ALLAHU Akbar! Muhammad Fadeel Tijjani Babangida, ɗan tsohuwar jarumar Kannywood Maryam Waziri, ya riga mu gidan gaskiya.
Hakan ta faru ne sakamakon haɗarin mota da suka yi shekaranjiya Alhamis tare da baban yaron, wato fitaccen ɗan ƙwallon ƙafa na Super Eagles, Tijjani Babangida, da ƙanen sa Ibrahim Babangida (Aruza). Sun yi haɗarin a unguwar Ɗanmagaji da ke garin Zariya.
Kamar yadda mujallar Fim ta ba ku labari jiya, tun a lokacin haɗarin ne shi Ibrahim ya rasu, yayin da aka garzaya da Maryam da Tijjani da kuma mai aikin su zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya.
Allah ya jiƙan mamatan, ya ba Maryam da Tijjani lafiya da kuma juriya, amin.