DARAKTA a masana’antar finafinan ta Kannywood, Hassan Giggs, tare da tsohuwar jaruma Muhibbat Abdussalam sun cika shekara 16 da aure a yau.
A yau ma’auratan su ka wallafa hotuna a soshiyal midiya inda suka nuna godiyar su ga Allah da ya wo su a wannan lokaci su na zaman aure tare da samun ƙaruwar arzikin ‘ƴa’ya mata uku, dukkanin su mata.
A lokacin da ya ke yin hamdala kan ganin wannan rana, Giggs ya ce: “Allah mu na ƙara gode maka bisa ni’imar ka. Yau mu ka cika 16 years da auren mu.
“Allah ba iyawar mu ba ne. Mu na ƙara miƙa godiya gare Ka.
“Alhamdu lillah. Alhamdu lillah. Alhamdu lillah.”

Mujallar Fim ta ruwaito cewa sun rayu tsawon waɗannan shekaru ba tare da yaji ba balle saki.
Wannan wani gagarumin abin alfahari ne a gare su da masoyan su da ma dukkan mai yi wa masana’antar Kannywood fatan alheri.
Allah ya ƙara masu aminci da zaman lafiya cikin so da ƙaunar juna mai ɗorewa, amin.