ABDULLAHI Abubakar, wanda aka fi sani da Auta Waziri, ba ɓoyayye ba ne a harkar waƙa. A wannan zamanin ya na ɗaya daga cikin mawaƙan da tauraron su ke haskawa a Kannywood.
Auta dai matashi ne, kuma ya haura shekara sha biyar a harkar waƙa. Asalin sa ɗan Zariya ne ta Jihar Kaduna, harkar waƙa ce ta sa ya dawo garin Kaduna da zama.
Duk da cewa an san sunan sa da waƙoƙin sa a baya, sai a shekarar 2022 ce Auta ya ƙara samun ɗaukakar da waƙoƙin sa su ka zaga ko’ina a faɗin Nijeriya, har maƙwafta.
Mujallar Fim ta tattauna da matashin mawaƙin, inda ya faɗi taƙaitaccen tarihin sa, da yadda ya tsinci kan sa a harkar waƙa, da dalilin da ya sa ya canza suna daga Autan Naziru zuwa Auta Waziri, da alaƙar sa da Momee Gombe, da sauran su. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
FIM: Ka faɗa wa masu karatu tarihin ka a taƙaice.
AUTA WAZIRI: Suna na Abdullahi Abubakar, wanda aka fi sani da Auta Waziri. Ni haifaffen Samaru ne, Samarun Zariya. Sannan kuma in ce mazaunin Jihar Kaduna, duk dai na daɗe a Kaduna, shekara goma sha, na zama ɗan Kaduna. Wannan shi ne a taƙaice.
FIM: Ya aka yi ka tsinci kan ka a harkar waƙa?
AUTA WAZIRI: Alhamdu lillahi. Ni dai gaskiya waƙa wata aba ce da tun ina ƙarami na ke sha’awar yin ta. Ko kuma in ce na kan yi tunani in wani abu ya faru, sai in ce wannan abin da ya ke faruwa, ta ina mutane da yawa za su san ya faru. Shi ne tunani na a lokacin ina ƙarami, ina aji biyu in na ji waƙa sai in rinƙa tunanin ta ya aka yi wannan ya yi tunani irin wannan, har ya rera mutane su ke saurare? Saboda haka, wannan abin shi ya ja hankali na, na ga ga hanya mafi sauƙi da zan isar da saƙo, shi ne na ce to bari dai in fara gwadawa na gani ko za a iya sauraren nawa.

FIM: Da wace waƙa ka fara, kuma a wace shekara?
AUTA WAZIRI: Kai, gaskiya shekarar da na fara waƙa da daɗewa! Domin tun ina ɗan shekara goma na ke ɗan rubuta waƙa, amma ban je situdiyo na rera ba. Zan dai iya cewa zan kai aƙalla shekara sha biyar; kai, na ma fi haka.
FIM: Wanene maigidan ka a harkar waƙa?
AUTA WAZIRI: E to, gaskiya ban taɓa sanin ya ake mutum ya ke zama maigida a wurin mutum ba. Kawai dai na san cewa na je situdiyo na yi waƙa, kuma da na rubuta waƙar, ta daɗe ina ta rihazal kafin na je na biya situdiyo na buga ta. Kawai dai na san akwai waɗanda su ka ɗan tallafa min, ka san lokacin ba kuɗi, babu yadda za ka yi, wanda har mijin ƙanwa ta ya taɓa ba ni wani abu, abin da ba zan taɓa mantawa ba, har da wani yaya na su ka rinƙa haɗa min kuɗin situdiyo. Duk wanda na haɗu da shi haka, sai in ciro takardar in yi, sai a ce kai waƙar nan ta yi daɗi.
FIM: Wannan maganar da ka yi na mijin ƙanwar ka da yayan ka sun sha ba ka kuɗi ka je ka yi waƙa a situdiyo, hakan ya nuna cewa ba ka samu ƙalubale ba a gida kenan da ka fara waƙa?
AUTA WAZIRI: Kai, ai ko ƙalubale an same shi! Saboda akwai kawu na, wanda shi ne mahaifi na, domin mahaifi na ya rasu, shi dai gaskiya bai so in yi harkar waƙa ba, kuma babu irin faɗan da bai yi ba, da sauran su. Ka san duk inda Allah ya tsara abincin mutum, babu yadda za a yi. Kuma duk abin da Allah ya tsara shi a haka za ka ɗauki ƙaddara. Ya dai yi iya ƙoƙarin sa gaskiya.
