• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, May 31, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gamsasshen Bayani Game Da Maguzawan IPOH

by DAGA DR. ALIYU U. TILDE
May 3, 2023
in Tsokaci
0
Makaɗan Hausa a fadar Sarkin Zazzau da ke Zariya. Hoto daga: Gerhard Kubik

Makaɗan Hausa a fadar Sarkin Zazzau da ke Zariya. Hoto daga: Gerhard Kubik

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

DA alama tsokacin da na yi kan ƙungiyar Indigenous People of Hausaland (IPOH) ta jawo ce-ce-ku-ce da yawa a yanar gizo a wannan satin. Wasu sun ɓata rai. Wasu na ganin ina adawa da Hausa ko ra’ayin Hausawa su kafa ƙungiyar ƙabilar su. Wasu na ganin ban san ma’anar maguzawa da maguzanci ba ma. To! 

Wasu kam takaici su ka ce na ba su. A shafin sa na Facebook, Marmara Habib Cln ya ce: “Abin takaici ne a ce wannan rubutun Dr. Aliyu U. Tilde ya yi shi. Wallahi abin baƙin ciki ne ƙwarai da gaske. To shi Bahaushe ba shi da damar ya bayyana ‘identity’ ɗin sa kenan? A ce kamar Aliyu Tilde ya ke kiran Hausawa Maguzawa?” Fahimtar sa kenan. Ban ga laifin sa ba saboda ya san ina cikin waɗanda ke kare Hausawa kuma ina cikin waɗanda su ke taimakawa wajen cigaban Hausa a yau.

Kar ku damu. Ga bayani na. Kuma na yi imani a ƙarshen karanta wannan maƙalar, duk wanda ya ke son Hausa da Hausawa da Musulunci da alheri zai gamsu da magana ta.

Ƙungiyar Hausawa

Zan fara da cewa ba na ƙin Hausawa su kafa ƙungiya muddin ta dace da martabar su. Kamar yadda na ba wani amsa, ni har taimaka mata ma zan yi in dai za ta kawo cigaba ga Hausa ne da zaman lafiyar mu a arewacin Nijeriya. Amma ba zan taɓa goyon bayan ƙungiya wacce za ta ruguza martabar Hausawa ta kuma haddasa ƙiyayya a tsakanin ‘yan Arewa ko kasancewa makira ga Musulmi da Musulunci ba. Hakazalika, ba zan goyi bayan ta yi kira zuwa ga abin da Musulunci ke hani da shi ba ko da a Fulatanci ne. Na san 95% na Hausawa za su goyi baya na a kan wannan.

Ni a wa?

Wani zai ce to ni a wa idan Hausawa su na sha’anin su? E, ina cikin masu ruwa da tsaki kan Hausa da Hausawa saboda duk abin da ya shafi Bahaushe yau ya shafe ni. Hausa harshe na ne. Zan yi Hausa sau ɗari ban yi Fulatanci sau ɗaya ba. Wasu ma za su kira ni Bahaushe kuma dole in amsa ina alfahari. Ga abin da na ce bara a waƙe na kan Hausa:

Mu gode wa harshen da yat tattaro mu

Ya maishe mu jinsi guda “Onye Hausa”.

Da Barno, Filato kaza Adamawa

Idan an gane mu a ce mana “Hausa”.

Idan an kira mu Bahaushe mu amsa

Da ƙarfi mu ce musu tushen mu Hausa.

Sannan Hausawa abokan zama na ne. Mu na gari ɗaya. Mafi yawan maƙwabta na Hausawa ne. Abin da ya shafe su ya shafe ni. Tare mu ke gwagwarmayar rayuwa, mu ke fuskantar ƙalubale iri-iri daga waɗanda ba sa ƙaunar mu ko son zaman lafiyar mu.

