TUN bayan fitar labarin zargin damfarar da jaruma Halisa Muhammad ta ce wani mai suna Bashir ya yi mata kan tafiyar ta zuwa ƙasar Saudi Arebiya neman magani a kwanan baya, jama’a suka zuba ido su ga irin matakin da hukumomi da sauran al’umma za su bi domin a ƙwato mata haƙƙin ta.
Halin da baiwar Allahn ta tsinci kan ta a ciki ya taɓa zuciyar mutane, ganin tsawon lokacin da ta shafe cikin rashin lafiya da kuma neman taimakon yadda za ta ceto rayuwar ta. A daidai lokacin da damar ta samu ta tafiya neman lafiyar, sai kuma ta haɗu da wannan jarabawa ta damfarar da ta ce an yi mata.
A yanzu da yake an ɗauki lokaci, mun nemi jin ta bakin Halisa don jin inda aka kwana. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
FIM: A kwanakin baya kin shirya tafiya zuwa Saudiyya don neman lafiyar cutar kansar mama da kike fama da ita, sai kuma kika ce wani ya damfare ki kuɗin tafiyar. Za mu so ki yi mana bayanin yadda al’amarin ya faru.
HALISA MUHAMMAD: To, assalamu alaikum. Suna na Halisa Muhammad, wadda nake fama da ciwon kansar mama. Mutane da dama, musamman ‘yan Kannywood, suka fara ɗaukar nauyin ciwon suka yi iya gwargwadon iyawar su. Saboda ciwo ne mai wahalar sha’ani, har aka zo ga taimakon mutanen da ba ‘yan fim ba, suka ba ni gudunmawar su sosai. Har aka saka a soshiyal midiya, wanda Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ɗauki nauyin allurai na, kuma ya ba mu kuɗi naira miliyan 15 domin mu sayi allurai da magani.
Sai wani bawan Allah mai suna Bashir Abdullahi, wanda ya yi iƙirarin shi mai yin hanya zuwa tafiye-tafiye ne, ya ce mana akwai wani asibiti a ƙasar Saudi Arebiya a Madina da ya kai mahaifiyar sa, don haka zai taimaka ya kai ni mu ƙarasa waɗannan magunguna. Abin da yake buƙata kawai daga gare mu shi ne kuɗin biza da na tikiti.
Daga nan muka fara wannan mu’amala da shi tun cikin azumi, har aka zo tafiyar aikin Hajji, kullum yana faɗar magana daban, yau ya ce a ba shi N500,000, gobe ya ce miliyan ɗaya, har ya kai ya karɓi miliyan bakwai da ɗari biyar.
Daga nan ya saka mana ranar tafiya, ya aiko mana da biza da tikiti. Muka je filin jirgi don tafiya, sai aka ce mun makara wajen tafiya. Don haka muka kira shi muka faɗa masa, ya kuma riƙa faɗa kan abin da aka yi mana.
A haka yake canza tikiti. Sai da muka je filin jirgi sau bakwai zuwa takwas, har ma akwai ranar da muka je sau uku. Amma da muka ga abin ya ci tura, sai muka tambayi mahukuntan filin jirgi yadda lamarin yake.
Shi manajan tafiye-tafiye na wajen da muka same shi muka sanar da shi halin da muke ciki, sai ya buɗe kwamfuta ya duba tikitin mu. Nan ya tabbatar mana cewa ba a saye shi ba ma a hukumance. Don ba a taɓa ma sayen sa ba, kamar yadda kwamfuta ta nuna.
Sai muka ce a gwada bizan ma. Da aka saka, ita ma ta ƙi ɗauka. Nan muka gane mun faɗa hannun ɗan damfara, ya ba mu tikiti da biza na bogi.
Muka dawo muka same shi muka sanar da shi, kuma ya amsa haka ne, amma mu jira zai biya mu kuɗin mu.
To, shiru-shiru sati ɗaya, kwana goma. Saboda sakamakon ciwo, sai muka koma asibiti mu ci gaba da magani. Sai muka je muka samu iyayen sa muka sanar da su. Suka ce za su taimaka, za su yi masa magana. Amma duk aka yi abu bai yi ba.
Sai muka kai ƙara Bompai wajen hukumar ‘yan sanda, sannan muka je DSS. Nan ma abin ya ci tura. Har na je na yi rubutu a soshiyal midiya, duk dai shiru.
