SANANNEN mawaƙin nan Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara) ya yi kira ga ɗaukacin al’ummar Musulmi da su riƙa taimakon na ƙasa da su domin samun falalar wannan rana ta hawan Arafa.
Rarara ya yi kiran ne a yau Juma’a, 8 ga Yuli, 2022 a cikin wani guntun bidiyo da mai taimaka masa kan harkar soshiyal midiya, Rabi’u Garba Gaya, ya fitar.
Taken bidiyon mai tsawon minti 2 da sakan 48 shi ne, “Tinatarwa Ga ‘Yan’uwa”.
A ciki, an nuno Rarara, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar siyasa ta ’13×13 Movement’, ya na riƙe da kwano a hannun sa ya na kaɗawa tare da rera waƙa irin ta almajirai masu bara.
A amshin waƙar Rarara na cewa: “A taimaka ma ɗan Malam zai soye, ko hanji ko hanta ko huhu.”
Mujallar Fim ta ruwaito cewa a baiti na farko ya na cewa:
“Idan ka na da sa Malam ko rago,
Ko kuɗi na sa Malam ko jogo,
Ko kuɗi na kaji ne ɗan waigo,
Ka taimaka akwai wani mai son soye.”
Bayan amshi, sai ya kawo baiti na biyu kamar haka:
“Mu taimaka wa junan mu da kayin mu,
‘Yan’uwan mu ko in ce dangin mu,
Mu waiwaya maƙota su yi shaidar mu,
Mu taimaka akwai wani mai son soye.”
Daga nan sai ya dakata ya yi jan hankali ga al’umma, ya na cewa, “To jama’a, ina yi wa kowa fatan alkhairi. Ina ma kowa murna ta riskar wannan rana ta Arfa, da wanda ya je Hajji da wanda bai je aikin Hajji ba.

“Wannan rana ce da duk wanda ya roƙi Ubangiji ya na amsa masa. Ta dalilin wannan na ke ƙara fargar da mutane wannan ranar fa duk abin da ka ke da shi ya kamata ka fito da shi ka taimaka wa mutane, domin Allah na taimakon wanda ke taimakon bayin sa.
“Duk abin da ka bayar, ka ba da ƙalilan ne, Allah ya ba ka mai riɓin-riɓin yawa. Saboda haka, ita ranar Arfa, duk buƙatun da ka ke buƙata a nan ake baje koli a faɗa, kuma Allah ya na amsawa.
“Ina kira, sai mun taimaki ‘yan’uwan mu da kan mu. Mu waiga maƙotan mu ko yaya abin ya ke, ko ɗan rabin kwano ko gwangwani ne ka taimaka wa wani don ya yi farin ciki, ma’ana kayan Sallah ne, naman Sallah ne, shinkafar Sallah ce, tuwon Sallah ne. Ka ga wannan wallahi kar ka duba ka ga ladan da za ka samu.
“Kuma ina kira ga waɗanda su ka tafi aikin Hajji, wasu sun tafi sauke farali, sun bar farilla a nan. Saboda haka ya kamata su waigo, tunda su na can yanzu zamani ne, za ka iya buga waya ka ce ga shi a yi kaza da kaza, a taimaki kaza, a yi kaza. Saboda in mu na taimakon mutanen mu – ni in taimaki na kusa da ni, kai ma ka taimaki na kusa da kai, wancan ma ya taimaki na kusa da shi – wallahi sai ka waiwaya ka rasa wani mai neman abin da zai ci da Sallah.
“Saboda haka, ni ina ƙara ba da shawara, ina ƙara kira ga al’ummar Musulmi, mu taimaki junan mu, mu kuma ƙara taya kan mu murna na cikar wannan ranar. Na ce Allah ya ƙara maimaita mana, Allah ya ƙara maimaita mana, Allah ya ƙara maimaita mana cikin aminci.”
Daga nan sai mawaƙin ya ci gaba da buga kwanon da ke hannun sa, ya na amshin waƙar da ya buɗe bayani da ita.