• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, April 5, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

INEC ta nesanta kan ta daga zargin baddala ƙuri’un zaɓen gwamnan Kogi a Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe, IRev

by DAGA WAKILIN MU
November 15, 2023
in Nijeriya
0
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ko kaɗan ba ta baddala sakamakon zaɓen da ta aika a Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe (IReV) ba.

INEC ta ce ta lura da wasu rahotanni da ta riƙa cin karo da su a kafafen yaɗa labarai, inda ake zargin ta da hargitsa sakamakon zaɓen da ta tura a manhajar IReV, na zaɓen gwamnan Jihar Kogi.

Kogi na ɗaya daga cikin jihohi uku da aka yi zaɓen gwamna, a ranar 11 ga Nuwamba. Sauran jihohin biyu su ne Imo da a Kudu maso Gabas da kuma Bayelsa a Kudu maso Kudu.

Cikin sanarwar da INEC ta fitar a ranar Talata, ta ja yankulan jama’a cewa su yi watsi da zargin hukumar ta baddala sakamakon zaɓen da ta loda a manhajar IReV.

Ta bayyana cewa wannan zargi da aka yi wa hukumar “ƙage ne kawai da ƙarairayin bugar da hankulan jama’a.”

Wannan kakkausan martani na INEC na ƙunshe cikin wata sanarwar da Kwamishinan Tarayya na hukumar, Mohammed Haruna ya fitar a ranar Talata.

Haruna ya ce: “Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta lura da wasu rahotanni da ke ɗora mata zargin baddala sakamakon yawan adadin ƙuri’un da ta loda kan Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe, wato IReV, a jihar Kogi. To ko ma daga ina, labarin ya fito dai ƙarya ce.

“Duk mai wata tababa ko shakku ya sani cewa sahihan adadin yawan waɗanda aka tantance karin shaidar zaɓen su na nan killace cikin Na’urar Tantance Adadin Masu Zaɓe (BVAS), wadda da ita ce ake amfani wajen tantance adadin masu rajistar da za su yi zaɓe a ranar zaɓen. Kuma adadin yawan masu zaɓen ha zai taɓa canjawa ba a cikin na’urar.”

Haruna ya ce batun duba adadin alƙaluman sakamakon zaɓe a manhaja ya danganta ne idan akwai ‘network’ ko babu.

Ya ce idan aka tura sakamakon zaɓe a IReV, to ba lallai ne ya isa a lokacin da aka tura ba. Kamar dai yadda saƙon tes na SMS ta waya ya ke, ba lallai ya isa lokacin da aka tura ba. Wani ya kan yi latti.

Daga nan sai ya ƙara da ce aikin Jami’an Zaɓe ne su danna ɗan maɓallin data kan Na’urar Tantance Masu Katin Zaɓe, wato BVAS domin tabbatar da an tura data a manhajar.

INEC ta ce babu inda ta baddala sakamakon zaɓe don a zalinci wani ɗan takara ko a fifita wani ɗan takarar kan wani.

Hukumar ta ce dukkan sakamakon zaɓen da aka gani a jihohin uku, shi ne abin da jama’a suka zaɓa, kuma shi ne INEC ɗin ta bayyana.

Haruna ya yi bayani dalla-dalla cewa babu yadda za a yi a iya baddala sakamakon zaɓen da adadin yawan rajistar da BVAS ta tantance idan an loda shi a manhajar IReV.

Idan ba a manta ba, tun a ranar zaɓe INEC ta fito ƙarara kamar yadda ta saba yi a kowane zaɓe, cewa ba ta da ɗan takarar ko ɗaya. Ɗan takara a cewar ta, na jam’iyya ne da ‘yan jam’iyya. Don haka sai wanda jama’a suka zaɓa.

Aikin INEC inji hukumar shi ne shirya zaɓe sahihi kuma karɓaɓɓe, kamar yadda a kowane lokacin ta ke yin bakin ƙoƙarin ta.

Loading

Previous Post

Ƙasashen Larabawa da na Musulmai sun haɗa kai wajen yin tir da hare-haren Isra’ila a Zirin Gaza

Next Post

Aiki sai mai shi: Ayyukan raya jiha da inganta rayuwar jama’a fiye da 300 a Kasafin 2024 na gwamnatin Namadi a Jigawa

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Gwamna Umar Namadi (a hagu) ya na miƙa kundin Kasafin 2024 ga Kakakin Majalisar Dokokin Jigawa, Alhaji Haruna Aliyu Ɗangyatun

Aiki sai mai shi: Ayyukan raya jiha da inganta rayuwar jama'a fiye da 300 a Kasafin 2024 na gwamnatin Namadi a Jigawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!