MASANA’ANTAR Kannywood ta na da ɓangarori na gudanar da sana’a masu yawan gaske, kuma kowane ɓangare zaman kan sa ya ke yi.
Aikin haɗa kayan magana, wato DJ, shi ma wani aiki ne mai zaman kan sa da ake buƙatar sa ko dai cikin fim ɗin ko kuma a wajen taro.
Saminu A. Hausawa ya na ɗaya daga cikin fitattun masu harkar DJ da ake yayin su a yanzu a Kannywood.
A cikin tattaunawar da mujallar Fim ta yi da Saminu, ya bayyana irin ƙalubalen da ke cikin harkar duk da yake wasu su na ganin ta kamar wasa.

Tun a farkon tattaunawar ya bayyana yadda ya fara harkar da cewa, “Ni da farko yaron aike ne a situdiyo har na zo na fara gane yadda ake kiɗa, na fara koya. Sannan kuma idan aka je wajen taro, mu ne masu haɗa kayan sauti da gyara lasifika a wajen, kuma daga haka har na zo na fara haɗa waƙoƙi a wajen taro.
“Kuma a wannan lokacin ina koyon yadda harkar DJ ta ke da yadda za a nishaɗantar da jama’a a wajen taro. To da haka mu ka saba har aka zo wannan lokacin da ake ganin mu a sahun gaba.”
Da mu ka tambaye shi yadda yanayin tsarin aikin su ya ke, kasancewar mutane su na kallon sa kamar wasa, sai ya ce: “Gaskiya aikin ba na wasa ba ne, domin samar da waƙar da mutane su ke so abu ne ba ƙarami ba, domin a cikin waƙoƙi sama da dubu biyu da su ke cikin kwamfutar ka ake so cikin daƙiƙa biyu ka saka waƙar da ake so. Ana cikin taro sai kawai a ce a saka mana waƙa kaza, to kuma a daidai lokacin ake so ka saka. Ka ga wannan ba ƙaramin aiki ba ne.”
Da mu ka tambaye shi ko a wane taro DJ ya fi shan wahala, cewa ya yi: “To gaskiya na halarci taruka da dama na yi DJ, kamar taron siyasa, na biki, na makarantu, na Mauludi. Amma babu taron da ya fi wahala kamar na biki. Saboda inda ake samun matsala shi ne sai wajen amarya su ce a saka musu waƙa, su kuma wajen ango su ce ba ta yi musu ba. Wani lokacin ka saka waƙar yara, iyayen su ce ba ta yi ba, ko ka saka waƙa mata su ce ai ta maza ce! To wani lokacin sai DJ ya rasa yadda zai yi, don haka a nan aka fi samun matsala, ƙarshe sai a tashi wasu su na jin haushin ka.”

Saminu A. Hausawa ya ja hankalin mutane da su riƙa yi musu uziri a wajen zaɓar waƙoƙin da su ke so a saka musu, domin babu yadda za a yi mutum ya iya faranta wa kowa da kowa rai.