JAMILA Muhammad, wadda aka fi sani da suna Jamila Kogi a harkar waƙa, ta na ɗaya daga cikin mawaƙa mata da a yanzu su ke haskawa a Kannywood. Mawaƙiyar ta na da nasibi sosai, domin ta ƙware wurin waƙe manyan ‘yan siyasa, ‘yan ƙwallo, sarakuna, kai har da manyan ‘yan fim. Jamila ba ta daɗe da fara waƙa ba, amma har ta samu ɗaukaka, saboda irin jajircewar ta. Da yawa an shaida cewa Jamila zabiya ce mai ladabi da biyayya, ga girmama na gaba da ita, har da ma na ƙasa da ita. Wakilin mu ya samu zantawa da ita, inda ta yi mana bayanin yadda aka yi ta fara waƙa, da tarihin ta, waƙoƙin da ta yi da sauran su.

FIM: Ki faɗa wa masu karatu cikakken sunan ki da tarihin rayuwar ki a taƙaice.
JAMILA KOGI: Suna na Jamila Muhammad Kogi, wadda aka fi sani da Jamila Kogi. An haife ni a Jihar Kogi, na yi karatu na daga firamare zuwa sakandare a Jihar Neja. Sannan yi karatun koyon aikin malanta a FCE Zaria. A halin yanzu ma ina tunanin ci gaba da karatu na. Da ma makaranta ya kawo ni Kaduna ba harkar industiri ba. Kuma ko da na zo industiri, fim na zo yi, amma da na roƙi Allah Ya zaɓa min abin da ya fi alheri, sai Ya zaɓa min waƙa.
FIM: Ke wace yare ce?
JAMILA: Ibiran Koto ce. Ka san akwai Ibiran Koto, akwai na Okene. To, ni ta Koto ce.
FIM: Ki na waƙa da yaren ki?
JAMILA: Ina waƙa da yaren Mama na da na Baba na. Wani lokacin har da Nufanci ina waƙa.
FIM: Yaruka nawa ki ke ji?
JAMILA: A gaskiya ina jin yaruka aƙalla sun fi biyar. A yaren can wuraren mu, ina jin Nufanci, ina jin Kakanda yaren Mama na, ina jin Ibira yaren Baba na, sannan ina ɗan jin yaren Ibiran Okene, tunda kusan yaren ɗaya ne. Ina jin Gana-Gana, ina jin Dibo, ina jin yaruka da dama a wuraren mu. Ina jin Hausa, kuma ina jin Turanci.
FIM: Ya aka yi ki ka fara waƙa?
JAMILA: Na fara waƙa ne ta dalilin ina son fim. Akwai yanayin da na bi wasu su ka faɗa min wasu abubuwa da ƙa’idojin su, ni kuma na ga ba zan iya bi ba. Kawai sai na ga gara in fara waƙa. Ana haka sai na samu DJ Barde na ce masa ina so in yi waƙa, a lokacin ban ma fara karatun ba. Na zo tantancewa, sai ya ce min a gwada murya ta. Da mu ka je aka gwada sai suka ji muryar ta yi daɗi, sai su ka ce mu yi waƙar gaba ɗaya kawai. Sai mu ka ɗora wata waƙa ‘A Je Makaranta’ ni da Ahmad A. Lansi. Idan ka ji waƙar ba za ka taɓa cewa ‘yar koyo ba ce! Don ko ni na yi mamaki da na ji yanayin yadda na yi waƙar. Amma ni a wuri na ba wani abu ba ne, tunda kamar gado ne, ban yi mamaki ba. Saboda baban Mama na da ɗan’uwan sa sun yi waƙa da da kiɗa tun a zamanin da. Yanzu haka akwai kawu na wanda ya na waƙar yaren mu. Domin superstar ne a Kogi; duk inda ka je ka ce Usman Kyo-kyo, ba wanda bai san shi ba.
FIM: Me ki ka karanta a FCE?
JAMILA: Islamic Studies da Social Studies.
FIM: Bayan waƙa, ki na aikin karatun da ki ka yi?
JAMILA: E, an yi min maganar ayyuka. Ni ce dai na nuna masu ba ni da ra’ayi. Na ce masu idan na tashi aure zan aje waƙa zan nemi aiki. Don ni ina ganin NCE bai kai min matakin da zan nemi aiki da shi ba. Ni so in ci gaba da digiri har ma in wuce. In kuma na canza ra’ayi kuma shi kenan.
FIM: Kin fuskanci matsaloli a harkar waƙa?