Sai na yi sa’a ta hanyar soshiyal midiya, na samu wani babban lauya, Barista Ɗantani, ya shigo ya ɗauke ni muka je DSS muka shigar da ƙara. Kuma a ranar ma aka je gidan sa domin a kama shi, babu shi, babu dalilin sa. Har yanzu a wannan magana muke.
Abin dai da na sani an samu cigaba. Bisa wannan ƙoƙari da Barista Ɗantani yake yi, ya turo dubu ɗari biyar, ya ce zai bayar. Daga baya ya kuma bada wata ɗari biyar. Aka ci gaba da bibiyar sa, ya kuma bayar da miliyan ɗaya. A yanzu abin da ya bayar miliyan biyu kenan, saura miliyan biyar da ɗari biyar. Kuma yanzu babu amo, ba labari.
FIM: Su a ɓangaren hukumomi, wanne matakai suke ci gaba da ɗauka na ganin ya dawo da kuɗin? Ko an kai ga kama shi?
HALISA: To, har yanzu dai ana ta ƙoƙari a kama shi, ko kuma ya zo ya kawo kan sa. Ana samun sa a waya, amma idan an je wajen da yake ba a samun sa.
FIM: To, ita maganar har yanzu ba ta kai ga kotu ba kenan?
HALISA: A’a, ba ta kai ga kotu ba, saboda ai ba a same shi ba da har za a kai shi kotu.
FIM: A yanzu da ake cikin wannan yanayin, wanne hali kike ciki dangane da jikin ki?
HALISA: E to, da yake matakai ne guda biyar zuwa shida. Alhamdu lillah, mun yi huɗu, saura guda biyu. Waɗannan kuɗaden ne za mu yi amfani da su wajen sayen magunguna da ake ɗora mutum a kan su na kusan shekaru huɗu ko biyar idan an yi gwaje-gwaje.
Shi gwajin da za mu je, ba a yin sa a nan Kano ko Abuja. A Legas ake yin sa. Kuma idan za ka tafi ana neman aƙalla ka riƙe miliyan hudu. Sannan idan an yi gwajin ka kawo sakamakon, daga nan sai a ɗora ka a kan magunguna. Wannan shi ne abin da ya rage mani, amma sai na samu kai na a wannan jarabawa ta damfara.
FIM: Wato kenan dai har yanzu kina neman addu’a da taimakon mutane kan halin da kike ciki?
HALISA: Gaskiya ne. Halin da nake ciki kenan, na neman taimako domin na samu na je wannan gwaje-gwajen, ko dai a taimaka a kwato mani haƙƙi na daga wannan bawan Allah, ko kuma a samu waɗanda za su taimaka mani da kuɗin da zan ci gaba da kula da lafiya ta.
FIM: A can baya an yi gwaje-gwaje. Shin sun lalace ne ko wata matsala aka samu?
HALISA: Ai da ma matakan guda shida ne, kamar yadda na faɗa maka. Mun yi guda huɗu. Tun da farko an kwanta a asibiti, an yi kemo (chemotherapy), sannan aka yi tiyata. Aka kuma yi wani kemo. Aka yi gwaje-gwaje, aka fara allura, wadda muka yi kashi shida. A lokacin hankali ya tashi saboda allurar tana yankewa, ba mu da kuɗin ta.
Sai Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, shi ne ya bayar da kuɗin allurar, muka saye su gaba ɗaya. Da muka gama sai wannan gwaje-gwaje, wanda idan a ƙasashen da suka ci gaba ne, ana yin sa kyauta, musamman a ƙasar Saudi Arebiya, za ka je ka yi ziyara, ka yi addu’a, ka yi gwajin, sannan ka dawo gida da sakamakon, a ɗora ka a kan magani. Ka ji yadda tsarin yake.
FIM: Wanne kira za ki yi ga al’umma dangane da halin da kike ciki?
HALISA: To, kiran da zan yi ga al’umma, a matsayi na na shugabar ƙungiyar wayar da kai a kan ciwon kansar mama, shi ne mata da maza su kula da lafiyar su, musamman wannan rashin lafiya ta cutar kansar mama. Domin ciwo ne da yake yaɗuwa kamar wutar daji.
Sannan gwamnatocin mu idan mun fito neman taimako ga masu wannan ciwon, don Allah a taimaka mana. Ina yi wa kowa fatan alheri.
FIM: Madalla, mun gode.
HALISA: To, ni ma na gode sosai.
![]()







