HUKUMAR Tace Finafinai ta Jihar Kano ta sake kama shahararren mawaƙi Nazir M. Ahmad (Sarkin Waƙa).
Ɗan’uwan sa, darakta Aminu Saira, shi ne ya sanar da haka a shafin shi na Instagram, inda ya ce: “Ina mai alhinin sanar da ‘yan’uwa da abokan arziki cewa Hukumar Tace Finafinai, ƙarƙashin Gwamnatin Jihar Kano, ta sake kama ɗan’uwa na, Nazir M. Ahmad (Sarkin Waƙa).
“A yanzu haka ya na tsare. Ƙarin bayani na nan tafe.”
Mujallar Fim ta ruwaito cewa wannan ba shi ne karo na farko da hukumar ta kama Nazir ba, domin kuwa a shekarar da ta gabata ne ta fara kama shi bisa zargin sakin wani kundin waƙoƙi ba tare da ya je hukumar ta tantance su ba.
An gurfanar da shi a kotu, inda daga baya ya samu beli.
Wata majiya ta bayyana wa mujallar Fim cewa wannan kamun da aka yi wa mawaƙin ya na da nasaba da wancan kes ɗin na bara.
Majiyar ta ce da ma can a bisa beli ne aka bar Nazir ya na shawagi, to amma kuma wai ya karya ƙa’idar belin, “shi ya sa aka sake kama shi”.
Majiyar ta ce hukumar ta fito da sababbin tsauraran ƙa’idojin beli, waɗanda su ka haɗa da tilas ne mawaƙin ya kawo wani babban basarake, kamar wakilin Sarki a gundumar su, ko wani babban darakta a gwamnatin Jihar Kano, domin ya tsaya masa kafin a ba shi sabon beli.
Majiyar ta ce, “Samun sabon belin zai ɗan yi wuya domin da yawa a gwamnati da kuma masarauta ana kallon Nazir a matsayin ɗan adawa.”
Nazir dai shi ne Sarkin Waƙar Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II, wanda aka tuɓe kwanan baya.
Mujallar Fim ta yi ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun hukumar tace finafinan kan wannan sabon salo da shari’ar Nazir ta ɗauka, amma sai ya bayyana mana cewa shi ma bai da masaniya kan kama mawaƙin da aka yi.
Haka kuma wakilin mu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin shugaban hukumar, Alhaji Isma’ila Na’abba (Afakallah), amma hakan ma ba ta samu ba.