• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ba za mu tace finafinan kamfanoni marasa rajista ba, inji Gwamnatin Tarayya

by DAGA ALI KANO
June 29, 2022
in Labarai
0
Ba za mu tace finafinan kamfanoni marasa rajista ba, inji Gwamnatin Tarayya
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNATIN Tarayya ta bayyana cewa ba za ta tace duk wani fim da wani kamfani maras rajista ya miƙa mata domin ta duba ba.

Ta ce kamfanoni masu lasisin rarraba finafinai (distributors) kaɗai ne za a karɓi finafinan su domin tacewa.

Hukumar Tace Finafinai da Bidiyoyi ta Nijeriya (NFVCB) ita ce ta bayyana haka a cikin wata takarda da ta aika wa shugabannin ƙungiyoyin ‘yan fim masu rajista, da rassan su da kuma sauran masu ruwa da tsaki a harkar shirya finafinai a Nijeriya.

Mataimakin shugaban ma’aikata na Babban Sakataren hukumar, Mista  Ogbonna Onwumere, shi ne ya rattaba hannu a kan takardar mai ɗauke da kwanan wata 28 ga Yuni, 2022.

A cikin wasiƙar, wadda aka miƙa wa mujallar Fim kwafe ɗin ta, hukumar ta ce ta lura da cewa akwai waɗansu kamfanonin rarraba finafinai waɗanda lisisin su ya ƙare amma “har yanzu su na yawo su na faɗin cewa wai su ma kamfanonin rarraba finafinai ne.”

Wasiƙar da Hukumar Tace Finafinai da Bidiyoyi ta Nijeriya ta tura wa mashirya fim

Hukumar ta ce domin magance wannan matsalar, ta kammala rubuta jerin dukkan kamfanonin masu rarraba finafinai waɗanda ke da cikakkiyar rajista da ita daga ranar 27 ga Yuni, 2022.

Ta ce: “Wannan ya yi daidai da Sashe na VI na dokar hukumar, wato Act 1993 CAP N40 LFN 2004 da Dokokin 2008, wadda ta ce ‘ba a amince wa duk wani mutum ya yi harkar rarraba ko nuna finafinai ko bidiyoyi ba har sai ya na da lasisi wanda wannan Hukuma ta ba shi a ƙarƙashin wannan Dokar’.”

Hukumar ta yi kira ga masu shirya finafinai da su yi hulɗa da kamfanonin rarraba finafinai waɗanda ke cikin jerin sunayen da ke wajen ta domin su kauce wa ƙorafin ɓata lokaci wajen ba su satifiket ɗin tace fim ɗin su.

Ta ce: “Ana shawartar masu shirya finafinai waɗanda su ka miƙa finafinan su ta hanyar kamfanonin da ba su cikin wannan jerin sunayen da su rubuto takarda ga Hukumar ta neman sauya kamfanin rarraba fim, idan ba haka ba kuwa Hukumar ba za ta tace fim ɗin su ba.”

Loading

Tags: distributorsdokakamfanonin rarraraba finafinaiƙungiyoyilasisiNFVCBOgbonna Onwumeretace finafinai
Previous Post

INEC ba za ta rufe rajistar zaɓen 2023 a ƙarshen Yuni ba, inji Farfesa Yakubu

Next Post

Cewar Hadiza Gabon: Ƙarya ne, ba ni da wata alaƙa da Shehu Gabam

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Hadiza Aliyu Gabon

Cewar Hadiza Gabon: Ƙarya ne, ba ni da wata alaƙa da Shehu Gabam

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!