• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, April 5, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ba mu hana mutum miliyan 7 kammala rajistar mallakar katin zaɓe – INEC

by DAGA WAKILIN MU
September 21, 2022
in Nijeriya
0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MAKO ɗaya kafin jam’iyyun da su ka takarar zaɓen shugaban ƙasa su fara yaƙin nan zaɓen 2023, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ba gaskiya ba ce zargin da ake yi ta tauye wa ‘yan Nijeriya milyan bakwai damar ƙasara rajistar da su ka fara ta manhajar INEC, domin mallakar katin rajistar zaɓe ba.

Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran INEC, Mista Festus Okoye, ya fitar, ya bayyana cewa hukumar ta bayar da isasshen lokacin da duk wanda ya fara yin rajistar mallakar katin zaɓe a manhajar INEC, to ya je cibiyar yin rajista ido-da-ido ya kammala rajistar sa.

Okoye ya ce duk waɗanda ba su kammala ba, ko dai sun fara ne su ka watsar, ko kuma sun fara, daga baya kuma ba su kammala ba, sai su ka koma a cibiyoyin rajista ido-da-ido domin su yi a can ɗungurugum.

Ya ce: An jawo hankalin INEC dangane da wasu rahotannin da ake yaɗawa cewa ana zargin INEC da tauye wa mutum milyan bakwai damar kallama rajistar su ido-da-ido, wadda su ka fara a shafin manhajar INEC ta intanet.

“To ya kamata a sani cewa a gaskiya INEC ba ta tauye wa kowa damar kammala rajistar mallakar katin zaɓe ba. Don haka rahotannin ba gaskiya ba ce, ƙarairayi ne kawai.

“Tun a ranar 24 ga Yuni, 2021 INEC ta ƙirƙiri tsarin fara yin rajistar mallakar katin zaɓe ta manhajar hukumar. Ta yi haka domin rage wa jama’a jeƙala-jeƙala da ɓata lokaci a wurin yin rajista ido-da-ido.

“A bisa wannan tsari, idan mutum ya fara rajista a manhaja, to daga baya zai samu lokaci ya je cibiyar yin rajista ido-da-ido, inda za a ɗauki hoton sa da tambarin yatsun hannun sa, domin kammala rajista, inda daga nan sai ya jira mallakar katin shaidar yin zaɓe (PVC).” Inji Okoye, wanda Kwamishina ne na Ƙasa, kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da kan Jama’a na INEC.

“Mutum 10,487,977 su ka shiga manhajar INEC domin fara yin rajista, amma a cikin su, yayin da 3,444,378 ne kaɗai su kammala yin rajistar a cibiyoyin rajista ido-da-ido.

“Daga cikin 7,043,594 waɗanda ba su kammala yin ta su rajistar a cibiyoyin rajista ido-da-ido ba, mutum 4,161,775 sun yi ƙoƙarin fara yin rajista ta cikin manhaja, amma sai su ka watsar, su ka koma cibiyoyin rajista ido-da-ido su ka yi kai-tsaye.

“Wasu 2,881,819 kuma sun kammala fara rajista a manhaja, amma ba su kai kan su cibiyoyin rajista ido-da-ido sun kammala ba.” Cewar Okoye.

Idan ba a manta ba, kwanan baya ne dai ƙungiyar SERAP ta jagoranci wakilcin mutum 24 waɗanda su ka shigar da INEC ƙara a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, su na neman kotu ta tilasta wa INEC cewa ta ba su dama, su da sauran ‘yan Najeriya milyan 7 su kammala yin rajistar su da su ka fara.

A ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1662/2022, sun shaida wa kotu cewa ba su samu damar kammala rajistar su ba har wa’adin da INEC ta gindiya za a rufe yin rajista ya cika.

Loading

Tags: Festus OkoyeINECrajistar zabeSERAPzaben 2023
Previous Post

A baya na ɓoye kai na, amma yanzu zan fito duniya ta san ni, inji Sani Liya-Liya mai waƙar ‘Sambisa’

Next Post

Cewar Rikadawa: Ba mu kafa ƙungiyar 13×13 don mu karya wasu ba

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Rabi'u Mohammed Rikadawa

Cewar Rikadawa: Ba mu kafa ƙungiyar 13x13 don mu karya wasu ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!