WASU manyan furodusoshi uku a Kannywood, Maje El-Hajeej Hotoro, Mustapha Ahmad (Alhaji Sheshe) da TY Shaban sun bayyana ra’ayoyi mabambanta dangane da dokar nan da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta bayyana wadda ta haramta shirya fim kan ayyukan ta’asa, musamman kidinafin, shaye-shayen muggan ƙwayoyi da kuma ƙwacen waya.
Mujallar Fim ta wallafa hirar da shugaban hukumar, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), ya yi da ita a ranar Talata da ta gabata inda ya ce sun ɗauki wannan matakin ne domin kare mutunci da al’adar mutanen Kano.
Maje El-Hajej Hotoro, marubuci kuma mai shirya finafinai a Kannywood, ya ce shi ya kalli dokar ne ta fuska biyu inda a gefe guda ya goyi bayan gwamnati, ta wani ɓangaren kuma ya nuna aibun dokar.
El-Hajeej ya ce, “Idan bincike aka yi ƙwaƙƙwara da ya nuna cewa yadda mu ke yin finafinan ya na ɓata tarbiyyar yara ko kuma ya gyara, to in hakan aka yi wannan abin ya nuna wannan abu da aka yi daidai ne, saboda mu ma burin mu shi ne mu ga cewa an gyara domin a cikin wannan al’ummar mu ke rayuwa; idan yau ta zo mu na yin wani abu da ya ke ɓata su, mu ma wata ran zai shafe mu wanda mu san ƙarshen ta ba.
“Ba mamaki hankalin mu bai nuna mana ba; mu na yi da kyakkyawar niyya mu na nuna illolin abin, to amma wanda ya nuna illa ya na dawowa ya taɓa rayuwar mu da ‘yan’uwan mu, ka ga ba za mu so ba.”
Da ya ke bayyana illar dokar kuma, sai ya ce, “Shi kuma adabi wannan duk abubuwan da ake nunawa ya na faruwa, ba wanda ba a yi. Idan aka zo aka ce ba za a yi fim ba, ka ga kenan kamar an tsuke mana basira da fasaha ta aikawa da saƙo.
“Ni yanzu ina da labari guda wanda ya ta’allaƙa a kan garkuwa da mutane ne, to amma saƙon fim ɗin ba garkuwa da mutanen ba ne, a’a, akwai saƙwanni kan me ya ke janyowa mutane su zama masu garkuwa da mutane, shi ne saƙon. Amma yanzu idan gwamnati ta ce ba zan yi ba, ya zan yi? Dole na haƙura.”
Shi kuwa furodusa Mustapha Ahmad (Alhaji Sheshe), ya goyi bayan dokar ne, inda ya ce ta zo a daidai lokacin da ya dace sakamakon yanayin da ƙasar nan ke ciki.
Alhaji Sheshe ya ce, “Mu na cikin mawuyacin hali, halin da bai kamata a ce ana ta nuna wa ‘yan ta’adda hanyoyin da za su bi a sauƙaƙe su yi ta’addanci ba.
“Kamar yadda na ji bayanin shi shugaban Hukumar Tace Finafinai, bayani ne wanda duk mai hankali ko ya ke cikin masana’antar zai iya gamsuwa da abin da ya faɗa.
“Ni a gani na, ba ma shi da amfani a ce ana nuna ƙwacen waya a cikin fim saboda ba ma shi da amfani da ma abubuwa makamantan wannan saboda abu ne wanda yanzu ya zama shi ne abin da ya fi addabar mu, musamman mu a nan Jihar Kano.”
Ya ƙara da cewa shi bai ɗauki dokar a matsayin wani abu da zai taɓa sana’ar fim ba ko wani abu da zai kawo cikas a masana’antar ba.
A nasa ɓangaren, jarumi, mawaƙi kuma furodusa T.Y. Shaban kira ya yi ga gwammati da ta sake duban wannan dokar domin kuwa wasu ƙasashen har yau su na nuna waɗannan abubuwan duk a cikin fim.
Ya ce, “Idan har aka ce ba a so mu nuna wannan abu na laifi, to kamata ya yi gwamnati ta shigo ta tallafa da kuɗin jarin yin fim, daga nan sai gwammati ta fito ta ce ga abin da ta ke so, sai a yi’.”
Copyright © Fim Magazine. All rights reserved.
www.fimmagazine.com