A Nijeriya kuma inuwar mu guda. Idan za a yanka Bahaushe a Inugu da ni za a haɗa idan ina kusa. Ko na ce ni Bafulatani ne aikin banza ne. A Zangon Kataf ko Jos ko Numan haka abin yake. Haka nan idan an zo ta’addanci ko siyasa. Yadda Boko Haram ko OPC ko IPOB in za su kai hari kan Bahaushe haka za su kai hari gare ni. Yadda ‘yan ta’adda, hatta a cikin Fulani, za su kai hari ga Bahaushe haka za su kai hari a gare ni. Sun sace sarakunan Fulani, da ‘ya’yan Fulani, da dabbobin Fulani kamar —ko kafin ma su fara ɗaukar — Hausawa. Balle a siyasar Nijeriya. Inuwar Bahaushe ita ce inuwa ta.

A yare kuwa, duk da cewa ni ba ƙabilar Hausa ba ne, Bahaushe bai kai ni amfani da Hausa ba, ko nazarin ta ko rubuta ta, a zube da waƙe. Wannan bayanin ga waɗanda ke bibiya ta sun san haka yake; ga waɗanda ba su san ni da jimawa ba, wata rana zan faɗaɗa shi.

IPOH

To meye illar ƙungiyar Indigenous People of Hausaland (IPOH) da zan ce masu Maguzawa kuma abin da su ke yi maguzanci ne, har ya sa na tsane su kuma na ce Hausawa su yi hattara da su? Biyo ni.

Na farko dai cewar su “native indigenous” a sunan da su ka yi amfani da shi wajen yaɗa wata buɗaɗɗiyar takarda zuwa ga Tinubu ya na nuna cewa su na nufin Hausawan asali, waɗanda kuma a sanin kowa su ne Maguzawa. Wannan ba kalmar zagi ba ce kamar yadda wasu su ka ɗauka. Su ne Turawa ke kira ‘Hausa pagans’ lokacin mulkin mallaka, sauran arna kuma su ce masu pagans kai-tsaye.

Sai dai wasu kila su ce gara in yi amfani da kalmar ‘Hausawan asali’ a maimakon Maguzawa saboda a Hausa Bamaguje shi ne Bahaushen da bai karɓi Musulunci ba ko da kuwa Kirista ne, alhali kalmar Bahaushe ta fi sifantuwa da Musulmin Bahaushe. Na ji daɗi da na ga wannan ma shi ne bayanin da mai rubutu a kan Hausawa a kafafen sada zumunta da jaridu, watau takwara na, Malam Aliyu Ammani, ya yi a Daily Trust. Yanzu ne wasu ke neman amfani da kalmar Bahaushe ta haɗa da Bamaguje ba tare da bambancin addini ba.

Daga cikin matsalolin da za a fuskanta shi ne ya za a yi da Hausawan da ba Hausawan asali ba, bayi ne ko zuri’ar bayin Hausawa da Fulani waɗanda aka kawo daga wurare daban-daban na tsohuwar Daular Borno da arewa-maso-gabas da arewa-ta-tsakiya ta Nijeriya? Waɗannan fa su na da yawa sosai. Barth, alal misali, ya samu a 1885 cewa sama da 50% na mazauna birnin Kano bayi ne. Kusan haka abin yake a garuruwan Arewa da yawa. Da zuwan Turawa, kamar yadda Yusufu Turaki ya rubuta a Tainted Legacy, waɗannan duk “sun zama Hausawa (kuma Musulmi) saboda su na magana da Hausa” (shafi na 71-72) In ka taso da fitinar asali, ina za ka kai su tunda su ba Hausawan asali ba ne?

Ah. To idan ka ce tunda su na jin Hausa sun zama Hausawa, me zai hana to ka yarda cewa zuri’ar Shehu Ɗanfodiyo, waɗanda da ƙyar yau a samu mutum guda mai jin Fulatanci a cikin su, su ma Hausawa ne?

