• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 23, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Fashewar gas a Kano: Ministar Jinƙai na so a ɗau matakan hana aukuwar bala’o’i

by DAGA ALI KANO
May 18, 2022
in Nijeriya
0
'Yan kallo a bakin ginin da ya ruguje (Hoto daga: NEMA)

'Yan kallo a bakin ginin da ya ruguje (Hoto daga: NEMA)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAR Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta ɗaukar matakan hana aukuwar fashewar abubuwa da kuma rugujewar gine-gine a ƙasar nan.

Ta yi kiran ne sakamakon fashewar silindar iskar gas da ta faru a unguwar Sabon Garin Kano har ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Hukumar Gudanar da Aikin Agajin Gaggawa (NEMA), wadda ke ƙarƙashin ma’aikatar ta Sadiya, ta bayyana tun da farko cewa wani gini ya ruguje a sanadiyyar fashewar gas ɗin, kuma an tsamo gawarwakin mutum tara daga cikin bulullukan rusasshen ginin wanda ke daura da inda gas ɗin ya fashe.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa ministar kan aikin jarida ta bayar, wato Nneka Ikem Anibeze, an ruwaito Hajiya Sadiya ta na bayyana alhini kan faruwar lamarin, yayin da kuma ta jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma gwamnatin Jihar Kano.

Ministar ta bayyana al’amarin da cewa wani abu ne mai ƙona rai kuma ibtila’i ne, har ta ƙara da cewa: “Wannan abin baƙin ciki ne. Iskar gas ta fashe, gini ya ruguje, kuma mutane da dama da abin ya ritsa da su sun rasu, sannan ana faman ceto wasu daga cikin bululluka da rodin ginin… wannan babban abin baƙin ciki ne.

“Ina jajanta wa iyalan waɗanda su ka rasu da kuma gwamnatin Jihar Kano. 

“Yawaitar aukuwar fashewar abubuwa a ƙasar nan a cikin ‘yan kwanakin nan ta na da ban-tsoro, kuma mu na kira ga hukumomin da su ka kamata da su yi wani abu da sauri don hana ci gaba da aukuwar fashe-fashe da rugujewar gini a ƙasar nan.”

Wata mota a wajen da silindar gas ɗin ta fashe

Darakta-Janar na NEMA, Alhaji Mustapha Habib Ahmed, ya tura motocin haƙar ƙasa kuma ya riƙa bada umarni wajen aikin ceton rai a wajen da abin ya faru tare da haɗin gwiwar hukumar agajin gaggawa ta jihar, wato SEMA, da ƙungiyar agaji ta Red Cross ta Nijeriya, da hukumar ‘yan sanda, da hukumar tsaron lafiyar ƙasa (Civil Defence) da sauran masu kai agaji don tabbatar da an ceto mutanen da ginin ya zube a kan su tare da kai su asibiti don a yi masu magani.

Bayan fashewar gas ɗin dai, an riƙa yaɗa ji-ta-ji-ta a soshiyal midiya cewa wai bam ne ya tashi, har sai da hukumar ‘yan sanda ta ƙaryata labarin.

Kwamishinan ‘Yanda na Jihar Kano, Alhaji Sama’ila Dikko, ya fito ya ce, “Ba bam ba ne ya tashi, silindar gas ce ta fashe. Mun san hakan saboda wani mutum wanda ya na cikin waɗanda abin ya fara ritsawa da su wani mai walda ne a wannan yankin.

“Mutum huɗu sun rasa ran su, waɗanda sun haɗa da maza biyu da mace ɗaya, amma ba mu sami ɗalibi wanda fashewar ta ritsa da shi ba.”

Loading

Tags: agaji da inganta rayuwabuilding collapseCivil Defence CorpsDisaster Management and Social Developmentfashewar gasgas explosionKanoMinistar Harkokin JinƙaiMinistry of Humanitarian AffairsMustapha Habib AhmedNEMANigerian Red CrossNneka Ikem Anibezepolicerugujewar giniSabon GariSadiya Umar Farouq
Previous Post

Ranar Iyalai ta Duniya: Ma’aikatar Jinƙai za ta agaza wa iyalai mabuƙata 30

Next Post

Zan yi amfani da sarautar da aka ba ni wajen inganta rayuwar matasa, inji Fatima Lamaj

Related Posts

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
Next Post
Jakadiya, Hajiya Fatima Ahmed Ibrahim (Lamaj), tare da dogari jim kaɗan bayan naɗin ta

Zan yi amfani da sarautar da aka ba ni wajen inganta rayuwar matasa, inji Fatima Lamaj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!