• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

by Ali Abubakar Sadiq 
March 7, 2025
in Tsokaci
0
Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

Wani sashe a fim din 'Yamutsin Rayuwa' na furodusa Wassh Waziri Hong

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MAGANAR aure ko saki a finafinan Kannywood ta fara zama abin tattaunawa tsakanin malamai a Yan shekarun nan. A bara, wasu malamai sun yi bayanin fatawar cewa Idan ka saki mace a fim ta saku. A bana ma, wannan zance ya sake dawowa ana ta ce-ce-ku-ce a kan sa, har ma da zancen ridda a fim.

Na farko dai abin da ya kamata mu fara ganewa shine kamar yadda Manzo ya faɗa: “Haram a bayyane take, haka shi ma halal a bayyane yake”. Sannan Allah ya bada hukunce-hukunce cikin Ƙur’ani waɗanda da su malamai ke gwamutsawa da wasu hadisai gwargwadon fahimtar su sannan su ba da hukunci. Ta wannan tsari, sannu a hankali magabata suka gina shari’ar Musulunci, akasari ƙarƙashin mazhabobi.

Yawancin malamai sun tafi kan cewa hukunce-hukuncen addini sun cika babu wani sabon hukunci da za a iya bijiro da shi, ko kuma dole sai dai kawai a bi hanyar magabata, amma na yanzu babu sauran ijtihadi da zaƙulo hukunci. Kowace ƙasar Musulmi, ban da tamu, za ka samu suna da majalisar fatwa domin tunkarar duk wata sabuwar matsala da ka iya bijirowa.

Zamani na caccanzawa yayin da yake bijiro da sabbin matsaloli waɗanda dole a samar musu hurumi na shari’a. Wannan tsari na gina ijtihadi a doron Ƙur’ani da Sunna da shi aka gina Shari’ar Musulunci kuma da shi ya kamata a ci gaba, amma wasu malamai sun kafe duk abin da magabata ba su ambato ba, to kawai a yi watsi da shi.

Gajeren misali na buƙatuwar malamai dole su rika ijtihadi domin samar da sabbin fatawa ko yin karo da abin da aka sani daga magabata na iya tasowa a ko da yaushe. Misali, idan ka ɗauki hukuncin zubar da ciki, wanda ƙarara ya saɓa wa Ƙur’ani da Sunna, amma misali yadda ‘yan ta’adda ke yi wa mata fyaɗe har su samu ciki, shin menene hukuncin mace da ta samu kan ta a wannan yanayi? Za ta iya zubar da wannan ciki? Abu ne da ke buƙatar malamai yin ijtihadi da ba da fatawa.

Idan muka koma kan sakin aure ko ɗaura shi a cikin fim, wanda wasu malamai ke ganin halastacce ne, ya kamata mu dubi abin ta mahanga da yawa.

Na farko dai shi fim a tsarin sa kowa ya haƙƙaƙe cewa gangan ne ba gaske ba, kuma a farko farkon fiƙihun Musulunci, abin da ya fara koya mana shi ne, “Dukkan ayyuka sai da niyya” wanda aka zaƙulo daga hadisin Umar cikin Al-Nawawi da kuma fassarar aya ta 100 a Suratun Nisa’i da ke nuna muhimmancin niyya a game da aiki. Shin fatawar saki a fim ta yi karo ko kuwa ta yi daidai da wannan aya da hadisai (Bukhari da Muslim duk sun ruwaito)?

Abu na biyu da ya kamata a ɗora kafin wannan fatawa shi ne: Duk mazhabobin nan guda huɗu sun gitta sharuɗɗa waɗanda sai sun cika aure ke tabbata. Cikin waɗannan sharuɗɗa akwai:

1. Sadaki, wanda Ƙur’ani ya tabbatar a matsayin sharaɗi cikin Ƙ4:4;

2. Shaidu: Wanda aka zaƙulo daga ayoyin Baƙara (Ƙ2:282) da Al Talaq (Ƙ65:2);

3. Amincewar ma’aurata: Wanda ayar Nisa’i ta kawo (Ƙ4:19);

4. Wali: Aure na ginuwa ne ta hannun wali.

Shin aure a fim ya cika duk waɗannan sharuɗɗa?

Allah ya gargaɗe mu cikin Suratul Ma’ida (Ƙ5:8): “Ya ku waɗanda suka yi imani…. kada ƙiyayya da wasu mutane su ɗauke ku, a kan ba za ku yi adalci ba”.

