• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mawaƙa mu dawo hayyacin mu

by DAGA ABDULHAMID MUHAMMAD SANI
December 13, 2021
in Tsokaci
0
'Yan ta'adda irin waɗanda su ka addabi arewacin Nijeriya

'Yan ta'adda irin waɗanda su ka addabi arewacin Nijeriya

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SALAMU alaikum, ya ‘yan’uwa na sha’irai! Barkan mu da wannan lokaci. 

Ya mu ka ji da juyayin halin da yankin mu ya ke ciki na ruɗani da rashin tabbas?

Na rubuto mana wannan takardar don tunatar da mu kan wani abu da ya kamata mu nazarta.

Kamar yadda mu ka sani, Allah ya yi mana baiwar tsara tsararrun waƙoƙi kan duk abin da mu ka ƙudiri aniyar tsarawa a kan sa.

Mu na da ƙaƙƙarfar ƙungiya mai cibiya a Sashen Harsuna da ke cikin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya mai suna Gamayyar Marubuta da Manazarta Waƙoƙin Hausa. Da yawan marubuta waƙoƙin Hausa ‘ya’yan wannan ƙungiya ne.

Wannan ƙungiya ta na da tsarin shugabanci tun daga ƙasa zuwa akasarin jihohin mu na Arewa.

Duk da wannan cikakken tsari da mu ke da shi, duk da cikakkar sanayyar da mu ke da ita a kan marubuta waƙoƙin da su ka gabace mu, ta yadda waƙoƙin su su ka zama magani na fitar da al’ummomin su daga ƙunci zuwa walwala. Ba shakka, waƙa ta taka muhimmiyar rawa wajen ilmantarwa, wa’azantarwa, faɗakarwa, nishaɗantarwa da sauran su, amma har kawo yanzu marubuta waƙoƙin mu na Hausa na wannan lokaci, duk da yanayin da yankin mu ke ciki, a iya cewa kamar ba mu taɓuka komai ba a kan rubutattun waƙoƙin da za su isar da saƙon haƙiƙanin halin da mu ke ciki mara daɗi a yankin mu na Arewa.

Ko da yake dai wasu kaɗan sun bayar da gudunmawa a gasar rubutattar waƙa da Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sakkwato ta sanya, to amma bai kamata mu yi ta saka a wannan a lissafi ba, tunda ta gasa ce, duk da yake dai ita ma ta bada fa’ida da yawa.

Ba shakka, mu sha’irai mun kwan da sanin halin da al’ummar mu ke ciki. Ko mun manta da cewa “waƙa magani ce”?

A gaskiya, lokaci ya yi da ya kamata mu dawo hayyacin mu, mu yi amfani da alƙaluman mu cikin hikimar da Allah ya ba mu, ba tare da tsoro ko taraddadi ba, wajen yin abin da ya dace.

In so samu ne, a inuwar wannan ƙungiya tamu ta Gamayyar Marubuta Waƙoƙi, mu yi ƙoƙari mu ƙara tunatar da mahukunta nauyin da ke kan su na kare dukiya da rayukan talakawa.

Mu yi ƙoƙarin amfani da basirar mu wajen wayar da kan jama’r mu kan yin duk abin da za su yi su yi shi a kan bin dokokin addinin mu da ƙasar mu ta aminta da shi.

Mu sa hikimar mu, mu sa basirar mu don bada gudunmawar mu don fita daga halin ƙaƙa-ni-ka-yi da mu ke ciki.

Allah ya ba mu sa’a. Allah kawo mana mafita.

* Abdulhamid Muhammad Sani(Malumma Matazu) shi ne shugaban riƙo naGamayyar Marubuta da Manazarta Waƙoƙin Hausa na Nijeriya, reshen Jihar Katsina
GSM: 08037868097

Malam Abdulhamid Muhammad Sani (Malumma Matazu)

Loading

Tags: ArewaHausa.Jami'ar Ahmadu Bello.Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyomarubutamawaƙarashin tsarosha'irai.
Previous Post

Jan Hankalin ‘Yan Arewa Kan Yin Abin Da Ya Dace

Next Post

Hotuna: Ali Nuhu da matar sa a dinar auren Abdul D. One

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida)
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Abdul D. One da amarya Ummu-Salma su na taka rawa tare da kallon juna cikin farin ciki

Hotuna: Ali Nuhu da matar sa a dinar auren Abdul D. One

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!