(Sadaukarwa ga Hajiya Rahma Abdulmajid,
Hajiya Zahra’u Usman
da Hajiya Bint Hijazi)
“Mu haɗa kai ‘yan Arewa mu yi abin da ya dace”
1. Bismillah da Sunan Allah Rabbana Mahalicce.
2. Mahaliccin duk ‘yan’adam, bishiya da itace.
3. Kai ka ɗaukaka mu bil’adam duk mazan mu da mace.
4. Kan na fara salati na yi ga Shugaba mafifice.
4. Shumagaban mu Rasulullah mai kyau a siffa da zance.
5. Na sa iyali nai Ahlulbait masu kyawun kwatance.
6. Sannan Sahabban Nabiyullah nagargartu kun yi dace.
7. Nai yekuwa ‘yan Arewar mu mu yi abin da ya dace.
8. An kashe mu a hanya har a gidan mu ma an yi ƙwace.
9. Ana ta fyaɗe ga mata, shanayen mu ma an ka kwance.
10. An sa rashin jituwa tsakankanin mu Hausa-Filance.
11. Ana ta yin garkuwa da mu ‘ya’yan mu har ‘ya mace.
12. Sannan mu bada kuɗin fansa yankin mu mun fa kurumce.
13. Mu na ta ƙara masu ƙarfi Arewa mun fa makance.
14. Zaɓaɓɓun mahukunta sun ƙi abin da ya dace.
15. Muggan makamai sun yayyaɗu Arewa yau babu zance.
16. Mu haɗa kai ‘yan Arewa mui abin da ya dace.
17. Mu ƙara komawa ga Allah Shi kaɗai mu kaɗaice.
18. Mu ninka istigfarin mu da hailala mu karance.
19. Sannan mu lizimci Ƙur’ani mu daina duk cece-kucce.
20. Ƙunutu ma mu lizimce ta yin gaskiya ma mu nace.
21. Mu nemi haƙƙoƙin mu amma cikin shari’ance.
22. Haƙƙin mu ne jerin-gwano cikin abin da ya dace.
23. Har yin zaman dirshan ma mu yi dai abin shari’ance.
24. Duk don mu ja hankulan mahukunta sui abin da ya dace.
25. Mu haɗa kai ‘yan Arewa mu yi abin da ya dace.
26. Abdulhamidi Matazu waƙar ni na yo kar ku mance.
27. A ‘two thousand twenty-one’ da mun ka zam a ɗimauce.
28. Ran sha biyu ga watan sha biyu amma a miladiyance.
29. Don shajja’a ‘yan Arewa ta mu tashi mu daina kwance.
30. Ya ikhwani liƙa’ul-khair Allah ya sa mun ji zance.
Alhamdu lillah!
- Abdulhamid Muhammad Sani
(Malumma Matazu) shi ne shugaban riƙo na
Gamayyar Marubuta da Manazarta Waƙoƙin Hausa na Nijeriya, reshen Jihar Katsina
GSM: 08037868097