JAMILA: Gaskiya na fuskanci matsaloli da dama. Farko da na fara an so a zuga iyaye na su hana ni. Duk yadda na so na fahimtar da su waƙar da na ke yi kamar gado ne, ba su so su fahimta ba da farko. Sai na haƙura da waƙar na ci gaba da karatu. A hankali na fahimtar da su, na ce masu, “Zaman banza ba zai yiwu ba. Tunda ina karatu zan so na haɗa da wani abu, ba kuma wai don kun gaza ba, don kawai kada in zauna haka nan babu abin da na ke yi.” A lokacin da na zo na jajirce ina waƙa, wasu sun ce ba zan iya karatun ba, zan daina in koma waƙa. Har na gama karatu na ban taƙa samun carry-over ba! Kawai na ce a raina ne abin da mutum ya wa kan shi zai yi, zai yi.
FIM: A yanzu da ki ke tsakiyar cin zamanin ki a harkar waƙa, za ki iya aje waƙa ki kama wata sana’ar?
JAMILA: A gaskiya in dai ba aure na yi ba, ba na tunanin zan iya aje harkar waƙa. Amma idan na yi aure zan iya aje waƙa, domin in yi biyayya ga duk wani abu da miji na ya ce ya na so. Daga nan zan iya ci gaba da karatu na ko kuma in ci gaba da aiki.
FIM: Ki faɗa wa masu karatu wasu daga cikin waƙoƙin ki.
JAMILA: Akwai ‘Nijeriya’, ‘Aure Ko Karatu’, ‘So’, Sarki Ali Nuhu’, ‘Sarkin Ƙwallo Ahmad Musa’ da sauran su. Ina waƙar yabo, jinjina, aure, suna, murnar zagayowar ranar haihuwa, da dai sauran su. Kuma ina waƙa da kowane irin yare in dai ina ji. In kuma ba na ji aka buƙaci in yi na kan je in samu masu yaren su koya min. Babu yaren da ba zan iya waƙa da shi ba.
FIM: Aƙalla zuwa yanzu waƙoƙin ki za su kai nawa?
JAMILA: A gaskiya ban san yawan waƙoƙi na ba, don gaskiya sun fi ɗari.
FIM: Amma ya ki ke ganin yanayin harkar waƙa a Kaduna?
JAMILA: Gaskiya maza su na ƙoƙari a Kaduna. Mata ne dai an bar mu a baya, domin mu na ganin kamar ba za mu iya ba. Amma kuma mu ne mu ke saka kasala a cikin lamarin namu. In dai har namiji zai iya rubuta waƙa, ki saka a ran ki ke ma za ki iya. In har namiji zai iya ɗaukar nauyin kan sa ya yi bidiyon waƙoƙin sa, ke ma za ki iya. In har namiji zai yi suna a waƙa, ki sa a ran ki ke ma za ki iya. Ba sai ka yi iskanci za ka yi suna ba, ba sai wani ya taimake ka za ka yi suna ba. In dai ka nemi taimakon Allah, za ka yi suna. In Allah bai amince ba, ba za ka yi suna ba. Amma abin da na yarda da shi, jajircewa na kai ka ga matakin yin suna. Za ka ga mace a Kaduna ba ta da waƙar kan ta da yawan su ya kai goma, sai kawai a kira ta ta je amshi. In dai har Umar M. Shariff zai yi suna, ƙaddara wa ran ki ke ma za ki yi suna. In har Nura M. Inuwa zai yi suna, ke ma za ki iya. In har Umar zai iya ɗora waƙa da kan shi, ke ma za ki iya. Biyayya ga na gaba shi zai kai ki ga nasara. Za ka ga mace an kira ta hira gidan rediyo, ta ce ba za ta yi ba, saboda ba ta san muhimmancin sa ba.
FIM: Amma ana cewa matan Kaduna ba su fita wasu garuruwa domin yin waƙa. Menene gaskiyar wannan magana?
JAMILA: A gani na ba a biya su ba ne kuɗin ya kai ba. In har za a biya su kuɗin da zai ishe su, me zai hana su zuwa? Misali, mutum ya gayyace ka garin da ba ka sani ba, ya ce maka dubu goma, sai ka yi tunanin nawa za ka kama otal, ga abinci da sauran buƙatu. In zan je maka aiki dole ka ɗauki nauyi na.
FIM: Menene bambancin mawaƙa ‘yan Kano da ‘yan Kaduna?