Maguzanci

Sai batun maguzanci da na caji ‘yan IPOH da shi. To maganganun su su su ka nuna haka. Membobin su na yin abubuwa da ba ɗabi’ar Bahaushe Musulmi ba ne, amma sun fi kama da na wanda ke da wani mugun nufi ga wasu mutane da ba sa so, waɗanda kuma su ne taurari a harkar Musulunci a nan arewacin Nijeriya. Wannan kuma ba shaci-faɗi ba ne; ni ganau ne, ba jiyau ba.

Wacce ta ke jagorantar wannan da’awa ta na kiran kan ta Kaltume Alumbe Jitami, a wasu wuraren ana ce mata Jarumar Hausa, kuma ita ta sa hannu a waccar buɗaɗɗiyar takarda da aka rubuta ga Tinubu daga “Native Indigenous People of Hausaland.” Wannan mata ta shahara wajen cin mutuncin Fulani, da shugabannin Fulani, musamman Shehu Ɗanfodiyo, da fitattun malaman Musulunci waɗanda fiye da kashi 80 cikin ɗari nasu su na da jinin Fulani a jikin su; kai, har da kowane Bafulatani. Kowa a cikin waɗannan mutane ta yi jama’u ta kira shi ɗan ta’adda. Ni kam ma ta kira ni Aliyu Turji, da ta gagara faɗar Tilde ɗin a wani audiyo. Ta ce duk ɗaya ne, da Turji da Tilde. Fulani ne, ‘yan ta’adda. Na sha dariya!

Sannan ta fito ta na yi wa Maguzanci kirari. Maguzanci kuwa addinin Maguzawa ne. Sannan ta faɗaɗa ma’anar Maguzancin har ta ce iyayen Annabi (SAW) da sahabbai duk sun yi Maguzanci. To idan haka ne, me zai hana ba za ta haɗa da kakannin Fulani ba? A’a. Su Fulani a ganin ta ba su da darajar da za a ce kakannin su Maguzanci ne. ‘Yan ta’adda ne.

Cin Mutuncin Fulani

To sai na ga tabbas alfahari da jahiliyya da arnanci, ko a ce Maguzanci, abu ne da bai dace da Musulmi ba. Kuma ba Musulmi Bahaushe da ya san ƙimar kan sa da zai kama sunayen akasarin malamai ya riƙa ɗura masu ashar da keta mutuncin su idan ba Maguzanci ya fi ƙarfin zuciyar sa ba. Wannan ba martabar Hausawa Musulmi da mu ka sani ba ce, malaman su da jahilan su. Kowa ya san me Shehu Ɗanfodiyo ya yi. Jihadi ya yi. To wanda zai ce wa jihadi ta’addanci, kuma ya na alfahari da Maguzanci, idan ban kira shi Bamaguje mai Maguzanci ba me zan kira shi da shi? Ba a nan maganar ta ƙare ba.

Ina cikin guruf-guruf da dama waɗanda ita wannan Bamagujiya ta kafa. Ina ganin abubuwan cin mutuncin da ta ke yaɗawa a ciki, da goge duk wani abin Musulunci wanda ya saɓa da maganganun makircin ta, da cire duk wanda bai yarda da ra’ayin ta ba. Ta na ta fama sai annobar ta ta addabi kowane gari a arewacin Nijeriya. Ta buɗe guruf har da na su “Hausa Bauchi”, Hausa Nijar da Hausa Abuja; a bar na su Kano, da Katsina da Zamfara. Mu na jiran Hausa Borno da Hausa Yobe da Hausa Adamawa da Hausa Jos. A yawancin guruf-guruf ɗin, ba wasu masu tura saƙo face ita. Ita ta ke kiɗan ta kuma ta yi rawar ta. Sai ta riƙa kwaso tarkacen da aka sa a wasu guruf-guruf ɗin game da Fulani da zagin Fulani ta riƙa yaɗawa a cikin waɗannan guruf-guruf ɗin.

