MAWAƘI a Kannywood, Malam Salisu Nuhu Mariri, ya ce saboda kishin ƙasa da ya ke yi ne ya sa ya shafe tsawon lokaci tare da kashe kuɗaɗe masu yawa wajen yi wa shugabannin Nijeriya waƙa.
A lokacin da ya ke tattaunawa da mujallar Fim a game waƙar shugabannin Nijeriya da ya ke kan aikin ta a yanzu, mawaƙin ya ce: “Tsawon lokaci na ɗauka, ko na ce shekaru, ina bincike da kuma rubutun waƙar wadda har zuwa yanzu ina cigaba da aikin, saboda a farko na fara yin ta ne odiyo, a yanzu kuma na mayar da ita bidiyo wadda kuma zan ɗauki lokaci mai yawa ina yin ta saboda waƙa ce da kullum za ta rinƙa ci gaba in dai an samu sabon shugaban ƙasa.”
Ya ci gaba da cewa, “Waƙa ce mai tafiya da tarihin ƙasar Nijeriya da kuma shugabannin da su ka yi mulki tun farkon ba da ‘yancin kai. Don haka tun daga kan Sa Abubakar Tafawa-Ɓalewa har zuwa kan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari babu wanda tarihin mulkin sa da irin cigaban da ya kawo bai shigo cikin waƙar ba.”
A kan irin zurfin binciken da ya yi, Salisu Mariri ya ce, “Na ɗauki lokaci mai tsawo ina bincike a wajen masa harkar mulki da malaman jami’a a game da tarihin ƙasar nan domin sai da na zama kamar ɗalibi a Jami’ar BUK, don haka manyan malamai kamar su Farfesa Ɗangambo, Ɗandatti Abdulƙadir, Sa’idu Muhammad Gusau, Abdalla Uba Adamu, duk sai da na kasance tare da su. Har gida na ke bin su don bincike da neman ƙarin bayani.

“Sannan sai da na zama ɗan gida a wajen marigayi Ɗanmasanin Kano, Maitama Sule, haka nan Umar Gimba wanda ya na da kusanci da marigayi Shehu Shagari. Don haka na yi yawo sosai, ba ma a Kano ba, har Abuja da Kaduna, a kan wannan waƙar.”
Mun tambaye shi ko wani ne ya ɗauki nauyin shirya waƙar? Sai ya ce: “Babu wani mutum da ya ɗauki nauyin shirya waƙar, ni da kuɗi na na ke yi. Don haka ma idan ina aikin kuɗi ya ƙare sai na samu lokaci idan kuɗi ya shigo na ci gaba. Amma dai babu wani da ya ɗauki nauyin waƙar, sai dai idan na samu gudunmawa ina buƙata.”
Idan kuwa haka ne, to ta yaya za a yi kuɗin sa su dawo? Amsar Salisu Nuhu Mariri ita ce: “To, a gaskiya har yanzu ina neman hanyoyin da kuɗin za su dawo ne, domin ka ga lokacin da na fara shirya waƙar tun a can baya akwai kasuwancin fim da na waƙa, amma a yanzu ka ga babu kasuwar da zan buga sidi na kai, saboda haka ina ƙoƙarin samar da hanyoyin da zan tallata waƙar da neman waɗanda za su ɗauki nauyin ta ko kuma a yi taron ƙaddamarwa. Kuma dai ina ganin lokaci ne da kuma damar da na samu a nan gaba zai tabbatar da yadda za a fitar da waƙar.”
Mawaƙin ya yi kira ga hukumomi da masu kuɗin mu da su tallafa masa “don ganin wannan waƙar ta samu fitowa.”
“Kuma ina kira ga jama’a, musamman matasa, da su kasance masu kishin ƙasar mu da kuma son cigaban ta. Ta haka ne za a samar da shugabanci nagari a shekaru masu zuwa,” inji shi.

