BAKIN DA ALLAH YA TSAGA. Wannan jumlar ita ce babbar madogarar Bahaushen da ya ɗauko aure ba bisa tsari da lissafi ba. Da yawan mu na ƙara aure ba bisa tsari ko cancanta ko kuma yadda Allah ya yi umarni ba. Mu na ƙara aure ne bisa son zuciya, rashin lissafi da sha’awa.
Mutumin da ke ɗaukar albashin dubu arba’in, ya na da mace guda da yara biyar. Albashin bai ƙaru ba, bai kuma sami wata sana’ar a gefe guda ya na yi ba, kawai wani lokaci mutum zai samu, sai ya takure matar sa da yaran shi ya shiga adashi a ofis. Albashin sa na dubu arba’in zai raba gida biyu, ya dinga zubin dashi da rabin. Kar ka ɗauka adashin na sayen fili ne tunda ya na gidan haya; adashin aure ne, kuma ɗaukar farko ya ke so saboda an sa masa rana. Idan ya ɗauki adashin sai kuma ya ciwo bashin banki yadda kuɗin za su isa aure da biyan hayar shekara guda na wajen da za a ajiye amaryar.
Bayan tarewar amarya, ga bashin adashi ga bashin banki. Ga sabuwar amarya ga kuma bayin Allah uwargida da sauran yara a gefe guda. Ba a maganar kuɗin makaranta da sauran mas’alolin rayuwa. Samu ya ragu, nauyi ya ƙaru.
Ana tsaka da haka amarya za ta fara laulayi, a shiga zaryar asibiti da kemis, sai kuma haihuwa da maganar suna. A nan kuma sai ya karɓi babur da ake raba bashi a ofis. Ga takarda an cike ta karɓar bashin babur, amma a zahiri kuɗin babur ɗin za a bayar: a takarda ya karɓi babur a dubu ɗari uku, wacce ita za a ci gaba da cirewa daga albashin, amma kuɗin da za a ba shi bai fi dubu ɗari da ashirin ba.
An yi hidimar suna an gama sai kuma maganar biyan haya. Nan ma sai a ƙara karɓar wani babur ɗin a karyar.Wani lokacin za ka sami ma’aikaci mai ɗaukar albashin sama da dubu hamsin, amma a duk wata bai fi ya tashi da canjin dubu goma ko ƙasa da haka ba.Kenan rashin lissafi da son yin jima’i da gamsarwa ta ‘yan mintuna sun jefa rayuwar yara cikin garari. Yaran za su tashi babu cikakkiyar kulawa da tarbiyya, ilmi kuma – wanda shi ne gishirin rayuwa – sai abin da Allah ya yi.
Da yawa mun kasa gane cewa wannan rashin lissafin shi ya haifar da rashin tsaro da ta’addanci da mu ke fama da su. Ko da yake na san da wuya mutane su amince da ni. Kenan akwai mamaki a ce abin da mutum ke faɗi daban da abin da ya ke aikatawa.
Mun san mutane da dama da su ke da damar yin mataye sama da huɗu idan ana yi, amma ba su yi ba kuma su ne kan gaba wajen kira da a ƙara aure kuma a ci gaba da haihuwa gaba-gaɗi.
Ba mu fi Larabawa Musulunci ba, ban ce kuma sun fi mu ba, amma ba na tunanin su na wannan lissafin Dokin Ranon.
Auwal Ɗanborno marubuci ne kuma manazarcin al’amuran yau da kullum, wanda ke zaune a Kano