• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Auren Hausawa/Maguzawa kafin zuwan Musulunci

by DAGA YABI BABBA KAITA
January 2, 2017
in Tsokaci
0
Wasu 'yanmatan Hausawa

Wasu 'yanmatan Hausawa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
BAYAN zuwan Musulunci, Fulani da Maguzawa sun karɓi Musulunci, wanda hakan ya kawo canji sosai ga harkokin mu’amalar su ta yau da kullum, wanda ya haɗa da harkar kasuwanci da auratayya, don guje ma saɓa ma addini. Wannan hanya ce ɗaya da ta bambanta Hausawan yanzu da Maguzawa.
A lokacin da yarinya ta tasa, tun daga shekaru sha biyar zuwa sha takwas, a lokacin ne iyaye ke ma yarinya aure. Shi kuwa namiji sai lokacin da ya nuna sha’awar sa ga auren.
 
TSARANCE
 
Abu mafi mahimmanci a auratayya tsakanin saurayi da budurwa shi ne yarda da junan su. Tun daga lokacin kuma yarinya za ta sanar da mahaifiyar ta cewa za ta yi baƙo.
 
Wannan hanya ce ta gabatar da wanda ta ke so ga mahaifan ta. Kuma za a ba ta abin da za ta dafa don taryar shi, ko kuma shi da zai kawo mata ziyarar ya ba ta.
 
Wannan ziyara a na kiranta da “TSARANCE“.
 
Tsarance dai saurayi ne zai kai ma budurwar da ya ke so da aure ziyara, inda zai wuce kai-tsaye ɗakin da yarinyar ta shirya don taryar shi. Zai iske girki da sauran abin motsa baki da ta haɗa na yi mashi sannu da zuwa. 
 
Shi dai tsarance, saurayi da budurwa za su kwana su na hira har gari ya waye, in ma barci ya kama su to za su yi barcin ne tare a ɗaki ɗaya, amma ba za su yarda wani abu ya haɗa su ba face wannan hira. Idan budurwa ba ta gayyaci saurayin ta ba zuwa gidan su, shi ya na iya gayyatar ta zuwa gidan su. Duk wannan ana kiran shi tsarance. 
 
ƊAURA AURE
 
Ana yin shagulgula kafin a ɗaura aure, wanda ya haɗa da su lalle da raye-raye da waƙoƙi na gaɗa, duk cikin shagalin aure. Haka nan ana yin kayan lehe.
 
A ranar ɗaurin aure za a kira yarinyar a gaban kowa a tambaye ta ko ta taɓa sanin ɗa namiji. In ta yi ƙarya, dodo zai tona mata asiri (ta hanyar tsafin su). Za a yi mata faɗa ta yi abin kunya. Don haka babu budurwar da za ta yarda ta bi son zuciyar ta ta karya doka da al’adar su. 
 
A yayin ɗaurin aure wanda zai bada ta aure zai ce, “Shi wane ya ba wane auren wance, don haka ya ga ******** da zai ƙara yi mata magana”. (***Ƙunduma zagi ake yi). 
 
Daga nan za a kai amarya gidan ta. Amma ba za ta shiga ɗaki ba sai an cire zoben hannun shi an ɗaura mata a zane, sannan ya kama hannun ta su shiga. 
 
Daga nan za a fita a cashe ana rawa da waƙe-waƙe. A lokacin in ango ya kasa rawa, to cikin abokan shi duk wanda ya shiga filin rawa ya yi rawa da amarya, to mata ta zama tashi.
 
Wasu daga cikin al’adun Maguzawa ya haɗa da zagaya jan zakara kan amarya kafin a yanka a binne.
 
A cikin waƙoƙin da ake shi ango zai rinƙa faɗa ma mata abubuwan da ya ke so ta rinƙa yi a matsayin matar shi, ita kuma za ta ba shi amsa da cewa ta na tare da shi.
 
A wannan zamani abubuwa da dama sun canza, amma haka abin ya ke a zamanin baya.
 
*
 
Malama Yabi Babba Kaita ta gabatar da wannan maƙala ne a shirin ƙungiyar marubuta ta ‘Nagarta Writers Association’ da ke Katsina a shekarar 2006 

Loading

Previous Post

Babu wani littafin Hausa da ya tada ƙura kamar ’Yartsana – Ibrahim Sheme

Next Post

Ban Goyi Bayan Korar Dan Fim Daga Industiri Ba, Inji Ali Nuhu

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Gwamna Abba Kabir Yusuf
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Ali Nuhu

Ban Goyi Bayan Korar Dan Fim Daga Industiri Ba, Inji Ali Nuhu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!