A DAREN jiya Asabar, 1 ga Yuni Allah ya ɗauki ran yayan shahararren marubuci, furodusa kuma jarumi a Kannywood, Malam Ɗan Azumi Baba Ceɗiyar ‘Yan Gurasa, wanda aka fi sani da Kamaye.
Malam Muhammad Inuwa Baba ya rasu da misalin ƙarfe 1:00 na dare bayan ya shafe tsawon shekara huɗu ya na jinya.
An yi jana’izar sa da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar yau Lahadi a gidan Ɗan Azumi Baba da ke unguwar Ceɗiyar ‘Yan Gurasa a Jihar Kano.
Daga nan aka kai shi gidan sa na gaske da ke maƙabartar Ɗandolo.
Ɗan’azimi Baba ya shaidawa mujallar Fim cewa, kwana uku ne tsakanin Malam Muhammad da babbar yayar su Hajiya Lami da ita ma Allah ya yi mata rasuwa.
Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, shi kaɗai ne wanda ya halarci jana’izar daga Kannywood.
Allah ya jiƙan su da rahama, ya kuma albarkaci bayan su.