Wato idan ka lura, wasu malamai a ƙasar Hausa na far wa ‘yan fim a duk wata kafa da suka samu. Da a ce haka suke wa ‘yan siyasa da wataƙila mun ga canji. Akasarin malamai na yi wa masana’antar Kannywood kuɗin goro, maimakon ajiye komai a muhallin sa kamar yadda waccan aya ke umarta. Don ba ka ƙaunar wani, idan gaskiya ta zo ko a kan sa, wajibi ka bi ta. Kuma kowace sana’a ko jinsin al’umma akwai baragurbi, amma rashin adalci ne ka yi kuɗin goro. Allah ya gina tsarin ɗan’adam a bigire biyu.

Ƙ90:10: “Kuma ba mu shiryar da shi (mutum) ga hanyoyi biyu ba?”

Muna da saurin mantuwa, amma a garin Kano, irin baɗala da aka samu wasu malamai a kai, da ‘yan fim ne da sai an tsire su! Domin akwai babban malamin Juma’a da aka kama da luwaɗi a cikin harabar masallacin sa. Har gaban Sarkin Kano, marigayi Ado, maganar ta je. Sannan akwai wani malamin da ya far wa ‘yan fim amma aka kama shi a titi yana ƙoƙarin yin lalata a cikin mota da yarinya wadda yake riƙo a gidan sa a matsayin ‘yar sa. Wannan zai sa a yi tir da malamai? Ko kaɗan. Abin sani kawai a ko’ina akwai nagari da mugu.

Adalcin Musulunci shi ne kada don ba ka son wani ka gaza yi masa adalci kamar kowa. Auren fim, auren wasa ne kuma har abada a wasa zai zauna domin faɗakarwa kawai. Aure ne da bai cika kowane irin sharaɗi da malamai da kan su suke koyarwa a babin aure ƙarƙashin tsarin duk mazhabobin nan guda huɗu ba.

Malamai a Turkiya, Masar, da Saudiyya a yanzu sun gane muhimmancin fim a rayuwar ɗan’adam, don haka suka soka kan su a cikin harkar domin tsaftace ta a waɗannan ƙasashen na Musulmi.

Ba na mantawa, a lokacin dambarwar film village a Kano, a wani taro da muka yi a Hukumar Shari’a tare da su Malam Khalid, Iyan-Tama da wasu ‘yan fim da wasu malamai, na yi wa Malam Abduljabbar (lokacin yana Kwamishina na hukumar din) irin wannan tambayar cewa babu film village a ƙasashen Larabawa? Shin shigar malaman su cikin harkar fim bai ba su damar tsaftace ta a waɗannan ƙasashen ba?

Wannan masana’anta ta Kannywood, babu wata masana’anta da ke sama wa matasa ayyukan yi irin ta a Arewa a yanzu. Kuma bincike ya nuna cewa akwai kimanin sana’o’i 26 da ke alaƙantuwa da masana’antar.

Wajibi ne malamai, gwamnati da attajirai su karkata hankulan su wajen saka hannu sosai a wannan masana’anta domin ci gaba da samar da ayyukan yi, kuɗaɗen shiga da tsaftace ta.

‘Yan siyasa da suka fi kowa hankali a Najeriya wajen bin hanyoyin biyan buƙatun su, ba ku ga yadda suka rungumi wani sashe na masana’antar fim ba, kuma suke cin moriyar sa? To haka kowa zai iya cin moriyar wannan masana’anta idan an inganta da tsara tsaftace ta, ba mayar da ita abin tsangwama ko saniyar ware ba.

* Ali Abubakar Sadiq marubuci ne a Kano

Loading

Previous Post

Nijeriya za ta fara aiwatar da yarjejeniyoyin haɗin gwiwa da kafofin watsa labarai na Chana – Ministan Yaɗa Labarai

Next Post

Nijeriya za ta nuna gyare-gyaren tattalin arzikin Tinubu a taron kasuwanci a Faransa

Related Posts

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida)
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Tsokaci

Shekaru goma bayan sace ‘yan matan Chibok: Nijeriya ba za ta ƙara biyan kuɗin fansa ba

April 15, 2024
Next Post
Nijeriya za ta nuna gyare-gyaren tattalin arzikin Tinubu a taron kasuwanci a Faransa

Nijeriya za ta nuna gyare-gyaren tattalin arzikin Tinubu a taron kasuwanci a Faransa

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!