• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, July 21, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Hukumar Hisbah ta goyi bayan manufofin ƙungiyar mata ‘yan fim

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
August 27, 2022
in Labarai
0
Mata 'yan fim daga ƙungiyar AKAFA a ofishin Kwamandan Hisbah, Ustaz Haruna Sani Ibn Sina

Mata 'yan fim daga ƙungiyar AKAFA a ofishin Kwamandan Hisbah, Ustaz Haruna Sani Ibn Sina

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Hisbah ta Jihar Kano ta bayyana goyon baya ga manufofin sabuwar ƙungiyar nan ta matan Kannywood mai suna ‘Association of Kannywood Female Artistes’ (AKAFA) tare da yaba wa ayyukan ta. 

Yabon ya fito ne daga bakin Babban Kwamandan hukumar, Ustaz Haruna Sani ibn Sina, a lokacin da wata tawagar ƙungiyar ta kai masa ziyara a ofishin hukumar da ke unguwar Sharaɗa a cikin birnin Kano.

A jawabin sa ga maziyartan, Ustaz Ibn Sina ya nuna farin ciki da ziyarar da ƙungiyar ta kai masu tare da cewa manufofin ƙungiyar da yadda su ke tafiyar da su sun yi daidai da ayyukan Hukumar Hisbah na daƙile ayyukan ɓarna, don haka hukumar ta amince da ta bai wa ƙungiyar goyon baya wajen cimma manufofin ta na gyara, domin inganta rayuwar matasa. 

Shugabar AKAFA, Hajiya Rashida Adamu Maisa’a (a gaba), ta jagoranci membobin ƙungiyar zuwa Hukumar Hisbah

Tun da farko da ta ke Jawabi a game da zuwan nasu, sai da Shugabar ƙungiyar ta AKAFA, Hajiya Rashida Abdullahi Maisa’a, ta bayyana cewa sun je hukumar ne domin gabatar da kan su da kuma neman a haɗa hannu a yi aiki tare domin magance matsalar da ke tasowa a cikin ‘yan fim lokaci zuwa lokaci, wanda in aka haɗa ƙarfi, za a samu a yi maganin matsalolin.

Ita ma a nata jawabin, Mataimakiyar Shugaban Hukumar Hisbah a ɓangaren mata, Malama Ummukhulsum Ƙasim, ta yaba wa yunƙurin mata’ yan fim na kafa ƙungiyar da su ka yi da kuma tunanin su na tsaftace sana’ar su tare da yaba masu wajen kyautata mu’amala da kamun kai. 

Shi ma mai ba Gwamna shawara a kan hukumar ta Hisbah, Alhaji Mujittaba Baban Usama, ya yi masu fatan alheri tare da kira a gare su da su tsarkake niyya a wajen gudanar da aikin nasu yadda za a samu a inganta tarbiyyar al’ummar Musulmi.

Tun dai bayan kafa ƙungiyar a watan Yuli da ya gabata, shugabannin ta su ka tashi tsaye domin zagayawa da kai ziyara ga manyan mutane da hukumomi a Jihar Kano domin gabatar da ƙungiyar da kuma neman goyon bayan su a game da aikin da ƙungiyar ta sa a gaba na tsaftace masana’antar shirya finafinan Hausa.

‘Yan AKAFA tare da Mataimakiyar Kwamandan Hisbah a ɓangaren mata, Hajiya Ummukhulsum Ƙasim, a lokacin ziyarar
Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Ustaz Haruna Sani Ibn Sina, a lokacin ziyarar matan na Kannywood

Loading

Tags: AKAFAHaruna Sani Ibn SinaHukumar HisbahKannywood female artistesKanomatan KannywoodMujittaba Baban UsamaRashida Adamu Abdullahi Maisa'a.Ummukhulsum Ƙasim
Previous Post

Murna ta cika Maryam Mushaqqa da mijin ta kan auren ‘yar su Illaf ran Asabar

Next Post

Cewar gwamnatin Kano: Jama’a ku taya mu mu kama Safara’u da Mr 442 domin a hukunta su

Related Posts

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 
Labarai

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

June 29, 2025
Next Post
Safiya Yusuf (Safara'u) da Mubarak Abdulkarim (Mr 442)

Cewar gwamnatin Kano: Jama'a ku taya mu mu kama Safara'u da Mr 442 domin a hukunta su

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!