• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, July 6, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jami’an tsaro za su kare rayuka da lafiyar malaman jami’o’in da za su yi aikin zaɓe – Yakubu

by DAGA WAKILIN MU
February 10, 2023
in Nijeriya
0
Farfesa Yakubu (a dama) a wajen taron INEC da Mataimakan Shugaban Jami'a

Farfesa Yakubu (a dama) a wajen taron INEC da Mataimakan Shugaban Jami'a

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

DAIDAI saura makwanni biyu a gudanar da zaɓe, Shugaban Hukumar Zaɓe na Ƙasa Farfesa Mahmood Yakubu, ya tabbatar wa Shugabannin Jami’o’i cewa za a kare rayuka da lafiyar dukkan malaman da za su yi aikin zaɓe.

Yakubu ya ce INEC na aiki tare da dukkan ɓangarorin jami’an tsaro na faɗin ƙasar nan domin samar da cikakken tsaro ga ma’aikatan da za su yi aikin zaɓe a matakai daban-daban har matakai 10.

Daga saman jerin sunayen muƙaman masu aikin zaɓe akwai Babban Baturen Zaɓe na Jiha, Jami’an Tattara Sakamakon Zaɓe na Jihohi, Baturen Zaɓe da Mataimakin sa da kuma masu sa-idon da aka tantance yardar su kula da yadda ake gudanar da zaɓen. Akwai kuma ‘yan jarida, waɗanda su ma waɗanda aka tantance ne za su riƙa zagayawa ɗauko labaran abin da ke faruwa a rumfunan zaɓe da cibiyoyin tattara sakamakon zaɓen.

Shugaban INEC ya ce an tanadi inshora ga duk wani ma’aikacin da aka tantance zai yi aikin zaɓe.

Wani sashe na Mataimakan Shugaban Jami’a a taron

Shugabannin jami’o’i sun nuna wa Shugaban INEC abubuwan da su ke da damuwa a kai, a lokacin ganawar ta su a Hedikwatar Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa, wadda ke kusa da Hedikwatar INEC a Abuja, a ranar Alhamis.

Yakubu ne dai ya nemi a yi ganawar domin nan amincewa a ɗauki sunayen malaman jami’o’i da za su yi aikin zaɓe.

Sai dai wasu shugabannin jami’o’in sun nuna ɗar-ɗar dangane da matsalar tsaro a wasu yankunan da za a tura wasu malaman a wuraren da ba cikin birane ba.

A nan, Yakubu ya tabbatar masu da cewa a ko’ina har a cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe.

Ya ce ya gana da shugabannin ɓangarorin tsaro na ƙasar nan, kuma sun tabbatar masa da cewa za su samar da isasshen tsaro.

“Za mu yi aiki ne tare da ma’aikatan tsaro, kuma sun tabbatar min cewa za su samar da isasshen tsaro.

Yakubu ya ce za a fara horas da malaman jami’o’i aikin zaɓe a ranakun 21 da 22 ga Fabrairu.

Loading

Previous Post

‘Yan jagaliyar da ke ƙulle-ƙullen fizgen na’urar tantance masu rajista a ranar zaɓe, aikin banza su ke yi – INEC

Next Post

Jerin jami’an INEC waɗanda gudanar da zaɓen 2023 ya rataya a wuyan su

Related Posts

SHEKARA ƊAYA BAYAN KOMAWA KAN KARAGAR MULKI: Tasirin Yadda Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Dawo Da Martabar Masarautar Kano
Nijeriya

SHEKARA ƊAYA BAYAN KOMAWA KAN KARAGAR MULKI: Tasirin Yadda Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Dawo Da Martabar Masarautar Kano

July 5, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya

July 1, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina

June 30, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin akwai tsaro a Abuja duk da gargaɗin da Amurka ta ba matafiya

June 23, 2025
Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya
Nijeriya

Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya

June 21, 2025
Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu
Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu

June 20, 2025
Next Post
Ma'aikatan zaɓe na wucin-gadi a wajen horaswa da INEC ta shirya a ranar Asabar

Jerin jami'an INEC waɗanda gudanar da zaɓen 2023 ya rataya a wuyan su

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!