• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, June 4, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

INEC ta aika wa Buhari wasiƙar amincewa da Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe

by DAGA WAKILI
December 10, 2021
in Nijeriya
0
Shugaban Ƙasa Buhari da Shugaban INEC Mahmood Yakubu

Shugaban Ƙasa Buhari da Shugaban INEC Mahmood Yakubu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta aika wa Fadar Shugaban Ƙasa da wasiƙar da batutuwan da Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe ya ƙunsa.

Sai dai kuma hikumar ta shawarci Shugaba Muhammadu Buhari da ya tuntuɓi jam’iyyun siyasa da ɓangarorin jami’an tsaro dangane da ƙudirin da aka shigar cewa zaɓen ‘yar-tinƙi jam’iyyu za su riƙa yi a wurin zaɓen fidda-gwanin ‘yan takara.

A ranar 29 ga Nuwamba ne Majalisar Dattawa ta aika wa Buhari Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe, wanda shi kuma a bisa doka ya na da kwana 30 kacal da zai ɗauka ya sa wa ƙudirin hannu domin ya tabbata doka kenan.

Shi dai wannan sabon ƙudiri, matsawar Buhari ya sa masa hannu, to ya shafe Dokar Zaɓe ta 2010 kenan, wadda ita ce aka yi wa kwaskwarima.

A cikin kwaskwarimar an nemi a riƙa yin zaɓen ‘yar-tinƙi wajen fitar da ‘yan takara.

Sai kuma batun aika sakamakon zaɓe ta yanar gizo da sauran na’urori da kafafen sadarwa na zamani.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Fargesa Ibrahim Gambari, shi ne ya rubuta wa INEC wasiƙa, inda ya nemi hukumar ta rubuto shawarwari ga Buhari kan batutuwan da Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe su ka ƙunsa.

Gambari ya shaida wa INEC cewa kada shawarwarin su wuce ranar 3 ga Disamba.

Batun a koma yin zaɓen ‘yar-tinƙi wajen zaɓuɓɓuka na fidda-gwanin takarar jam’iyyu ya haifar da ka-ce-na-ce a cikin jam’iyyar APC mai mulki. Yayin da ‘yan majalisa waɗanda mafi rinjaye ‘yan APC ne, su da ɓangaren Bola Tinubu ke goyon bayan ‘yar-tinƙe, su kuma yawancin gwamnoni sun fi so a bar tsarin yadda ya ke, wato wakilai su riƙa yin zaɓen fidda-gwani tun daga mazaɓu har zuwa sama.

Loading

Tags: Dokar ZaɓeFarfesa Mahmood YakubuHukumar Zaɓe ta ƘasaIndependent National Electoral CommissionINECShugaba BuhariZaɓen 2023
Previous Post

An ba Umar Gombe ragamar shugabancin ‘yan fim na Kano

Next Post

Tarihin Fulani: Mahangai huɗu

Related Posts

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London
Nijeriya

Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

May 16, 2025
Tinubu ya yaba wa Sule Lamiɗo a taron ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar sa
Nijeriya

Tinubu ya yaba wa Sule Lamiɗo a taron ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar sa

May 13, 2025
Next Post
Waɗansu 'yanmatan Fulani a ƙasar Benin. Hoto daga: Alamy

Tarihin Fulani: Mahangai huɗu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!