WASU suna kushe ilimi (satifiket) ko ƙoƙarin taƙaita amfaninsa. Sun ɗauka sana’a ta fi ilimi saboda talaucin da ake ciki. Malam ƙyale ilimi. Babu kamar sa. Ilimi ya wuce komai.
Da ilimi ake sana’a. Duk abin da ba a gina shi kan ilimi ba, ko da sana’a ce, amfanin sa taƙaitacce ne. Ranar da mai ilimi ya shigo cikin sana’ar ka za ka gane kuren ka don kan ka ce kwabo ya maka fintinkau.
Kuma a ilimin boko, babu wanda ba za ka mai da shi sana’a ba kuma ka rayu a kai. Tunani kawai ya rage maka sai ka gano ta wace hanya za ka mai da shi kuɗi. Ko Turanci kawai ka karanta kana iya mai da shi kasuwanci.
Na kan faɗa wa ɗalibai na har yau cewa kowane sakin layi (paragraph) a littafin boko kuɗi ne. Ina cikin koyar da ɗalibai dabarun ajiyar amfanin gona a 2018 sai na yi kiciɓis da wata saɗara (sentence) ɗaya da ta rage mani asara ta miliyoyin naira, ta kuma ƙara bunƙasa kasuwa ta da miliyoyin naira.
A 1992 da zan bar koyarwa a jami’a saboda halin tsanani da aka shiga, irin na yau, sai na rubuta wa kai na wasiƙa ta neman aiki. Na tilasta wa kai na tunanin yadda zan yi amfani da ilimi na na tsirrai da na yi digiri biyu a kai in samu kuɗi.
Bayan wuni biyu na shata hanyoyi huɗu. Allah ya taimaka ya yi mani fatahi a kan haka har na zauna cikin wadata ta tsawon shekara ashirin. Na yi ayyuka (projects) sama da 70 ta hanyar su. Ban daina amfani da waɗannan hanyoyin ba sai 2012 da Allah ya musanya mani da wacce ta fi su; duk dai cikin ilimin boko na ne.
Don haka a ci gaba da neman ilimi, kuma idan ba aikin takarda a yi sana’a ko a haɗa da ita.
Kar a yi ƙuruciya babu neman ilimi, kuma kar a girma babu sana’a, ko da ta ci da ƙarfi ce. Amma mafifici shi ne a yi amfani da ilimin wajen gina sana’a. Da sannu za a sha mamaki.
* Dakta Aliyu U. Tilde, wanda tsohon malamin jami’a ne, manomi ne kuma mai sharhi kan al’amurran yau da kullum. Yana zaune a Bauchi.