Sai kuma ɗan isgilanci dai na abokai da ‘yan unguwa da ba a rasa ba, tonon faɗa da waye, da dai wasu abubuwa dai na wasu lokuta za ka yi aiki, musamman aiki na ‘yan siyasa a wancan zamanin, kai ta wahala, a ce je wuri kaza, irin waɗannan wahalhalun, ka yi tafiya, ƙila ka je kai wani aikin kun yi magana, ka je a ce ba ya nan ya yi tafiya, da sauran su. Duk irin waɗannan abubuwan idan mutum ya na farko-farkon yin waƙa ya na fuskantar su kafin ya kai matakin da ya ke buƙatar ya kai.
FIM: A baya ana kiran ka da Autan Naziru, sakamakon ka na waƙa da irin muryar sa da kuma salon waƙar sa. Daga baya kuma sai aka ji ka koma amsa Auta Waziri. Me ya faru?
AUTA WAZIRI: E to, gaskiya a lokacin na ɗan samu wasu ‘yan ƙananan matsaloli ne, musamman a lokacin da na ke waƙar sarauta ka’in da na’in, wanda har yanzu ina yi sosai, amma lokacin da na ke yin su ka’in da na’in Naziru ya na tashe farko-farkon zuwan shi shi ma, sai ake ce min Autan Naziru, in na yi wani aikin sai wasu mutanen su je su ce Naziru ne, lokacin sai aka rinƙa haɗa ni da shi, wani lokacin sai wani ya je ya yi abin da ba ni na yi ba, sai a ce ai ni ne, murya na ɗaya da shi, masu yin irin farisin waƙa haka su je su yi waƙa su ce Naziru, alhalin ba shi ba ne. Ko kuma in na yi waƙa ta ban sa suna ba kafin in samo logo na na Auta Waziri, in na yi waƙa sai su je su ce Naziru ne, da sauran su. Sai abin ya jawo ce-ce-ku-ce. Sai na ga cewa mafi sauƙi in cire sunan daga Autan Naziru zuwa Auta Waziri.
FIM: Ana cewa kun sha samun takun saƙa da shi Nazirun, musamman da ka nemi ku yi waƙa tare ya ƙi amincewa. Haka ne?
AUTA WAZIRI: E to, ba takun saƙa ba ne, don ni ban ɗauke shi wani takun saƙa ba. Saboda Naziru ba sa’an yi na ba ne bare a ce na yi wani abin nan da shi, kuma tsakani na da shi akwai mutunci da mutuntawa na gaskiya da gaskiya. Kawai dai ‘issues’ ne kamar yadda na faɗa maka, in na yi aiki a wani wuri ko kuma in na yi aiki a je a cire farkon, su je su kai aiki su ce Naziru ne, kuma alhalin ba shi ba ne. Ka san irin wannan abin ba daɗi. To irin wannan abubuwan su mu ka rinƙa samun ‘challenges’ a kai, wannan shi ne.

FIM: A wannan zamanin, ka na cikin fitattun mawaƙan da idan aka fara ƙirge daga ɗaya ba za ka wuce na biyar ba. Wane ƙwarin gwiwa ka ke ji a wannan matsayi da ka ke a yanzu?
AUTA WAZIRI: Alhamdu lillah! Na gode wa Allah (swt), ina kuma ƙara godiya. Kawai dai tunda ka san mun daɗe a ‘system’ ɗin, kawai abu ne da lokacin sa ya yi, kuma zai wuce. Ina jin daɗi, ka san masoyi ya na da daɗi a ko’ina ka gan shi. Ina jin daɗi in na ga mutane su na ‘appreciating’ abubuwan da na ke yi masu su na jin daɗi, wannan shi ne.
FIM: Menene alaƙar ka da jaruma Momee Gombe? Don ana yawan ganin bidiyon waƙoƙin ka tare da ita, wasu na cewa soyayya ce a tsakanin ku. Mecece gaskiyar maganar?
AUTA WAZIRI: Maganar bidiyoyi na da ake yawan gani da Momee Gombe, har wasu ke tunanin mu na soyayya, kawai dai shaƙuwa ne na aiki, abokiyar aiki na ce. Kuma ka ga ‘star’ ce, wacce ta na cikin taurarin zamani, wadda zamani ke yi da su. Mu na da kyakkyawar fahimta ne, sai mutane su ke ɗauka soyayya ce, amma babu wani abu.
