A RANAR Asabar da ta gabata aka ɗaura auren Safiyya Muhammad Abubakar, ‘ya ta biyu ta jarumar Kannywood, Hajiya Jamila Usman, wadda aka fi sani da Jamila Lasco.
An ɗaura auren Safiyya ne da abin ƙaunar ta, Misbahu Abdulhameed Yunus, da misalin ƙarfe 2:00 na rana a garin Kargi da ke Ƙaramar Hukumar Kauru a Jihar Kaduna, a kan sadaki N200,000.

An yi shagulgulan biki tun kafin ranar ɗaurin aure, kamar Ƙauye Day (Ranar Ƙauyawa), Fulani Day (Ranar Fulani),
Ladies Party (Fatin ‘Yan Mata) da kuma yinin biki.
Wasu daga cikin ‘yan fim da su ka halarci bukukuwan sun haɗa da Ummi Hutu, Fanan Buzuwa, Raliya Muhammad, Zee Shewa, Anisa, Nura Small, Hassan Ramin Kura, Jamil Nafseen, Nazari, Mubarak, Adamu Usaini, Nafisa Shoki, Aisha, Farida Feedy, Maryam Ɗalibi, Khadeeja Kt, SK Mafiya, Ummi Beauty, Ɗan Sholi Comedy, Malo Comedy, Abdullahi Abu Uku, Aminu Jahilin Malami, Haske Comedy, Adam Ɗorayi Kano da Umar Kano.

Idan ba ku manta ba, mujallar Fim ta ba ku labarin cewa a ranar Asabar, 27 ga Janairu, 2024 aka ɗaura auren babbar ‘yar Jamila ɗin, wato Amina Muhammad, a Zariya.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.