Bincike kaɗan ya nuna ita wannan mata an ce wai Musulma ce, kila daga Hausawan da su ka rasa mulki lokacin jihadin Shehu Ɗanfodiyo. Amma mutanen da ta ke alaƙa da su akasari waɗanda Bahaushe Musulmi ba zai zauna inuwa ɗaya da su ba ne. Zan yi ƙarin bayani a kan wannan a nan gaba.

Yau a ce wannan mata ita ta kafa ƙungiya mai suna irin na IPOB, ta na kira zuwa ga cin mutuncin Fulani da murya wacce ta saɓa wa dokokin amfani da yanar gizo (Cybercrime Act), da kira zuwa ga ƙabilanci mai muni wanda Musulunci ya hana, me zai sa ba zan ce Hausawa, masoya na, dangi na, abokai na, da maƙwabta na, da Musulmi iri na, su yi hattara ba?

Yau in da ƙungiya ce Hausawa managarta su ka kafa su na kira ga samun hanyoyin da za a raya ƙasar Hausa da warware matsalolin ta irin su ta’addanci da talauci da jahilci da rashin aikin yi, da ina kan gaba wajen mara masu baya. Amma ko Bafulatani ne ya yi abu bisa ƙabilanci ba zan goyi bayan sa ba.

Ƙabilanci

Kuma komawa ga ƙabilanci cibaya ne sosai zai kawo wa Hausa da Hausawa. Amma wannan bayanin sai wani jiƙon. Kamar Larabawan asali na Arebiya ne yau su ware kan su, su ƙyamaci sauran al’ummomin da su ka rungumi Larabci su ka mance da yarukan su na asali, a Iraki, Siriya, Lebanon, Masar har Morokko. Hausa ta kai minzalin Larabci a ƙasaita. Alfaharin ta jama’ar ta, da harshen ta ba asalin ta ba. Ta nan ta ke samun faɗaɗa da ɗaukaka, mutane da yawa waɗanda ba Hausawa ba iri na su ke magana da ita kuma su ke mata hidima. 

Ga waɗanda su ka waye, ko wasu ne ke da kalmomi a yaren su da su ke kama da na hausar su sai su jawo su cikin su. Haka Larabawa su ka yi. Mutanen Somaliya, misali, ba da Larabci su ke magana ba, amma su na cikin ƙungiyar Larabawa. 

Idan aka ɓullo da wannan da’awar cin mutunci da gorin asali, anya Hausa za ta zame harshen koyarwa da na ofis a Arewa nan gaba kuwa? Wayayyun Hausawa ya kamata su kira duk ƙabilun da ke magana da Hausa su sanya su cikin ƙungiyar Hausawa don cigaban Hausa da jama’ar ta. Har Dr. Tilde ma su ba shi Babban Sakataren ƙungiyar, su ga aiki ba kama hannun yaro. Amma kash! An bar nama na jan kare. Wai masu aƙidar wariya ta IPOH su ne jagororin ƙungiyar ƙabilar Hausawa.

Misali

Ana kawo misali da Yarbawa Wabi su na da ƙungiyar Afenifere. Yaushe Bahaushe Musulmi zai lalace ya zama kamar Afenifere? Ai Afenifere babbar aƙidar ta danne Musulmi da Musulunci a ƙasar Yarbawa. Shi ya sa ba ta goyi bayan Tinubu ba.

Akwai kuma misalin ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria wacce wasu Hausawa su ke cewa “to ai Fulani su ma su na da ƙungiya”. Akasarin ‘yan Miyetti Allah Fulani ne amma ba don ƙabilancin Fulatanci aka yi ƙungiyar ba. Don kiwo aka yi ta. Makiyaya kuma na kowace ƙabila su na iya shiga, sai dai in ba sa so. Da wannan matsalar rashin ilimi da rashin cigaban Fulanin daji da fashin daji ta taso, akwai ƙungiyoyi masu zaman kan su, NGOs, da aka yi ta kafawa ban da Miyetti Allah, amma dukkan su ayyukan cigaba ne ya haɗa su don samun yadda za a warware matsalolin, ba makirci don ƙyamatar wata ƙabila ba. Duk wanda ya kawo ƙabilanci, taka masa birki ake yi. Na shaida wannan.

