A YAU Asabar, 20 ga Agusta, 2022, fitaccen mawaƙi kuma jarumi Garzali Mika’ilu Mailemu, wanda aka fi sani da suna Garzali Miko, ya jaddada zurfin soyayyar sa ga matar sa, Habiba Ahmad Dikwa, a daidai ranar da su ke cika shekara ɗaya cif da aure.
Jarumin ya jaddada soyayyar ne a saƙon da ya wallafa a Instagram, inda da farko ya ɗora hotunan musamman da ya ɗauka da iyalin sa.
A hoto na farko, shi da Habiba ne da ɗan su, inda ya yi rubutu da Turanci cewa: “It’s easy to fall in love, but staying in love with the same person for the rest of one’s life is considerably more difficult.
“May God provide us the strength to stay committed to one another. Happy Anniversary.”
Ma’ana. “Abu ne mai sauƙi faɗawa soyayya, amma zama a cikin soyayya tare da mutum ɗaya a cikin rayuwar sa abu ne mai matuƙar wahala.

“Ya Allah ka hore mana ƙarfin zama da jajircewa da juna. Barka da zagawowar ranar auren mu.”
Haka kuma a hoton da ya ɗora na biyu, wanda shi da matar ne, abin da ya rubuta a farko shi ya sake rubutawa.
Wakilin mu ya yi ta kiran mawaƙin don jin ƙarin bayanin da zai yi dangane da wannan rana ta murnar zagayowar ranar auren su, amma bai ɗaga wayar ba, kuma bai maido da saƙon ya tura masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
Idan ba ku manta ba, mujallar Fim ta ruwaito labarin ɗaura auren Garzali da Habiba da aka yi a ranar Juma’a, 20 ga Agusta, 2021 a Kaduna.
An ɗaura auren a kan sadaki N200,000.
Auren ya yi albarka, ga shi ya fara yabanya.