• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, July 26, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

An shiga tsananin jimami sakamakon rasuwar Umar Sa’idu Tudunwada

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
July 1, 2019
in Labarai
0
Marigayi Alh. Umar Sa’idu Tudunwada

Marigayi Alh. Umar Sa’idu Tudunwada

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

DA yammacin Lahadi, 30 ga Yuni, 2019 al’ummar Arewa su ka samu kan su cikin jimami tare da alhinin rasuwar furodusa, fitaccen ɗan jarida kuma tsohon shugaban Gidan Rediyon Jihar Kano, Malam Umar Sa’idu Tudunwada (Ɗanmasanin Tudunwada). 

 Allah Ya yi wa Umar rasuwa ne a sakamakon wani mummunan haɗarin mota da ya ritsa da shi a kusa da garin Kura, a kan hanyar sa ta dawowa daga Abuja. Motar sa ta yi karo da wani mai babur ne, inda nan take Umar ya rasuwa, yayin da matar sa Hajiya A’ishatu Sule (wadda a yanzu ita ce shugabar Gidan Rediyon Jihar Kano) da ’yar sa Maryam da direban sa Malam Ado Gauta su ka samu raunuka. 

 Ya zuwa lokacin rubuta wannan labarin tuni an sallame su daga asibiti sun koma gida.

 An dai yi jana’izar Umar a gidan sa da ke Hausawa Gidan Zoo da misalin ƙarfe 5 na yamma, inda shehin malami Malam Ibrahim Khalil ya jagoranci yi masa sallah. 

 Wajen jana’izar ya samu halartar ɗimbin jama’a, babu masaka tsinke. An binne shi a maƙabartar Tarauni.

 Cikin jama’ar da su ka halarci jana’izar akwai tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Sanata a yanzu, Malam Ibrahim Shekarau, da shugaban Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN), Farfesa Abdalla Uba Adamu. 

 Babu shakka, rasuwar Umar, wanda abokan sa ke kira da laƙabin UST, ta bar wani babban giɓi a rayuwar al’umma, musamman idan aka dubi irin gudunmawar da ya shafe tsawon rayuwar sa ya na bayarwa a ɓangarori da dama na ci gaban jama’a. 

Alhaji Umar ƙwararren ɗan jarida ne da ya shafe kusan shekaru 30 ya na bada gudunmawa a harkar yaɗa labarai.

 Ya fara aiki ne da tashar talbijin ta NTA Kano a 1980, daga bisani da aka kafa gidan talbijin na CTV (wato ARTV a yanzu) a 1983, sai ya koma can da aiki, inda ya shafe kusan shekaru 20 ya na aiki. Kuma ya taɓa zama wakilin gidan rediyon Jamus a Kano, wato Deuschewelle, sannan ya yi aiki da Sashen Hausa na gidan rediyon Muryar Amurka (VOA) na tsawon shekara uku. 

Ana yi wa Umar Sa’idu Tudunwada sallah

 Kafin nan, ya taɓa zama mai ba gwamnan Kano shawara kan yaɗa labarai. Haka nan ya taɓa zama editan mujallar ‘Concern’, kuma ya riƙe muƙamin Manajan Darakta na gidan rediyon ‘Freedom’. Haka nan ya riƙe matsayin Manajan Darakta na gidan rediyon Dandal Kura da ke yaɗa shirye-shirye da harshen Kanuri a Maiduguri. Daf da rasuwar sa ne ya sauka daga matsayin Manajan Darakta na gidan Rediyon Jihar Kano. 

 Bugu da ƙari, a lokacin da ya rasu shi ne mataimakin shugaban Ƙungiyar Editoci ta Nijeriya (Nigerian Guild of Editors). Sannan shi ne shugaban wani kamfani mai zaman kan sa da ake kira ‘Amara Publicity and Marketing Services Limited’.

 Ƙwarewar Umar ba ga yaɗa labarai kaɗai ta tsaya ba, domin kuwa ya ƙware a wajen rubuta labarin dirama da kuma tacewa. Haka nan ya na ɗaya daga cikin mutanen da su ka bai wa Kannywood gudunmawar da ba za a manta da ita ba a tarihin masana’antar, domin kuwa shi ne ya shirya fim ɗin ‘Bilkisu’ wanda ya ke mai dogon zango ne kuma an yi ittifaƙin babu wani fim irin shi da aka taɓa yi a masana’antar da ya kai shi kyan tsari da kuma cin kuɗi, saboda fim ɗin ya ci miliyoyin naira. 

 Sai da aka shafe tsawon wata biyu ana ɗaukar fim ɗin kafin a gama aikin sa. Ana cikin tace fim ɗin, daf da kammalawa, sai Allah Ya yi wa Umar rasuwa. Allah bai nufa zai ga fitowar sa ba. 

 Umar Sa’idu Tudunwada ya rasu ya na da shekaru 59 a duniya. Ya bar mata uku da ’ya’ya 21.

 Da fatan Allah Ya jiƙan sa, Ya kai rahama kabarin sa, amin. 

Loading

Previous Post

Fati Ladan da Shettima Yerima sun haifi A’isha Humaira

Next Post

Abin da ya sa na ke hidimar agaza wa marasa galihu – Rasheeda Maisa’a

Related Posts

Labarai

Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar

July 24, 2025
‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Next Post
Rasheeda Adamu Abdullahi

Abin da ya sa na ke hidimar agaza wa marasa galihu - Rasheeda Maisa’a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!