopaedia Britannica ya riƙa shiga ya na jawo hujja. Na uku, kowannen su shugaba ne na jama’a; yayin da Mohammed ke jagorantar Boko Haram, Pantami limamin masallacin Juma’a ne, ga shi kuma malami a Jami’ar Abubakar Tafawa-Ɓalewa da ke Bauchi. Na huɗu, muhawara ce wadda kamar babu tsama a cikin ta, musamman daga ɓangaren Pantami wanda har murmushi ya ke yi a lokacin gwabzawar tasu.Daga baya, mun dai ga yadda ta kasance da Boko Haram, wato yaƙin da ta ke yi da gwamnati da bala’in da hakan ya janyo: mace-macen dubban jama’a, tursasa jama’a zuwa gudun hijira da karyewar tattalin arziki tare da haifar da fargaba a yankin Arewa-maso-gabashin Nijeriya har ma da wasu sassan ƙasar nan.
Abin da yawanci ba a sani ba shi ne Dakta Pantami na daga cikin waɗanda su ka cutu daga bindigancin Boko Haram. Saboda ya ƙaryata aƙidar ’yan ƙungiyar, ya nuna ba ta da hurumi a Shari’ar Musulunci, sai zaman Nijeriyar ma ya gagare shi. Tilas ya gudu daga ƙasar. Ban tsammanin har yau ɗin nan ya na da cikakkiyar natsuwa game da tsaron lafiyar sa, musamman da yake Boko Haram sun nuna ba su yafe masa ba.
To, wai irin wannan mutumin ne, wanda ya sadaukar da rayuwar sa wajen yaƙi da ta’addanci ta hanyar kawo hujjojin da ke rusa aƙidar ’yan bindigar, wanda wani mai hankali zai fito ya zarge shi da mara wa Boko Haram baya. A ranar Lahadi da ta gabata wata jarida da ake bugawa a intanet wai ita ‘Independent Newspaper’ ta wallafa wani labari cewa wai gwamnatin Amurka ta saka sunan Sheikh Pantami a cikin jerin mutanen da ta ke sanya wa ido saboda ana zargin su da yin mu’amala da ƙungiyar ta’addanci. Jaridar ta ce wai Pantami, wanda a yau shi ne Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, abokin shawarar marigayi Mohammed Yusuf ne. Ta ƙara da cewa wai ya na da alaƙa da wani Abu Quatada al Falasimi da wasu jagororin ƙungiyar ta’addanci ta Al-Ƙa’ida. Wata jaridar irin ta, ‘Newswire’, ita ma ta kwafi wannan labarin ta yi tallar sa.
Abin mamaki, jaridun ba su kawo wata hujja ba illa sun fake da cewa wai wata majiya a gwamnatin Amurka ce ta ba su labarin. Sai dai gwamnatin Amurka ba ta amince da labarin ba; ofishin jakadancin ta da ke Abuja ya ce bai san da zancen ba.
Duk mai hankali idan ya karanta labarin zai lura da cewa kame-kame ne kawai aka shirya don a yaudari wanda ba zai iya yi wa jaridun tambayoyi ba. Ɗaya daga cikin tambayoyin ita ce: ta yaya Pantami zai zama aminin Mohammed Yusuf bayan tona shi da ya yi a muƙabalar su? Ta yaya Pantami zai zama aminin ƙungiyar Al-Qa’ida, wadda Boko Haram reshen ta ne, a yayin da Boko Haram ke farautar sa? Ko kuwa da ganin mutum da Mohammed Yusuf a hoto ko bidiyo sai a ce aminin sa ne? Idan haka ne, ai da an kama ɗimbin mutanen da Mohammed ɗin ya yi hoto da su a Borno da sauran wurare. Wani ƙoƙari da jaridar ‘Premium Times’ ta yi na gano gaskiyar labarin a wajen waɗannan jaridun biyu ya yi nasarar gano cewa ƙarya ce su ka shara.
Akwai yiwuwar wasu abokan gabar Pantami ne su ka kitsa wannan labarin ko kuma jaridun sun buga labarin ne a cikin jahilci ko kuma haɗin duka biyun. Idan bisa jahilci ne jaridun su ka yi wannan kwavar, to editocin su sun nuna ba su san abin da su ke yi ba, kuma sun zubar da ƙimar aikin jarida.
