MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana aiwatar da wasu tsare-tsare da sauye-sauye da aka tsara domin magance kurakuran da aka yi a baya da kuma sanya Nijeriya ta zama wata babbar ƙasa mai ƙarfin tattalin arziki nan gaba kaɗan.
Idris ya bayyana haka ne a cikin jawabin sa a Abuja ranar Alhamis a wani taron duniya da aka yi na manema labarai domin bayyana abubuwan da aka shirya domin bikin cikar Nijeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai.
Ya ce: “A ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Tinubu, mun ɓullo da tsare-tsare da sauye-sauye da nufin gyara kurakuran da aka yi a baya da kuma mayar da Nijeriya matsayin mai ƙarfin tattalin arziki nan gaba kaɗan.
“Duk da halin da tattalin arzikin duniya yake ciki da kuma raɗaɗin da ke tare da wasu sauye-sauyen, Shugaban Ƙasa ya ci gaba da mai da hankali kan ƙoƙarin sa na farfaɗo da tattalin arzikin mu da kuma maido da ƙasar kan turbar wadata da cigaba mai ɗorewa.”
Ministan ya bayyana cewa a wani gagarumin yunƙuri na kawo sauyi ga cigaban zamantakewa da tattalin arzikin karkara a Nijeriya, Shugaban Tinubu ya yi nasarar nema tare da samun gagarumin hukuncin Kotun Ƙoli da ya ba ƙananan hukumomi cin gashin kai.

Idris ya ce wannan shawara guda ɗaya ta tabbatar da cewa zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi a yanzu suna da ikon sarrafa kasafin kuɗi kai-tsaye, wanda zai inganta tsarin mulki da cigaban ƙananan hukumomi.
“Bugu da ƙari, ana aiki sosai wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki, daidaita tsarin musayar kuɗaɗen waje, sake fasalin tsarin haraji don inganta shi, da rage nauyi a kan ‘yan Nijeriya, sake daidaita ɓangaren man fetur da iskar gas ɗin mu don jawo sababbin jari, da kuma ba da fifiko wajen rarrabawa da faɗaɗa kuɗaɗen shiga na gwamnati.”
Ministan ya ƙara da cewa sannu a hankali Shugaban Ƙasar yana jagorantar Nijeriya ta shiga wani yanayi na canjin makamashi na musamman ta hanyar ƙaddamar da shirin shugaban ƙasa na matsar da ƙasar daga amfani da man fetur zuwa iskar iskar gas (CNG) a matsayin makamashin ababen hawa da injina.

Ya amince da cewa ci gaba da fitar da iskar gas da kayayyakin da ke da alaƙa da su yana rage tsadar sufuri ga ‘yan Nijeriya da kashi 60 cikin 100, da samar da ayyukan yi, da kuma jawo dubun-dubatar daloli a cikin gida da waje.
“Ta hanyoyi da yawa Shugaban Ƙasa ya mayar da hankali wajen sanya ƙarin kuɗaɗe a aljihun al’ummar Nijeriya, da samar da hanyoyin samun cigaba mai ɗorewa,” inji shi.
Ministan, wanda ya ce bikin cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai lokaci ne na tunani, da biki, da sabunta fata, ya jaddada cewa ya zuwa yanzu Nijeriya ta nuna juriya, ƙarfi, iyawa, da kuma jajircewa wajen fuskantar ƙalubale masu tarin yawa.
Idris ya ce tun bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1960, Nijeriya ta samu cigaba daga ƙasa mai fata ta zama ƙasa mai ƙarfin faɗa a ji a nahiyar Afrika kuma mai martaba a duniya kuma duk da ɗimbin ƙalubalen da ake fuskanta, ƙasar na ƙara samun ƙarfi ta hanyar hangen nesa mara kaushi na ƙasa mai haɗin kai da wadata.

Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen yaba wa ‘yan Nijeriya kan haƙuri da juriya da suka nuna a wannan lokaci mai matuƙar wahala a cikin sauyin tattalin arzikin ƙasar, inda ya ce tafiyar ta yi tsauri amma akwai haske a ƙarshe.
Ya ce a kwanan nan ne Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta amince da Yarjejeniyar Ɗa’a ta Ƙasa, wanda yanzu Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai za ta fara aiwatarwa daidai da ƙudirin Shugaban Ƙasa na farfaɗo da ɗabi’u, ɗa’a, da kuma al’adu.
“Yarjejeniyar za ta ƙarfafa imanin cewa abubuwan da suka haɗa kawunan mu -kishin ƙasar mu, wajibcin mu ga ƙasar mu, da wajibcin ta a gare mu – za su kasance masu ƙarfi da zurfi fiye da abin da ke son raba mu,” inji shi.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, shi ne ya ƙaddamar da shirye-shiryen bikin cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai, wanda ya samu halartar Ministan Kasafi da Tsare-tsare na Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu; Ministan Kuɗi da Gudanarwa na Tattalin Arziki, Mista Wale Edun; Ministan Ayyuka, Sanata Dave Umahi; Ministan Albarkatun Ruwa, Farfesa Joseph Utsev; Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman; Ministan Yawon Buɗe Ido, Lola Ade-John; Ministan Ayyuka na Musamman da Harkokin Gwamnati, Zaphaniah Jisalo, da sauran manyan jami’an gwamnati da mataimakan Shugaban Ƙasa.