MATASHIN darakta a Kannywood, Usman Ɗahiru Jauro, wanda aka fi sani da Usman Aphala, ya auri matashiyar jarumar Kannywood, Amina Hassan Wada (Miemie Doziey).
An ɗaura auren su da misalin ƙarfe 1:30 na rana, bayan gama sallar Juma’a, a masallacin Juma’a na Abubakar Mahmud Gumi da ke Titin Nagwamatse, Unguwar Rimi, Kaduna, a kan sadaki N150,000.
‘Yan Kannywood da su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Jamil Nafseen, Sulaiman Sir Zeesu, Abdullahi Abbas, Lawandi Wassh, Abdullahi Abu Uku, Ahmad D-Prince, Ya’u Boza, Albasheer Yarima, A.A. Rasheed Kabala, Abubakar Ɗanjummai CV, Ɗanladiyo Mai Atamfa, Umar M.B., da Aminu Saira Kaduna.
Sauran su ne Halliru Magyazo, Muhammad Showman, Ibrahim Mazaje, Sulaiman Justice, Aliyu Haidar, Aminu Haske, Hamisu Ba Wasa, Yahaya Mai Ganga, Nafi’u Bigi, Mubarak Coge, Ibrahim Mai Gala, Yusuf Dogo, Jaman Mai Kyamara, Abubakar Ɗan Shuwa da Sadiq Superstar.


An yi walima a ofishin Lawandi Wassh da ke Amal Complex, Mogadishu.
Kafin ɗaurin auren, a ranar Laraba aka yi wasan ƙwallon ƙafa da ranar ‘yan wasa a Police College.

Jiya Alhamis kuma aka yi Ranar Ƙauyawa a gidan su amaryar da ke Accra Road, Unguwar Rimi.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.