SHAHARARRIYAR jaruma a Kannywood, Halima Yusuf Atete, ita ma lokaci ya yi, domin kuwa yau saura kwanaki shida ta shiga ɗakin mijin ta.
Za a ɗaura auren ta Halima Atete da sahibin ta Mohammed Mohammed Kala a ranar Asabar, 26 ga Nuwamba, 2022.
Katin ɗaurin auren wanda mujallar Fim ta samu ya nuna cewa za a ɗaura auren da misalin ƙarfe 10:30 na safe a masallacin Juma’a da ke Abuja Sheraton Bus Stop, Maiduguri, Jihar Borno.

Kafin ranar ɗaurin auren akwai shagulgula da za a gudanar, kamar ƙwallon ƙafa da misalin ƙarfe 7:00 na yamma a ranar Laraba; Ranar Margi (Margi Day) da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Alhamis; Daren Larabawa (Arabian Night), da misalin ƙarfe 7:00 na yamma a ranar Juma’a. Sai dai kuma ba a bayyana wuraren da za a yi shagulgulan ba.
Bayan ɗaurin auren, za a yi dina da misalin ƙarfe 8:00 na dare a Maiduguri ranar Asabar ɗin.
Mujallar Fim ta samu labarin cewa jarumar Kannywood da dama, musamman matan, su na nan su na shirin zuwa Maiduguri domin taya ƙawar su kuma abokiyar aikin su murna.

