MASU iya magana na cewa mai haƙuri shi ke dafa dutse har ya sha romon sa. Lallai tsohuwar jaruma Hajiya Fati Ladan ta na ɗaya daga cikin masu haƙuri da jarabawar Allah (SWT), domin tsawon shekara shida Allah bai ba ta haihuwa ba sai a wannan shekarar.
Fati ta haifi ɗa namiji bayan auren su da shekara huɗu, kafin suna Allah ya karɓi abin sa.
A ranar Talata, 21 ga Mayu, 2019 Allah ya azurta jarumar da mijin ta Alh. Yerima Shettima da santaleliyar yarinya.
Ta haihu a asibitin sojojin sama (‘Air Force Base Hospital’) da ke Kaduna. Da ya ke aiki aka yi mata, ta ɗan zauna asibitin na ɗan wani lokaci duk da cewa a cikin watan azumin Ramadan ta haihu. Bayan kwana biyu aka raɗa wa yarinya suna A’isha Humaira. Amma ba a yi taron suna ba sai bayan wata ɗaya da kwana ɗaya, wato a ranar Asabar, 22 ga Yuni, 2019.
An yi ƙasaitaccen bikin a wani ɗakin taro da ke otal ɗin Tavern da ke Gwamna Road, Kaduna.
An fara bikin da misalin ƙarfe 3:30 na yamma.
Bayan su Fati Ladan sun shigo ɗakin taron sun zauna, jarumi Abbas Sadiq ya buɗe taro da addu’a duk da yake shi ne mai gabatarwa a wurin bikin.
An umarci manyan baƙin da su ka halarci bikin da su je su zauna a wurin da aka tanadar masu na musamman. Daga nan sai aka shiga fagen nishaɗi, inda Buzun Kaduna ya fara buɗe taro da waƙoƙin sa.
Bayan ya gama sai aka kira matan Kannywood su ma su ka cashe da waƙoƙin Ado Gwanja da Adam A. Zango.
Shi ma jarumi Adam A. Zango ba a bar shi a baya ba, domin ya baje kolin sa, aka yi ta yi masa ruwa nairori.
Daga shi sai mawaƙi Salisu Mariri, inda shi kuma waƙa ya yi wa jaririya Humaira da iyayen ta.
Haka dai aka ci gaba da cashewa ana murna da farin ciki.
’Yan fim, musamman mata, sun yi wa ’yar’uwar tasu kara, domin kuwa sun zo da ɗan yawa. Sun haɗa da Adam A. Zango, Al-Amin Buhari, Abubakar S. Garba, Usman Uzee, Zaharaddin Sani, Abdullahi Tasiri, Kabiru A. Zango, Abbas Sadiq, Buzun Kaduna, A.A. Rasheed Kabala, Mansurah Isah, Fati KK, Fati Al-Amin, Wasila Isma’il, Asma’u Sani, Ladidi Tubeless, Hajara Dumɓaru, Saddiƙa Jibrin Sarki, Hadiza Kabara, Maryam Aliyu, Hassana da Hussaina Yusuf, Fati Nayo Fulanin Asali da sauran su.
An ci, an sha, an kuma yi nishaɗi.
An tashi daga taron da misalin ƙarfe 6:00 na yamma.
Allah ya raya A’isha Humaira Yerima Shettima, amin.

