• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Raddin minista ga gwamnonin PDP: An ƙi wayon! Tinubu ba zai yi murabus ba

by WAKILIN MU
February 19, 2024
in Nijeriya
0
Duk da matsalolin da ake ciki, Nijeriya za ta ci gaba da bunƙasa – Minista Idris

Alhaji Mohammed Idris

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa kiran da Ƙungiyar Gwamnonin PDP ta yi wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ya yi murabus ba komai ba ne illa wani yunƙuri na karkatar da hankalin jama’a daga mutanen da ya kamata su shagaltu da tallafa wa ƙoƙarin shugaban ƙasa na kawo wa al’ummar Nijeriya agajin gyaran tattalin arziki.

A cewar sa, bai kamata PDP da gwamnonin ta su riƙa nema, ta hanyar tsoratarwa, abin da su ka kasa cimmawa ta hanyar dimokiraɗiyya tun cikin 2015.

A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan aikin jarida, Rabi’u Ibrahim, ya bayar, Idris ya ce: “Bai kamata waɗanda su ka gaza kawo sauyi a lokacin da su ka samu dama mai tsawo ba su nemi katsewa ko karkatar da hankalin masu aiki kan manufar shugaban ƙasa da ‘yan Nijeriya su ka zaɓe su don aiwatarwa ba.

“Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, tun da aka kafa ta, ta ba da tallafin kuɗi ga dukkan gwamnatocin jihohi, ba tare da la’akari da ɓangaranci ba.

“Kazalika, cire tallafin man fetur, wanda aka yi ba zato ba tsammani, ya na ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, wato don ya ƙara kuɗaɗen shiga na ɗaukacin jihohi, ciki har da jihohin PDP. Wanda aka ba da yawa, ana sa ran samun da yawa daga wurin shi.”

Ministan ya ce, “Shugaban Ƙasa da gwamnatin sa sun amince da ayyukan da ba a kammala ba na farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar mu da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fara, ta hanyar shirye-shiryen da su ka mayar da hankali kan manyan ababen more rayuwa, walwala da jin daɗin jama’a, da ba da fifiko wajen samar da kayan aiki da kyautata wa sojoji da hukumomin tsaro, da kuma maido da Nijeriya turbar matsayi mai mahimmanci a tsakanin ƙasashe.”

Ya yi nuni da cewa tun daga shekarar 2014/2015 aka kawo ƙarshen Boko Haram da masu alaƙa da su, kuma a halin yanzu ana samun irin wannan gagarumar nasarar a kan ‘yan bindiga da sauran miyagun mutane.

A cewar sa, ‘yan Nijeriya dai ba su manta da cewa gwamnatin APC ce ta kawar da naƙasu da dama da gwamnatin PDP ta bari a baya ba, kamar neman tallafin man fetur da ‘yan kasuwar man fetur ke yi, da dawo da kuɗaɗen Paris Club, biyan fansho da ba a biya ba, da kuɗaɗen sallama daga aiki, da basussukan albashi da ake bin kashi daban-daban na ’yan fansho daga kamfanoni mallakar gwamnati da aka sayar da kuma waɗanda ake da su a yanzu.

Ya ce: “Manyan sauye-sauye a ɓangaren man fetur da PDP ta dinga tallatawa na tsawon shekaru amma ta kasa cimmawa – ƙaddamar da Dokar Masana’antar Man Fetur (PIB), sababbin matatun mai, da kuma sake fasalin waɗanda ake da su, da sauran su – su ne ainihin abubuwan da jam’iyya mai mulki ta APC ta yi.

“Dukkan waɗannan an yi su ne ba tare da samun ribar man fetur da gwamnatin PDP ta ci a tsawon lokacin da ta ke kan karagar mulki ba, sannan kuma a lokacin annobar Korona.

“Dole ne mu ci gaba da bayyana waɗannan hujjoji domin ’yan Nijeriya su san daga inda mu ke, kuma su yaba da abin da ake yi.

“Shugaba Tinubu ba zai taɓa gajiyawa da ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta a halin yanzu ba. Ba zai yi watsi da nauyin da ke kan sa ba, da jajircewa zai ci gaba da kokawa da shawo kan ƙalubalen da ke gaban sa, tare da aza harsashi mai ɗorewa ga sabuwar Nijeriya da ke tasowa.

“Har ila yau, ba zai ce bai san raɗaɗin sauye-sauyen da ake ci gaba da yi ba, ya kuma yi amfani da duk wata dama da za ta samu wajen tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa raɗaɗin sauye-sauyen ya ta’allaƙa ne da samar da arziki mai ɗorewa da cigaban ƙasa.

“Ga gwamnonin PDP, bari mu sake nanata cewa: Wannan ba lokacin da za a raba hankali ba ne. Lokaci ya yi da za a yi shirin aiki, don tallafawa da cika aikin Shugaban Ƙasa da gwamnatin sa.”

Loading

Tags: Bola TinubugwamnoniMohammed Idris
Previous Post

‘Yan Kannywood sun farfaɗo da gidauniyar tallafa wa iyalan mamata a wurin taron addu’ar Bintu ta ‘Daɗin Kowa’

Next Post

‘Yan guruf ɗin ‘Kannywood Family’ sun je dubiyar tsohuwar jaruma Halisa Muhammad da Maryam CTV

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
‘Yan guruf ɗin ‘Kannywood Family’ sun je dubiyar tsohuwar jaruma Halisa Muhammad da Maryam CTV

'Yan guruf ɗin 'Kannywood Family' sun je dubiyar tsohuwar jaruma Halisa Muhammad da Maryam CTV

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!