JAMILA: Magana ta gaskiya Kano sun ci gaba fiye da Kaduna, ba don komai ba sai don su na taimaka wa kan su, kuma su na taimaka wa wanda su ka ga ya na da ƙoƙarin yi. Misali, Ali Nuhu idan ya ga mutum ya na ƙoƙari, zai ɗauko shi ya nuna masa irin ƙoƙarin da ya ke yi, sannan ya ƙara masa ƙarfin gwiwa. A Kaduna ko babu irin wannan. Zai yi wuya ka yi abu wani babban ka ma ya ce maka ka yi ƙoƙari. Maimakon su ƙarfafa maka gwiwa, sai dai su kalla su wuce. Kuma ‘yan Kano ba su raina samu. Idan zai fita ya samu ɗari biyar, zai sarrafa ta ya saka a asusun bankin sa. Amma a Kaduna mutum sai ya samu dubu goma, sai ya kashe su kafin ya samu wasu.
FIM: Kin taɓa tunanin fitar da kundin waƙoƙin ki?
JAMILA: Na yi na yaren mu. Amma ban saki ba, don ban san yadda zan yi in saki waƙoƙi na ba a kasuwa. Ban san wanda zan samu ba waƙoƙi na su bazu a gari. Manyan mu ya kamata in ka na ƙoƙari su ce mana ga yadda za a yi kaza da kaza. So, ni ban san inda zan saida waƙoƙi na ba. Don haka duk mai neman waƙoƙi na sai dai in ce masa ya je shafi na na YouTube ya sauke a wayar sa.
FIM: Ba ki ganin yawan waƙoƙi barkatai da ki ke yi zai gundiri mutane?
JAMILA: Gaskiya ba zai gundiri mutane ba. Hasali ma sai dai ya taimake ni tallata ayyuka na. Saboda ba iri ɗaya na ke yi ba. Mutane da yawa sun kira ni, sun ce babu mace mai yawan bidiyo a Kaduna kama na. A Kano ma yadda su ka ce, sai an tantance kafin a samu kama ta. Gaskiya ina yawan bidiyo amma ban san yadda zan kai kasuwa ba. Ni na ke yin abu na da kai na, ba wani ya ke yi min ba. Ba ni da mataimaki sai Allah, sai kuma wasu daga cikin masu gida. A industiri kowa oga na ne. Kuma a waƙa kowa nawa ne, idan ka sa ni aiki zan yi maka. Babu ruwa na da jam’iyya, babu ruwa na da faɗan ka da wani. Ni kuɗi kawai na ke nema!
FIM: A kwanakin baya kin yi wa wasu jarumai waƙa. Da farko kin yi wa jarumi Adam A. Zango, kwatsam kuma sai ga shi kin yi wa Sarki Ali Nuhu, kuma akwai rashin jituwa a tsakanin su. Ba ki samu matsala da ɗaya daga cikin su ba dalilin waɗannan waƙoƙin?
JAMILA: E to, Adamu Zango dai oga na ne. Shi ma Ali Nuhu oga na ne. Ba ta ko’ina ba saboda sun girme ni a wannan masana’antar. Gani na yi don na yi wa Adamu da Ali Nuhu waƙa ba wani abu ba ne. Saboda sana’a ta ce. Babu ruwa na da faɗan da su ke yi. Adamu na yi masa waƙa biyu tun ina NCE, na buga kwafi sittin na kai masa, ya karɓa ya nuna min ya ji daɗi ya yi min godiya da sauran su. Na kuma yi masa waƙar auren da ya yi daga bayan nan guda biyu. Na yi wa Yallaɓai (Ali) waƙa. Ban taɓa yi masa ba, wannan ita ce ta farko da na yi masa har na yi bidiyo. Na yi na’am da yadda ya nuna min jin daɗin sa da kuma yadda ya karɓe ni ya kuma ja ni a jiki ya nuna godiyar sa sosai. Dukkan su sun nuna min jin daɗin su. Amma karɓuwar abin da bambanci. Domin har yaran gidan Yallaɓai da kowa na shi sun karɓe ni. Shi ma Adamu ban ce bai gode min ba, ya gode min.
FIM: Amma kuma an ce shi Adamu ya yi ƙorafi a kan waƙar da ki ka yi wa Ali. Mecece gaskiyar maganar?
JAMILA: E, Adamu ya yi min magana. Yaran sa ne su ka fara magana, su ka ce min, “Jamila, kin canza gida ne?” Na ce masu, “Ni ban canza gida ba, sana’a ta na ke yi. Ba ni da hanyar da ke kawo min kuɗi face waƙa. Don na yi wa Yallaɓai waƙa ba wani abu ba ne. Kuma ni ba da wata manufa na yi waƙar ba. Don haka idan Adamu na faɗa da Yallaɓai, wannan ba zai hana in yi masa waƙa ba.” Akwai wata waƙa da na yi wa Laila da Gabon, sai wasu su ka ce kin yi wa jaruma waƙa kuma kin yi wa su Laila. Sai na ce masu kuɗi na na ke nema, duk wanda ya biya ni zan yi masa waƙa! Babu ruwa na da faɗan da su ke yi. In na haɗu da Adamu zan gaishe shi, in girmama shi. Haka shi ma Yallaɓai. Dukkan wanda ya girmama ka, kai ma ka sani. Hausawa su ka ce ido ba mudu ba, amma ya san kima.
