GWAMNATIN Jihar Kano ta yi kira ga jama’a da su taimaka mata ta kama fitattun mawaƙan nan biyu da aka fi sani da Safara’u da Mr 442 domin a hukunta su saboda “waƙoƙin baɗala” da su ke yi a soshiyal midiya.
A shelar da ta yi, gwamnatin ta buƙaci jama’a da su taya ta wajen yi wa matasan biyu kwanton ɓauna a duk lokacin da aka gan su a cikin jihar domin a cafke su a kai su kotu.
Sunan Safara’u na sosai dai Safiya Yusuf, yayin da shi kuma Mr 442 sunan sa Mubarak Abdulkarim.
Safara’u ta yi fice ne a shirin diramar ‘Kwana Casa’in’ na tashar talbijin ta Arewa24, kuma sunan ta ya ƙara yaɗuwa ne bayan an cire ta daga shirin a cikin shekarar 2020 bayan ɓullar wani bidiyon tsiraici da ta yi.
Shi kuma 442, wanda ɗan Zariya ne, ya fara yin fice ne bayan waƙar zambon da ya yi wa jaruma Maryam Booth kan wani bidiyon ta na tsiraici da kuma tsare shi da ta sa aka ɗan yi.
Safara’u da 442 sun shiga bakin duniya tun lokacin da su ka haɗe waje guda su na yin guntayen bidiyo waɗanda su ke wallafawa a Instagram, masu ɗauke da kalamai da rawar batsa.
Shugaban Hukumar Tace Finafinai Da Ɗab’i ta jihar, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallahu), ya ce abin da su ke yi ya saɓa wa dokar hukumar sa, don haka tilas ne a gurfanar da su a gaban alƙali domin a hora su.
Afakallahu ya bayyana haka ne a lokacin da ya tattauna da mujallar Fim a ofishin sa a jiya Asabar.

Ya ce: “Wannan umarnin ba tun yanzu ba ne mu ka baza komar mu ta farautar waɗannan mutane, sai dai yanzu ne da labarin ya fita ake ganin kamar yanzu ne. Amma mun daɗe da sanar da neman su, kuma mun yi hakan ne a sakamakon waƙoƙin batsa da suke saki na ɓata tarbiyyar mutane.
“Ba wai ita hukumar ta na kallon su ne a matsayin mawaƙa ba, sai don abin da su ke yi na batsa da ɓata tarbiyya. Kuma duk abin da za ka yi na neman abinci, idan har akwai saɓa wa Allah a cikin sa, sai dai ka ci guba, ba dai ka ci abinci ba.
“Kuma idan ka kalla, a yanzu ba sa ma ƙasar, daga can su ke yi su ke turawa a soshiyal midiya. Kuma babu wani uba ko uwa da zai bar ɗan sa ya ci gaba da irin waɗannan abubuwa na ɓarna da sunan ya na tura saƙo.
“Da man saƙo kala biyu ne: akwai na ɓarna, akwai na alkhairi. To, su wannan da su ke turawa na ɓarna ne. Ana yin waƙoƙin ɓarna ana yin batsa waɗanda ba su dace ba.
“Ita kuma hukumar an samar da ita ne saboda yaƙi da irin wannan. Don haka duk wanda ya taka dokar wannan hukumar, mu na mai tabbatar masa da cewa ya haɗiyi taɓarya!
“Don haka jama’a su taya mu wajen kawar da irin waɗannan abubuwan, don aikin nan ba na hukuma ita kaɗai ba ne, na jama’a ne baki ɗaya. Saboda haka babu wanda zai zo garin nan don ya samu ɗaukaka ta shaiɗanci mu bari ya lalata mana tarbiyyar mu ta addini.
“Don haka lallai mu na neman su, kuma mun ba da sanarwar a dukkan gidajen da ake yin wasanni da gidajen da ake yin bukukawa duk irin waɗannan waƙoƙin ba za a saka su ba.”
Shugaban ya ƙara da cewa, “Ita hukuma abin da ya bayyana shi ta ke iya karewa, don ba za ta shiga gidajen mutane ta ga me su ke kallo su da iyalan su ba. Mu abin da ya bayyana shi mu ke hukunci a kan sa, don haka mu ka ce ba za a saka waƙoƙin a gidajen wasanni ko wajen taron biki ba, don haka mu ka kira iyaye da magidanta da su hana abubuwan ta ɓangaren su.
“Don haka, mutane su gane ko su waɗannan da su ka yi laifin ba mu su ka yi wa laifi ba, doka su ka taka, don haka duk lokacin da mu ka kama su za mu tattara ne mu kai su ga hukuma. Kotu ce za ta yi masu hukunci. Don haka ba Afakallahu ne zai zauna ya ce ka yi ba daidai ba a yanke maka hukunci. Don haka lallai za mu gurfanar da su ne a gaban kotu, domin sun karya dokar Jihar Kano da kuma rashin girmama mutanen Jihar Kano.
“Kuma gudun da su ka yi, ya nuna hukumar a tsaye ta ke wajen kare dokoki da jama’ar Kano a kan duk wani abu da zai kawo barazana a gare su. Kuma duk wanda ya ke ganin zai karya doka, to ga shi ga wajen. “
Afakallahu ya yi kira ga iyaye da su sa ido kan tarbiyyar ‘ya’yan su domin zamani ya zo na soshiyal midiya inda akwai ƙalubale a gaban su a kan abin da ya shafi wayoyin ‘ya’yan su.
Ya ce: “Duk abin da ka ke ganin ka yi na tarbiyya, cikin ƙaramin lokaci za a rusa shi. Don haka ka sa idanu a kan yaran ka. In dare ya yi, duk wata mace a karɓe wayar ta, saboda wasu abubuwan sai kun kwanta ake yin su.”