KWANAKI ina tsakar shawagi a duniyar gizo daga Fesbuk (Facebook) sai na ga an yi waje-rod da ni, su ka ce wai an kulle min akawun. Nan take kuma sai na ga suna na ya canja zuwa Williams Daniel.
Abin ya yi matuƙar ba ni mamaki, ganin dai ba wani abu na aikata wanda ba daidai ba, sannan ba wayo aka yi min aka ƙwace akawun ɗin ba, illa dai katsahan hakan ta faru.
Da Allah ya taimake ni sai kurum na ga sun turo min saƙo ta imel cewar na sake tantance kai na ta hanyar tabbatar da wasu bayanai da kuma katin shaida. Nan da nan kuwa na bi umarni. Ba tare da ɓata lokaci ba sai na ga an dawo da ni ruwa tsundum. Na yi hamdala da wannan ƙetare rijiya da baya da na yi.
A daidai lokacin da na ke kokawar ƙwacen kai na kuma sai wasu jama’ar su ka riƙa kira na domin neman taimako na, su na cewa su ma sun shiga irin wannan matsalar. Wasu an sauya musu suna, wasu an hana su kwamen, wasu an hana su rubutu, wasu ma ɗungurungum an daƙile su daga shiga akawun ɗin nasu. Iyakaci na kan ba su shawarar abin da za su yi irin yadda na yi. Wasu sun yi sa’a sun dawo, wasu kuwa sun tafi kenan sai dai su sake sabon lale.
Ganin haka ya sa na shiga bincike da ƙoƙarin gano musabbabin ƙwacen akawun na Fesbuk da Instagram da yanzu ya zama ruwan dare. Mu a ɗan taƙadirin sanin mu, sai mutum ya san cikakken bayanin wani sannan zai iya yi masa arufta (hacking). Ana amfani da hanyoyi iri-iri kamar Phising, Social Engineering, Baiting, Quad pro, Brute Force da sauran su. Haka kuma da yawan lokaci mu kan yi zargin wasu mahassada ne ke yi mana bi-ta-da-ƙulli su ke kulle mana akawun.
Duk da yake an sake bunƙasa waɗannan dabaru, yanzu abin ya wuce haka. Ba sai mutum ya san suna ko ‘password’ zai iya yin arufta ga duk inda ya ga dama ba; da zarar tsautsayi ya gitta, sai kurum gatarin gwari ya sauka. Ko shi kan sa Maku Zuka kwanaki wani ɗan ƙanƙanin yaro ya so ya yi masa arufta. Shi ya sa ma da ya ga uwar bari, ya bayyana kan sa fiye da baya kuma aka ƙara yi wa akawun ɗin nasa garkuwa ta musamman. A halin yanzu, ko hoton sa idan ka sa, ko ka ambaci sunan sa yadda kwamfuta za ta gane, nan take za a rafka maka sandar hukunci.
Wayoyin da mu ke amfani da su, su ne lambawan wajen jawo mana aika-aika. A wani bincike da aka yi a ƙasar Jamus, an gano cewa kamfanonin waya su na maƙala wasu irin manhajoji a ɓoye a wayoyin domin su riƙa samun bayanan sirri daga yadda ake amfani da su.
An tabbatar da cewar masu kamfanin wayar Gionee sun maƙala manhajar satar bayanai a wayar su, don haka a bara wata kotu a Chaina ta tabbatar da wannan zargi da cewar kamfanin ya saci bayanan mutane fiye da sau biliyan 3. Ta wannan hanyar an ce kamfanin ya samu kuɗi sama da Yuan miliyan 30.
Haka nan an tabbatar da cewa Tecno su na maƙala wata manhajar satar bayanai masu suna xHelper da Triada. Ta nan su ke iya tura wa mutane talla ko haka kurum wayar ta daina aiki da sunan ta cika, ko ta rage sauri, da dai sauran su.
An gano wayoyin Samsung da Redmi da Infinix da Rhino da Vivo da Lenovo da Huawei duk an yi bincike kuma an gano su na ɗauke da wasu ɓoyayyun masarrafai da ke satar bayanai sannu a hankali.
Sabon tsarin da Fesbuk su ka zo da shi na ba sani ba sabo ya sa da zarar sun ga wata manhajar a wayar ka ta na ƙoƙarin yin kutse, sai su yi wuf su kulle akawun ɗin. Ba za su buɗe ba har sai mutum ya bayyana kan sa. Wasu kuma su na samun nasarar kutsawar har su canja wa mutum suna da hotunan da bai ji ba bai gani ba.

A cikin waɗannan matakan kuwa, mai akawun ɗin ne ke jin jiki, walau an yi masa arufta ko Fesbuk ya daƙile aruftar. Idan mu ka yi duba na tsanaki, za mu ga cewar yawancin matsalolin da mu ke fuskanta a akawun ɗin mu na Fesbuk yawanci daga wayoyin mu ne.
Alamomin da za ka gane wayar ka na yi maka ɗan sandan ciki sun haɗa da:
# Da zarar ka buɗe datar intanet sai ka ga tallace-tallace na hotuna da ‘notification’ na wasu shiririta na shigowa.
# Wayar ta riƙa ɗaukar zafi na ba gaira ba dalili.
# Wayar ta yi nauyi ba ta aiki yadda ya kamata.
# Ka riƙa ganin saƙonni na wofi na bayyana a gilashin wayar, watau ‘pop ups’.
# Haka kurum ka ga kuɗin kira na raguwa ko data na ƙarewa da sauri.
# Idan ka ga wasu manhajoji na wasanni (games) ko caca da ba ka san lokacin da saka su ba.
# Wayar ta riƙa cunkushewa, ga wuri amma sai ta riƙa nuna cewar ta cika.
# In ka duba ma’ajiyar wayar, ka riƙa ganin hotuna da bidiyo da wasu fayiloli da ba ka san da zaman su ba.
# In za ka buɗe wata manhajar kamar Chrome ko Mozilla ko Xender sai wayar ta danƙare.
Maganin wannan shi ne ko ka gaggauta sake waya ko kuma ka rushe komai na ciki a sake sabon lale, watau ‘formatting’. Har ila yau, a guji shiga kowanne liƙau da aka gani a Fesbuk, a daina biye wa ‘game’ ɗin nan irin su OMG, Max Grid da sauran su. Sannan a riƙa cire kowacce manhaja da aka ga ta maƙale da Fesbuk da sauran su.
Masana na ganin zai yi wahala kamfanonin waya su daina maƙala manhajojin satar bayanai duk da cewar kamfanin Google mai Playstore na yin iya bakin ƙarfin sa na daƙile manhajoji masu almatsutsai, amma ba za su iya hana su yaɗuwa ba.
Wannan al’amari dai ya zama gobara daga kogi… KOWA YA YI TA KAN SA!
Ɗanladi Z. Haruna marubuci ne mazaunin Kano