FIM: Kin ƙware wurin yi wa manyan mutane waƙa. Akwai alherai da ki ka samu daga wurin su? Don wasu na ganin kawai ki na yi masu ne ba don ki samu komai ba.
JAMILA: In da ba don in samu wani abu ba ne da yanzu an daina ji na. Har nawa na ke da shi da zan rinƙa zubawa ba su dawowa kuma in ci gaba da kashewa? Ni ma na ji labarin an ce ina bidiyo ba a biya na. Ba fa tsafi na ke yi ba. Ba yankan kai na ke yi ba. Ya za a yi in rinƙa kashe kuɗi ba su dawowa kuma in ci gaba da kashewa? Na yi wa gwamnoni da matan su waƙa, na yi wa manya-manyan ƙasar nan. Ka na ganin in ba a biya na zan ci gaba? Ai wannan ba zai yiwu ba ma.
FIM: Kin taɓa aure?
JAMILA: Ban taɓa aure ba. Amma in-sha Allahu aure na cikin ajanda na, domin an ce mutuncin mace ɗakin mijin ta. Ina nan ina addu’a Allah Ya zaɓa min miji na gari.
FIM: Akwai lokacin da ki ka ɗauka na daina waƙa?
JAMILA: Gaskiya babu lokacin da na ɗaukar wai kai na na daina waƙa. Ko gobe aure na ya zo zan yi, don ban rasa wanda zai aure ni ba. Lokaci mu ke jira.
FIM: A lokacin da ki ka shigo industiri, akwai wanda ya gindaya maki wasu sharuɗɗa. Ko za ki iya faɗa mana wasu irin sharuɗɗan da ya gindaya maki?
JAMILA: Lokacin da na zo da niyyar yin fim, wani da na fara haɗuwa da shi ya ce min idan ina so in yi fim sai na yarda duk wanda zai sa ni a fim zai yi iskanci da ni. Ya nuna min ya na so na. Ni kuma sai na ce masa ni ba abin da ya kawo ni ba kenan. Sai ya ce min ko wurin manyan su na je haka za su ce min, don haka ya ce in amince da shi, in cimma abin da na ke so. Ni kuwa na ce masa, “Da na amince da kai da kar na amince da kai, kai ba ka isa ka kai ni matsayin da Allah bai kai ni ba! Ko na amince da kai ko ban amince da kai ba in Allah Ya ce zan zama, sai na zama. Kuma ni na yi maka alƙawari sai na yi suna a industiri.” Ya rantse min ya ce ba zan yi suna ba in dai ban yi iskanci ba. Na ce masa ni da shi mu ƙulla alƙawari, “Ka zauna kuma za ka ga na yi suna da yardar Allah.” Kuma na ce masa, “In don Allah na bar wannan abu, sai na yi suna. Kuma na san ba a taru an zama ɗaya ba, so kawai ka ke yi ka ɓata masu suna.” Ya na faɗa min haka na ga gara na haƙura da fim ɗin, na fara waƙa. A zuciya ta na ce masa da in yi iskanci a sa ni a fim, gara na tafi na shiga karuwanci, na san sana’ar karuwanci na ke yi.
FIM: Amma ki na haɗuwa da shi bayan kin fara waƙa?
JAMILA: Da na fara yin waƙoƙi ina bidiyo, sai ya ke ce min ya idan zan yi aiki ba na neman sa duk da cewa a industiri shi na fara sani ko kuma ai ɓangaren su na fara sani ba na kiran su aiki. Sai na yi dariya na ce masa, “Mu da aka ce ba za mu yi suna ba in dai ba mu yi iskanci ba! Ka san dai abu na Allah da yawa ya ke, kuma na Allah ba su ƙarewa.” A haka dai na kira shi mu ka ci gaba da aiki. Da ma wannan ƙudirin nashi ya na nan a ran shi, kawai sai na fita daga harkar sa na daina kiran shi aiki, na kuma yanke duk wata alaƙa da shi.
FIM: A ƙarshe, me za ki ce wa masoyan ki?
JAMILA: Ina godiya ga masoya na da irin ƙaunar da su ke nuna min. Ina roƙon su da su ci gaba da yi mani addu’a. Allah Ya bar mu tare. Domin su ne ni. Allah Ya saka masu da alheri, Ya kuma biya masu buƙata.