FIM: Yaushe Auta Waziri zai yi aure?
AUTA WAZIRI: To, aure nufin Allah ne. In ta kama gobe ma mutum sai ya yi. Fatan da na ke yi, Allah ya kawo mace tagari, wacce za mu dace mu yi aure in-sha Allahu.
FIM: Ka na da burin auren ‘yar fim ko mawaƙiya?
AUTA WAZIRI: Auren mawaƙiya ko ‘yar fim, mutum ba ya wuce ƙaddarar sa, ba ya wuce abin da Ubangiji Allah ya ƙadarta masa a rayuwar sa. Ka ce ka auri mawaƙi ko ‘yar fim, ka ce ba za ka aure ta ba, in Allah ya ƙadarta maka ka aure ta, ba ka da yadda za ka yi, sai ka aure ta. To ni abin da na fi dubawa, natsuwar mace da tarbiyyar ta, a duk inda ta ke zan iya auren ta, ba ni da matsala da wannan. Maganar auren mace ‘yar fim in ta kama zan aura, ni zan zauna da ita.
FIM: Ka na ɗaya daga cikin mawaƙa da su ka ba da gudunmawa a siyasar Jihar Kaduna, ana iya cewa ma kai ne a gaba. Ko bayan an ci zaɓe Auta ya samu wani abu daga sabuwar gwamnati?
AUTA WAZIRI: A sabuwar gwamnati ta Malam Uba Sani, ƙwarai da gaske mun ba da gudunmawa ɗari bisa ɗari, mun ba da lokuta da basira da jiki, mun yi abin da ya kamata, kuma mun san cewa ya na sane da mu, tunda har yanzu mu na da kyakkyawar alaƙar da idan wani abu ya taso, mu ka yi magana ana sauraren mu. Maganar muƙami ko wani abu, mu abin da mu ke kallo ta yaya gwamnati za ta tsaya da ƙafar ta, ta yi wa mutane abin da ya dace. Mu da ma da mu ka taho, ba wai mun je don kawunan mu ba ne, mun taho don kawunan al’umma ne, in amfani ya zo, ya amfane mu gaba ɗaya da mu da al’umma. Don haka dole mu yi ‘focusing’ a kan me gwamnati za ta yi don ta amfani al’umma. In gwamnati ta yi kuskure za mu faɗa mata; yadda mu ka zo mu ka tsaya mu ka tallata ta, in ta yi kuskure za mu faɗa mata. Amma sakayya wani abu ne da ke zuwa daga baya in-sha Allah.
FIM: Menene saƙon ka ga mawaƙa ‘yan’uwan ka?
AUTA WAZIRI: Saƙo ga ‘yan’uwa na mawaƙa, ko da yaushe mu fara neman ƙwarewa, ba ƙoƙarin da mutum ya fara waƙa ya ce sai an san shi ba, a’a, ka nemi ƙwarewa, ɗaukaka lokaci ne. Allah ya na iya kawo wanda yau ya fara waƙa, kuma waƙar sa ta shiga duniya. Ɗaukaka wannan iko ne na Ubangiji. Neman ƙwarewa, jajircewa da kuma haƙuri da rashin kallon kowa. In mutum ya na harkar sa, ya yi ‘facing’ abin da ke gaban sa kawai ya yi. Kada ka damu da wane ko wani ya yi kaza, ka ce sai ka yi dole. Wannan ya na kai mutum ga halaka. Ni shawarar da zan iya ba da wa, duk inda mawaƙi ya ke ko ya ke kallo wani mawaƙin da ya ke so ya zama irin sa, to ya natsu ya yi abin da ya ke gaban sa, ya kuma inganta ayyukan sa, ya yi tunani mai kyau, ya kuma yi addu’a.

FIM: Me za ka cewa masoyan ka?
AUTA WAZIRI: Masoya na a duk inda su ke, ina yi masu fatan alkhairi, kuma ina jin daɗin yadda su ke ba ni goyon baya. Allah ya saka da alkhairi, su kasance tare da ni a ko da yaushe. Zan yi ƙoƙarin ganin na yi abin da zai faranta masu rai in Allah ya yarda.
FIM: Mun gode Auta.
AUTA WAZIRI: Ni ma na gode.


