WANI fim mai suna ‘Thinline’ wanda jarumar Nollywood Mercy Aigbe ta shirya ya samu cinikin naira miliyan ɗari a gidajen sinima a faɗin ƙasar nan cikin mako huɗu kacal.
Kamfanin Cinemax, wanda shi ne ya yi hidimar rarraba fim ɗin, shi ne ya bayyana a shafin sa na Instagram, wato @cinemaxng, a jiya Juma’a.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa an saki fim ɗin ‘Thinline’ ne a gidajen sinima a ranar 13 ga Disamba.
Yayin da yake
gode wa ‘yan kallon fim ɗin, kamfanin Cinemax ya ce: “An samu sama da miliyan 100 million, Kuma duk saboda ku ne. Godiya gare ku baki ɗaya saboda ƙaunar ku da goyon bayan da kuka nuna.
“Muna godiya ga dukkan waɗanda suka kalli fim ɗin. Ku kuma waɗanda ba ku kalla ba, don Allah ku je ku sayi tikitin ku domin ku samu cikakken nishaɗi da labarin da ba za ku taɓa mantawa da shi ba.
“Shi dai Thinline ba kawai fim da aka saba gani ba ne, domin yana ɗauke da duk wani abu da za a so a gani.”
Ita ma jaruma Mercy Aigbe ta hau shafin ta na Instagram, wato @realmercyaigbe, domin yi wa masoyan ta godiya.
Ta ce: “Elede mi a de Oyo, Ariwo e lo ma po. Bayan dukkan wahalhalu, bayan dukkan ƙalubalen da na sha, fim ɗina mai ban-mamaki, Thinline yana ta ƙara samun kasuwa.
“Zuciya ta tana cike da godiya ga Allah da kuma dukkan wanda ya mara wa wannan tafiya baya zuwa yanzu. Ina gode maku ƙwarai da gaske.
“Wannan nasara ba ta samu ba sai da soyayyar ku da ƙwarin gwiwar ku da tallafin ku. Don haka, ina miƙa babbar godiya ga dukkan wanda ya kalli wannan gagarumin fim a gidan sinima.”