• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ban ja baya da harkar fim ba, na koma gefe na zura wa ‘yan Kaduna ido ne – furodusa Lamaj

by DAGA ABBA MUHAMMAD
June 23, 2023
in Labarai
0
Hajiya Fatima Ibrahim Ahmed (Lamaj)

Hajiya Fatima Ibrahim Ahmed (Lamaj)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

TSOHUWAR shugabar Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kaduna, Hajiya Fatima Ibrahim Ahmad (Lamaj), ta bayyana cewa ba ta ja baya da harkar fim ba, ta dai koma gefe ne don ganin irin abubuwan da ke wakana yanzu a masana’antar.

Lamaj ta yi wannan bayani ne yayin da ta ke tattaunawa da mujallar Fim, bayan an daina jin ɗuriyar ta gaba ɗaya a kan harkar masana’antar Kannywood.

Ta ci gaba da cewa, “Amma alhamdu lillahi, akwai fim da na ke so na yi kwanan nan in-sha Allahu nan da bayan Sallah. Fim ɗin kuma a kan rayuwar ‘yan mata ne, a kan haka zan yi fim ɗin, za ka ga fastocin fim ɗin na yawo a soshiyal midiya. Aƙalla mata kusan goma ne cikin fim ɗin, ba a maganar maza, amma akwai mazan sai dai ba su da yawa, saboda labarin a kan mace ne; ‘Gidan Zeenat’. 

“Abubuwan da ake tafkawa a ‘Gidan Zeenat’, shi mutane za su saurara su gani in fim ɗin ya fito. Don ko yanzu da mu ke magana ina Legas, na je magana a kan wanda zai yi min dillancin fim ɗin.

“Haka kuma na je na zauna da wasu masu gidajen talbijin don ganin na kai masu fim ɗin. Sannan kuma akwai wani sabon gidan talbijin da za a buɗe nan da Satumba, na zauna da su, mun yi yarjejeniya da su, har an saka hannu zan ba su fim ɗin Turanci guda goma, amma zai zama matan mu da mazan mu Hausawa ne za su kasance a ciki, don su na so su ga ya aikin su ya ke a kan aikin fim ɗin Turanci. Don haka mun gama magana zan yi masu finafinai goma in Allah ya yarda.”

Fostar shirin ‘Gidan Zeenat’

Da mu ka tambaye ta abin da za ta ce game da mulkin MOPPAN na Jihar Kaduna a yanzu, sai ta amsa da cewa, “Ni yanzu babu abin da zan ce a kan mulkin MOPPAN na yanzu, saboda ni ba shiga cikin su na ke yi ba. Kwanaki dai sun yi ‘workshop’ da ‘National Film and Video Censors Board’, sun gayyace ni, amma Allah bai ba ni ikon zuwa ba.

“Amma kuma a taron ‘National Exco’ da aka yi a Kano, mun haɗu da shi ciyaman na MOPPAN reshen Jihar Kaduna.

“Ni yanzu na zarce wa Kaduna, tunda ina ‘national’ ne. To wanda ke sama kuma ya za a yi ta waiwayi jiha? Yanzu jiha ba hurumi na ba ne, akwai wanda hurumin su ne jiha, to su ne mu ka koma gefe, mu ka zura wa ido mu ga me za su yi mana.

“Ga masu zaɓe, waɗanda su ka zaɓe mu baki ɗaya, sun san wacece Lamaj. Kuma sun san su waye su ke mulki yanzu. Lokacin da ni na ke shugabantar Kaduna, sun san me da me na yi a zamani na. Tunda na yi finafinai biyar zuwa shida. Alhamdu lillahi, yanzu ga zamani, Allah ya ba Kaduna zamani daidai da abin da ta ke so. Abin da Kaduna su ka zaɓa, shi Allah ya ba su. Ni kuma da su ka ce ni mace ce bai kamata a ce mace ta mulke su ba, alhamdu lillahi, kowa mace ta haife shi, kuma namiji ba zai iya auren namiji ɗan’uwan sa ba, dole sai dai mace zai aura. Haka kuma namiji bai da zaɓi in Allah ya ba shi zuri’a ya ce namiji ya ke so. 

“Don haka mace ta na gaba da komai, tunda Allah ma sai da ya ambaci mahaifiya sau uku, sannan ya ambaci mahaifi. 

“Yanzu ni babu abin da zan ce wa industiri sai godiya, saboda ni yanzu gaba na yi.  Mutanen da na ke mu’amala da su yanzu lokacin da na ke ‘chairperson’ na Kaduna State MOPPAN, wallahi ban san su ba, bari na jiha ya ƙara buɗe min ido. Tunda yanzu za ka ga an gayyace ni ‘film festival’, an saka ni a kwamiti na ‘film festival’, ka ko san cewa ai cigaba ne. 

“Duk wanda ya riga ya yi gaba, ba ya waiwayar baya. Saboda ko yanzu aka ce Lamaj dawo ga Kaduna an ba ki, ba sai kin sayi fom ba, zan roƙe su in ce su yi haƙuri su ba waɗanda su ke so. 

“Yanzu fim ɗin da zan yi, akwai ‘yar Abuja, akwai ‘yar Bauchi, akwai ‘yan Kaduna, akwai ‘yan Kano, haka na cakuɗa su. Kuma tunda fim ne mai dogon zango, za a riƙa buɗawa ana ɗauko na wasu jihohin ana sakawa a ciki.

“A matsayi na na ‘national exco’, babu abin da zan ce, godiya na ke yi wa Allah da sakayyar da ya yi min da Kaduna su ka ce ba su yi na, kuma ‘national’ su ka ce su na yi na, don haka me zan cewa MOPPAN,  sai hamdala.

“Ina godiya ga kowa da kowa, ina kuma yi maka fatan alkhairi Abba.”

Loading

Previous Post

Mawaƙi Zayyanu Extra da Nana Firdausi sun samu ɗan fari

Next Post

Ba a duba cancanta a Kannywood – Habibu Yaro Haruna

Related Posts

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 
Labarai

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

June 29, 2025
Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta
Labarai

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta

June 23, 2025
Next Post
Habibu Yaro Haruna

Ba a duba cancanta a Kannywood - Habibu Yaro Haruna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!