FITACCEN jarumi a Kannywood, Ali Muhammad, wanda aka fi sani da Ali Artwork, ya bayyana mamaki da alhini kan ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa cewa wai ya rasu a daren jiya.
An dai wayi gari a yau da wannan labari mai rikitarwa.
Bayan mujallar Fim ta sha faman neman sa a waya, ta same shi da ƙyar, inda wakilin mu ya tambaye shi idan ya na da masaniya game da labarin. Sai jarumin na barkwanci ya amsa da cewa, “Wallahi ni wannan abu ya ɗaure min kai. Can cikin dare mata na ta ke ce min ga waya ta fa ta na ta ringin, sai na ce mata, ‘Kin ga yanzu fa dare ne, ni ba zan ɗauki waya ba.’ Kawai na koma na ci gaba da bacci na.
“Da asuba na tashi na tafi sallah. Na dawo masallaci sai na duba waya ta, na tarar da ‘missed calls’ da ‘messages’ da yawa, sai na ce ko wani abu ne ke faruwa? Kawai sai na ga wannan abin!
“To, da ya ke mun tashi da ruwa yau, shi ya sa ban yi bidiyo tun da safe na ƙaryata ba. Kiran da ka yi min yanzu na dawo daga yin bidiyon ne a waje. Amma kuma kiraye-kirayen da na ke samu shi ya hana ni ɗora bidiyon.
“Ni ban san me ya sa mutane ke irin wannan abin ba. Ban san menene ribar su ba in ya yi.”
Shin Ali ya san waɗanda su ka yi masa wannan abu kuwa? Sai ya ce, “Wallahi ni ban sani ba. Me ya sa irin waɗannan gidajen jaridun ba za su riƙa yin bincike kafin su bada labari ba? Ka na da shafin jarida a yanar gizo saboda ana bibiyar ka, kawai sai ka riƙa bada labarin ƙarya. Ai wannan ba daidai ba ne.
“Yanzu haka ‘yan’uwa na baki ɗaya an tada masu da hankali. Ga mutanen gari ma duk an tada masu da hankali.

“Ni yanzu kira na ga masu yi mana irin wannan abu shi ne su daina. Kuma ko yanzu idan na san wanda ya yi min haka, iyaka in yi masa nasiha, ba zan sa a kama shi ba ko a tozarta shi ba. Annabi Muhammadu (S.A.W), cewa ya yi ka faɗi alkhairi ko ka yi shiru.
“Yanzu waɗanda aka tada wa hankali ya za su da zunubin tada masu hankali da su ka yi?
“Allah dai ya sa mu dace. Su kuma Allah ya sa su gane.”
To amin, Ali.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa an sha yaɗa labarin ƙarya a ce wani ɗan fim ya rasu. Idan aka duba za a ga cewa kusan duk wani ɗan fim ko mawaƙi da ya yi fice an taɓa yaɗa cewa ya rasu.
A ‘yan watannin baya ma haka aka ce fitaccen mawaƙi Hamisu Breaker Ɗorayi ya rasu.
A safiyar yau Asabar, 16 ga Yuli, 2022 kuma sai ga na Ali Artwork.
An yi ta yaɗa hoton sa ɗauke da rubuta R.I.P.”, wato ‘Rest In Peace’ (Allah Ya Jiƙan Ka) da jar kala a jikin hoton.
Wata jaridar yanar gizo mai suna Debit.ng Hausa ma ta bada ɗan gajeren labarin cewa ya rasu a asibiti bayan doguwar jinya da misalin 11:15 na dare.
Wannan labari ya tada hankalin jama’a, musamman masoyan sa. Ko ina ka leƙa a Facebook da guruf-guruf na WhatsApp labarin da ake yi kenan. Sai dai kuma babu wani ɗan fim da ya ɗora cewa Ali Artwork ya rasu kamar yadda aka saba ganin ‘yan fim na yi idan Allah ya yi wa ɗaya daga cikin su rasuwa. Tun daga na nan za ka gane cewa akwai alamun babu gaskiyar a labarin rasuwar.
Kiraye-kiraye sun yi mana yawa daga jama’a don tabbatar da gaskiyar lamarin.
Haka shi ma Ali Artwork da ƙyar wakilin mu ya samu damar magana da shi, saboda yawan kiran da ya ke ta samu.
Comment:Allah ya haskakamai kabarinsa amin