Ta’addanci

Haƙiƙa, harkar ta’addanci a arewa-maso-yamma ta jawo tsagewar bango tsakanin Hausawa da Fulanin daji. Wannan abu ne da ya kamata mu haɗa kai don a shawo kan sa, a toshe shi, amma ba a bari wasu ƙadangaru su yi amfani da shi ba don kawo wata tsohuwar ajandar raunata Musulunci da mutanen Arewa ta hanyar jawo ɓaraka tsakanin Hausawa da Fulani da ƙasƙantar da Bahaushe zuwa ƙabila. Shi ma wannan zan yi faffaɗan sharhi a kan sa wata rana. Kar a mance, ɗan ta’adda bai bambance tsakanin Bafulatani da Bahaushe. Ba wanda bai kamawa ko kashewa ko ƙwace wa dukiya.

Da su Shehu Ɗanfodiyo, Bello da Abdullahi na da rai da iko, da sun ta da runduna a take su shiga dazuzzukan nan su yaƙi ‘yan fashin da su ka addabi al’umma. Mu ma abin da ya kamata mu yi kenan. Da da hali, wallahi da ni zan jagoranci wannan rundunar a yau, ko da ta Fulani ce kaɗai, alabasshi in ce Bahaushe ya sha kurumin sa. Amma tsarin mulkin zamani ya keɓance ikon amfani da bindigogi ga gwamnati da jami’an ta. Don haka ita gwamnatin ya kamata mu taru mu matsawa ta kawo ƙarshen lamarin kuma ta kare kowa da kowa, ba mu lalace mu koma zagi da cin mutuncin juna ba, bayan mun zauna ɗaruruwan shekaru tare, kuma akwai dubban shekaru na jiran mu a gaba.

A Ƙarshe…

A ƙarshe, waɗannan su ne dalilai na na cewa IPOH ba ta cancanci wakiltar Hausawa ba saboda ɗabi’un ta na cin mutuncin ɗan’adam, da ƙabilanci, da karya doka, da rashin mutunci, wanda Bahaushen da ya san Allah ya wuce wurin tun tuni har ta kai idan ya ce ‘ ƙabila’, to ya na nufin wanda ba Bahaushe ba. To ta yaya kuma yau za a jawo shi cikin ƙabilanci ya yarda?

A samu wata ƙungiyar dai, amma ba IPOH ba. Ba laifi IPOH, kamar yadda sunan ta ya nuna, ta shugabanci Maguzawa da Maguzanci, amma ba Hausawa ba waɗanda akasarin su Musulmi ne masu mutunci, da daraja, da sanin ya-kamata, da son zaman zaman lafiya, irin ‘Aliyu Turji.’

Haza wasalam.

* Dr. Aliyu U. Tilde ya rubuto ne daga Bauchi

Loading

Tags: Aliyu TildeDanfodiyoharsheHausaHausawaIPOHkabilaMaguzanciMaguzawayare
Previous Post

Marubutan gargajiya da ‘yan onlayin sun yi taron fidda jaki daga duma a Kano

Next Post

Mun kwaso ‘yan Nijeriya 376 daga Sudan, kuma ba za mu bar ko mutum ɗaya a baya ba – Sadiya Farouq

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida)
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Hajiya Sadiya Umar Farouq ta na marhabin ga waɗanda aka dawo da su Abuja daga Sudan

Mun kwaso 'yan Nijeriya 376 daga Sudan, kuma ba za mu bar ko mutum ɗaya a baya ba - Sadiya Farouq

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!