Da ma a yau ’yan kutse sun yi wa aikin jarida yawa saboda damar da intanet ta ba kowa. Babu ilimin aikin, amma sai mutum ya yi rajistar gidan yana kawai, ya riƙa wallafa shirme a matsayin aikin jarida. Idan kuma abokan gabar ministan ne su ka ɗauki nauyin su su ka buga labarin ƙarya domin cimma wata manufa, to a nan ma sun nuna ba su cancanci riƙe muƙamin edita ba; abin da su ka cancanci zama shi ne fursunoni. Na goyi bayan Pantami ya kai ƙarar su domin a bi masa haƙƙin sa.
Tun daga lokacin mujadalar Sheikh Pantami da Mohammed Yusuf ya samu abokan gaba, wato almajiran marigayin waɗanda a gaban su aka yi muhawarar. Idan an tuna, waɗannan mabiyan sun riƙa bin malamai da sauran manyan jama’a su na kashewa. Ana zargin su da halaka Sheikh Ja’afar da Sheikh Albani; akwai lokacin da idan an ji sun kashe Sheikh Pantami ba za a yi mamaki ba. Har yau ɗin nan Boko Haram ba su yafe masa ba. Ko a watannin baya, lokacin da ya fito da sabon tsarin rajistar layin waya, sun fito sun yi Allah-wadai da shi, har su ka ƙara nanata cewa jinin sa ya halatta. Dalili shi ne sun hango cewa yin rajistar zai iya sanyawa a gano wanda ke amfani da layin wayar, domin an ɗauki dukkan bayanan sa.
To amma kuma ƙullin sharri a kan Pantami zai iya ɓullowa daga wata kafar. Ko a aikin sa na minista ma, ya cimma nasarorin da zai baƙanta ran wasu. Tun ya na shugabantar hukumar NITDA ya kafa ginshiƙin ɗaga darajar Nijeriya a idon duniya a fagen kimiyya da fasahar zamani. Wasu sun ɗauka Shugaba Buhari zai sallame shi bayan zaɓen 2019, sai su ka ji likkafa ta yi gaba, an yi masa minista. Kuma bai bada kunya ba. Ya ci gaba da kawo kyawawan tsare-tsare a ma’aikatar sa, musamman wajen sauya mata fasali. Su ma kamfanonin waya, ba lallai ba ne duk su so shi. Haka masu amfani da waya ko kasuwancin layin waya.
Saboda haka, nasarorin da ministan ya samu sun isa a yi masa hassada. Ana yi masa kallon ɗaya daga cikin ministocin Buhari “masu aiki”. Ga shi matashi wanda Allah ya ba ilimin addini da na zamani, kuma ya na aiki da su yadda ya kamata. Akwai alamun idan ya ci gaba da tafiya a haka, to Allah kaɗai ya san bangon da zai taɓo.
Wani labari da na taɓa ji shi ne kila Pantami ya shiga siyasa. Har ana yi masa bushara da zama gwamnan Gombe a zaɓen 2023. Duk da yake bai fito ya tabbatar da maganar ba, akwai Gombawa masu son hakan ta tabbata. To idan hakan ne, tilas kuma a samu masu ƙin hakan ta tabbata. Su ma za su yi murna idan sun ji an watsa wa garin sa ƙasa tun kafin tafiya ta yi nisa.
Ko ma dai menene, masu hassada da nasarorin da Pantami ya ke samu a matsayin minista da kuma matsayin shugaban addini su sani cewa shi ba irin shugabannin da aka saba gani ba ne a Nijeriya, wato marasa kishin ƙasa ko marasa tsoron Allah. Mutum ne wanda ya san akwai hisabi a gobe ƙiyama kuma ba zai so ya tsaya a gaban Allah ɗauke da zunubin cin amanar jama’a ba. To, su sakar masa mara ya yi aikin da aka ɗora masa ba tare da tursasa masa da labarin ƙanzon kurege ba.
![]()








Very nice u