A RANAR Asabar, 26 ga Nuwamba, 2022 aka ɗaura auren jarumar Kannywood, Amina Abdullahi, wadda aka fi sani da Amina Buzuwa da sahibin ta, matashin mai ɗaukar hoton bidiyo a Kannywood, Abdulazeez Muhammad Sani, wanda aka fi sani da Abdul Wassh.
An ɗaura auren su da misalin ƙarfe 11:00 na safe a Layin Malam Isah Hassan da ke ‘Yan Majalisu, Unguwar Dosa, Kaduna, a kan sadaki N150,000.

Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Aminu Haske, Aminu Jahilin Malami, Mustapha M. Shareef, da Ibrahim Yalawa.
A daren ranar ɗaurin auren, an shirya dina inda ‘yan’uwa da abokan arziƙi su ka halarta, su ka taya su murna.
Kafin ranar, an yi bikin Ranar Buzaye (Buzaye Day).
Da farko dai Abdulazeez mata biyu ya yi niyyar aure a rana ɗaya, domin har a katin gayyatar ɗaurin auren mata biyu ne, wato na Amina Buzuwa da misalin 11:00 na safe, da kuma na Khadija Abdullahi Baba da misalin ƙarfe 2:00 na rana, a Tudun Wada, Kaduna.

Sai dai kuma wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa ita Amina ce ta ƙi amincewa da auren ɗayar yarinyar, wanda ya sa dole aka fasa.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.
Wanna maganar ba haka take bah uban yarinya ya Hana auren sbd yace baxai hada yarinyar shi da wanna babbar mace ba kuma ga boyewa da sukayi sai bikin yana sauran kwana goma sannan mahaifin yarinyar yagano kuma ya binciko mgn bikin idan yace ba haka bane to ayi hirar dashi kuma khadija baba Abdullahi karamar yarinya ce me shekara 19 baxai yihu ahadata da wanna uwar matan ba